← Book details Kaine Sirrina Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 39 OF 43

Sashe 39

Kaine Sirrina Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ahankali yadaga kafa ya juya ganin Mum tsaye abayanshi hawaye na kwarara a fuskarta yasa ya kakalo murmushi ya sakar mata yazo zaibi ta gabanta ya wuce tarike hanunshi”dont hide anything, maiya sami Son?I know something is wrong I can feel it here”ta nuna mishi zuciyarta tana kuka sosai. Dad ya rungume ta yana shafa bayanta ahankali yace”Adama kisan Allah shike hallito bawa yakuma dauke abinshi idan yaso ko? “Ta girgiza kai tare da rike kirjinta “karkiji tsoro,ki dake kikuma yarda da kaddara,Barraq ya rasu! “Amma da karaso warta kenan wajen tace”what! Mum ta rike rigan Dad gam tai kasa zata fadi Dad ya riketa da sauri yana lallashin ta, Amma tafashe da kuka tazo ta kama hannun Mum tana kuka. Mum ta kalli Amma “wasa yake dena kuka Maman Auta dena kinji”. Dad da idanunshi yay ja yace”Amma take her inside ki dau Rufaida ki kaita part din Barraq banason tasan komi,batada lapiya kar ciwonta ya dawo sabo,bari naje mutaho dashi”. Dad yay hanyar gate yay magana damai gadi maigadi ya dafe kanshi kafin ya bude gate din da sauri Dad ya shiga katuwar jeep yaja yafita mai gadi yarufe gate da sauri yafita ya shiga mota suka tafi tare da Dad. Dad yana tuki yana kiran mutane da yan uwanshi saida ya biya yadau imam din anguwar su da wayansu mutane dasukayi mota guda dan ansan Barrister Barraq ko ina. Ahankali Imam ya tura kofar bedroom din gidan Nana dan tunda suka shiga gidan Dad jikinshi yay sanyi idanunshi sukai jajir sukai zuru zuru. hango Muzzamil zaune gaban Barraq da fuskarshi ke alullube duk jini yasa Dad ya rike zuciyar shi Muzzammil ya dago jajayen idanunshi ya kalli su Dad ciki harda Dadinshi da sauri yatashi ya rungume Dadinshi yasaki Kuka. Kafin yasaki dadin shi ya rungume Dadin Barraq yana kuka sosai. Dad ya shafa bayanshi Muzzammil ya sakeshi ya koma gefe. Dad ya karaso ya tsugunna yasa guiwowin shi akasa yakai hanun damanshi ya yaye rigar Muzzammil dake kan fuskarshi, ganin Fuskar Barraq dinshi ya bayyana yasa ya daga hannu ya kulle bakinshi yana kokarin hana kukan dake neman zuwan mishi ganin gawan danshi agaban shi. Ahankali ya dukar da kanshi ya sumbaci goshin Barraq yamai addu’a ya lumshe idonshi yana tunanin randa Barraq yacemai I luv yhu Daddy a restaurant din wajen asibiti. Wani mugun kuka ya kufcemai. Daddy ya girgiza kai “Barraq noo, u can’t die! Barraq kai kadaine dana namiji ku biyu gareni,narasa grandson dina,banason rasaka yanzu dan Allah kadawo”Baban Muzzammil ya kama kafadarshi ya murza alamun ya yakuri Dad ya juyo ya kalli Muzzammil cikin dishahshiyar muryarshi yace “waya mishi haka?waya kashemin da?” Imam ya girgiza kai “wanan za yishi anjima, yanada kyau akai gawa makwancinta da wuri mutafi” ya daga Dad ahankali. Yayinda mai gadi ya kawo pakaceciyan tabarma Imam Daddy da Dadin muzzammil suka daga Barraq suka sashi aciki aka nannade shi suka daukoshi aka fito dashi aka sashi a dogon bus din da Dadin muzzammil yazo dashi. Duk aka shishiga mota aka kama hanyar zuwa gida dan yimishi sutura. Alokacin gari yasoma duhu dan mangariba ta wuce amma isha bai riga yayiba. Rufaida dake zaune akan gado Amma a gefenta idanunta yay jajir tadai daure takiyin kuka dan kar Rufaida ta gane wani abu. Zumbur Rufaida ta mike ta rike zuciyar ta gam tana hawaye Amma ta tambaya “menene “Rufaida ta fashe da kuka sosai “bakin ciki nakeji sosai