← Book details Kaine Sirrina Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 34 OF 43

Sashe 34

Kaine Sirrina Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Alh ya rike mata hannu da sauri, Dad yatashi daga kan sofan dayake Alh ya daurata akai, kowa ya mike tsaye,Amma ta dauko goran Eva water mai sanyi ta mikama Alh ya bude yaba Umma tasha kadan tana Nuna Rufaida da hannu. Barraq dake dauke da yaron su a hannu ya juya dan ganin abunda Umma ke nunawa ganin Rufaida yasa ya dawo da kallonshi garesu a natse yace”Umma itace matata Rufaida,mesa kike nunata?” Alh ya mike tsaye ya share dan guntun hawayen idonshi”itace Rufaida dana fadama case dinmu akanta,wlh yarmu ce! Rufaida yar muce! Dad, Barraq,Amma da Mum suka hada baki alokaci daya sukace “what?! Umma ta daga kai cikin kuka ta kallesu tace “wlh yarmu ce,Rufaida baby na,i missed u” ta tashi zataje wurin gadon Barraq ya tsaya agaban ta “don’t touch my wife Ma,imma turoku akayi kutafi,inma set up ne to it won’t work,cuz Rufaida iyayen ta sun mutu, a minna parents dinta suke aiki amma asalin su yan kauyen gujungun ne na jahar jigawa, gini yafado ma iyayen ta ,nida kaina naje na karbo kudin da Gov. Sukaba duk family da ginin yafado musu,so yhu guys should cut d drama,I respect yhu alot Alh,ku barmin matata tahuta,why soo much hate??kowa yatashi Rufaida, everything Rufaida, wani laifi yar yarinyar nan tayi dat deserves all dis wahala?? Yhu guys should get out of dis hospital before I call security”. Ya mikama Alh yaron. Umma ta tsugunna tafashe da kuka sosai Alh yace”wlh wlh Barraq yarmu ce,itace Rufaida damuke ta nema”. Barraq cikin daga murna yace”I know is all a setup,idan itace Rufaida ku maisa baka taba nunamin hoton taba duk zuwana gidanku? “Alh yay shiru yakasa magana ga yarshi amma ana karyata shi, da kyar ya tattaro karfinshi yace”dan girman Allah ka yarda damu Barraq, wlh yarmu ce,ban taba tunanin nunama hoton taba but look inada hoton Rufaida a cellphone dina” Barraq yace” I don’t want to see, just get out of dis hospital now” Idanun Barraq yay ja dan duk atunanin shi wata kullalliyar aka kullo. Umma takara fashewa da kuka takama kafar Mum tace”Hajiya wlh yarmu ce,Rufaida nace, kice yabar mu muganta”. Mum ta girgiza kai “Hajiya batar fuska kikayi,Rufaida nan iyayen ta sun rasu, dan Allah kutafi murabu ta arziki inma turoku akayi mun gane bazaiyi aiki ba kutafi” Umma taki tashi, Alh yaki matsawa yaron hanunshi na kuka sai alokacin Dad yay magana “Alh wanan ba itace Rufaida kuba, kutafi kafin akira security bamuson tashin hankali”. Barraq ya daga murya yana kiran security! Security! Umma takara kecewa da kuka yaron hanun Alh ya fashe da kuka, hayaniyan dayacika dakin da koke-koke yasa Rufaida tafara motsi, kafafun ta suka fara rawa ahankali tace”wayyo Mummy,Uncle B Duduwa “da sauri kowa ya juyo inda take Barraq yakarasa wajen da sauri yarike hanunta ahankali yace”Baby ni ne, open ur eyes” ahankali ta bude ido tana ganin Barraq ta kankameshi tana kuka sosai “zata dakeni,plz kace karta daken Uncle B, banason duka ” Barraq ya cireta daga jikinshi yasa hannu ya share mata fuska yace”Hey!calm down,look nikadai ne sai Mummy da Daddy dakuma Amma,babu wanda zai dakeki,bazan kara bari acutar dakeba” da kyar ta iya maimaita abinda yace saboda zafin dataji cikinta namata tace”Mummy?” Barraq ya girgiza Mata kai” yes!mummy tazo tun jiya” matsawa gefe yayi Mum ta bayyana agaban ta tana murmushi,Rufaida ta bude ma Mum hannu tanason ta rungume ta, da sauri Mum ta rungumeta. Sai alokacin idanun Rufaida ya sauka kan wata yar mata a tsugunne idanunta hawaye shabe shabe,sai kallonta take da wani mutume yana dauke da yaro shima sai kallonta yake. ta dago da kanta daga jikin Mum tana kallon mutanen dabatasaniba, Mum da kowa na dakin yabi Rufaida da kallo. Umma ahankali takara matsowa jikin gadon ta daga hannu tana kokarin taba Rufaida da sauri Rufaida ta shige jikin Mum tadanyi ihu “Mummy wacece wanan?maisa take kuka?maisa itada wanchan suke kallona? ” kafin Mum tai magana Umma tarigata tace”Rufaida nine Mummy ki, Umma,kin manta ni Rufaida? ” Umma ta tashi da sauri tariko hanun Alh tace “kinga ga Daddy ki shima kin mantashi??” Rufaida ta girgiza kai “nidai kidena kuka,Ga Mummy na nan,asalin Amma na da Abba na sun rasu”idanunta yakawo kwalla Barraq yace”look sir kufita daga dakin nan,kunga bata da lpy,kundai ji tafadi muku da bakinta bata sanku ba”. Saida aka kira security sanan Alh da Umma sukabar asibitin. Da kyar Alh ya kwantar ma da Umma hankali yace”Alhamdulillah ma munganta,mun kuma san tana hannu nagari masuji da ita,masu sonta,matsalar da tambayar daya ce tak! maisa Rufaida ta manta damu??Maisa? “. Maman Abd Shakur😘

[7/14, 23:04] Aishat Muhammad: *KAINE SIRRI NA*
75

Da kyar suka kai hotel din dasuka sauka, Abba yakira kanninshi dasuke kano ya sanar dasu anga Rufaida,amma anhana su ita, kowa yahau murna, sukai alkawarin zasuzo gobe da sassafe Abujan, ayita a waje dole suji daga garesu. Yakira amintaccen mai gadinshi dayake yanada makullin gida yace ya shiga dakin Rufaida ya bude wardrobe dinta ya kwaso albums din hotunonin su duka da kayan makaran tarta da jakar makaran tarta yahada su waje daya gobe zai turo wani abokinshi akaishi Airport yazo Abuja yarike katin zaben shi dan zaa tambaya. Mai gadi ya amsa da to Alhj ya shiga gida yahada komi tsaf dan shirin zuwa Abuja gobe sai murna yake zai shiga jirgin sama. Yau Babbar rana ce ga Alh,Umma da yan uwan su harda mai gadi. Misalin sha biyu na rana kowa ya iso daduk all evidence da shaidun da suka nuna cewa Rufaida yarsu ce. Manyan motoci biyu suka cika aka tafi asibitin dashi. Koda suka isa ba’a barsu sun shiga ba wai ba visiting hour bane. suna tsaye saiga Dad yazo zai wuce