azuciyata, jinake kaman zan mutu,wlh bature kawai nakeson gani. Inajin alamun shi araina,kaman yana cikin gidanan yanzu,naji kamshin turaren shi”. Ahankali Amma ta zaunar da ita “zauna Rufaida, nanda anjima zai dawo meeting ya tsareshi”ta share hawayen ta”are yhu sure?” Amma ta gyada mata kai. Zaunawa Rufaida tayi shiru Amma ta tashi cikin dabara tadan bude labulen window hango maza an cika gidansu ga su dad sun dauko abu a tabarma ya tabbatar mata Barraq ne kasa rike hawayen ta tayi da sauri ta gogesu ta saki labulen ta kalli Rufaida datai tagume gwanin ban tausayi tace”bari naje nakawo miki abinci,ki jirani karki fito” tafita daga dakin da sauri batare data jira amsan Rufaida ba. Minti 30 da fitar Amma Rufaida ta tashi ta bude kofa ganin maza an cika ko ina a gidan wasu na kuka yasa jikinta yafara rawa taji wani irin motsi acikinta kaman na yaro, ganin wani dan tsoho na kuka agefe yasa Rufaida taje wajenshi “Baba meke faruwa? ” “yarinya mutumin daya taimake ni arayuwa yabani jari,yarana mata uku sun tashi aure Banda komi ya dauken mun nauyinsu,yamusu komi na daki yabiya kudi akama matata aikin cancer a nono datake dashi,shine yarasu,wasu mugaye suka kasheshi”. Rufaida ta rike cikinta gam ta tsugunna a wurin “Baba ya sunanshi menene kamanininshi?” Tsohon ya sharce majina “Barraq!Rufaida ta zaro ido dan taji dazu abbanta yakira baturen nan da Barraq. Ahankali Muryarta na rawa tace”Baba bature ne? ” Baba ya girgiza kai “eh jini biyu ne dai”Mamar shi yar rasha(Russia)babanshi dan Nigeria”. Rufaida ta tsala wani irin uban ihu tafashe da kuka tai hanyar part din Daddy yanda maza suka cika wajen yasa tajuyo takoma dakinsu tana kuka wardrobe ta bude taga suit baki daukowa tayi tasa ta daure wandon da dankwali saboda yamata yawa tasa necktie, rasa yanda zatayi da uban gashin ta yasa ta dauko wani facing cap data gani tasa ta dunkule gashin aciki tana kuka sosai”wlh saina ganka, saina kutsa cikin mazanan na ganka,dan Allah karka mutu” kara rike cikinta tayi dataga yakara motsi ta tashi da kyar tafito. Koda takaraso wurin taga an lullube abu da fararen kaya ansa amakara jiri tafara gani batasan lokacin data shiga cikin dandazon mazan nan ta dinga kutsawa har saida ta taba makarar ta rike gam tana kuka. Muzzammil dake hawaye ya juyo dan yaga me bugeshi garin kokarin kama makara. Ana saka makarar a mota Rufaida tariga kowa fadawa ciki ta chusa kanta a cinya tana kuka. Tadaiji mota natafiya wanda hakan yasa ta dago kanta ta kalli kowa Daddy kadai ta gane acikin mutanen Motar. Kuka tasake fashewa dashi sabo kafin ta zabura saboda motsin dataji cikinta nayi ta rike cikin gam tana kuka cikeda ihu tace”kadena min ciwo,wlh saina raka bature gidan gaskiya,inason shi,Allah ya jikan mijina ” kowa na motar ya zabura yana kallon mutumin da akaji da muryar mace, Dad yakai hannu ya cire hular gashin ta ya zuba akafada atare Dad da Muzzammil sukace “Rufaida! Kuka tasake fashewa dashi tana wani irin haki kaman zata mutu, ganin kowa na motar take biyu biyu ta hade hannayeta da kyar ta iya magana “Dad dan Allah karka koran zan bishi ne, idan kace a’a zan mut…”bata karasa maganan ba idanunta suka fara juyawa wani irin mugun jiri ya kwasheta ta sulale kwance a wurin hannunta daya ya sauka akan farin kyallen da Barraq ke ciki”. Dad yay salati Muzzammil yaza. ..” Muzzammil yace”Daddy look” ganin farin kyalle na motsi sosai yasa sauran mutanen cikin motar suka fara neman wurin guduwa. “Daddy budeshi, doguwar suma ce,he is alive! Maman Abd Shakur😘

[7/25, 20:28] Aishat Muhammad: *KAINE SIRRI NA*
83

Muzzammil yataya Dad suka ciroshi Dad ya warware kyallen jikinshi. Ahankali Baban muzzammil ya paka mota agefen titi sauran motoci da machina dake binsu abaya duk suka paka suna mamakin maiya tsayar da motar daya dauko gawa.
Daddin Muzzammil ya bude mota ya fito,Imam ma yafito suka zagayo baya,Muzzammil ya bude musu da sauri hawaye na kwarara a idonshi ahankali yace “Daddy da ranshi doguwar suma yayi,mutafi asibiti kawai” Dadin muzzammil yakai dubanshi ga Dadin Barraq dayasa Barraq a kirji yana hawaye sosai ahankali Barraq ya furta “Boo water,I need water” Dad ya dago kanshi da sauri yace”Muzzammil bamu ruwa ” kafin kace kwabo mutanen da suka zageye motar kowa yafara gudun nemo ruwa a shagunan dake kan hanya. Wani bawan Allah yasamu aka dinga pasin pasin goran ruwan faro saboda yanda jamaa suka taru har ya iso cikin motan muzzammil ya karba ya bude yabama Dad,Dad ya saka abakin Barraq da sauri yafara sha rabi na zuba akasa, Dadin Muzzammil ya gyara mai bakinshi ajikin ruwan yadan sha dadan yawa sanan Dad ya cire goran a bakinshi. ahankali Dad yace “mutafi asibitin”. Da kyar jama’a suka matsa ma Dadin Muzzammil da Imam suka fito suka shiga mota akaja, yayinda Muzzammil ya rufe kofa. Jama’a anata al’ajabin al amarin wato daguwar suma yayi. Aka koma mota wasu suka bisu wasu kuma suka juya gida tareda fatan Allah bashi lafiya. Karfe 10:30 P.M. suka isa Baban asibitin garin Abuja mai suna “Handsome Shakur Specialist Hospital” kwararun likita suka karbi Barraq da Rufaida da gaggawa. Anata yima Dad gaisuwar Allah bashi lpy mutane na tafiya. Muzzammil yasamu yadan kebe ya ciro wayarshi ganin kusan 35miss calls din Hafsat yasa yakirata da sauri yay mata bayanin abunda yafaru. labarin ya girgizata Muzzammil yace duk dare zai dawo tanuna mai bakomi,ya kula da abokinshi zuwa gobe yazo ya dauketa yakaita ta dubasu sukai sallama suka katse wayan. Yana gama wayan kiran Mum ya shigo wayarshi da sauri ya dauka Mum da muryarta ya dishe sosai tace”Muzzammil neman Daugther muke bamu ganta ba,kuyi sauri ku dawo” Muzzammil yay murmushi dimple dinshi suka bayyana “Mum kira Daddy danshi yakamata ya baki goodnews dinan” ya katse wayan yayi dailing number wani abokinshi ishak babban police ne,daya rike matsayin DpO yamai bayanin komi,DPO yace”gobe da safe zasuzo idan lokacin Barraq zai iya magana dole suyi magana dashi dan yamusu bayanin maiya kaishi gidan Nana,da sauran vital informations. Muzzammil yay godiya ya katse wayan tareda komawa cikin asibitin. Maman Abd Shakur😘

[7/25, 20:28] Aishat Muhammad: *KAINE SIRRI NA*
85
Chapter 39 · 0% Book details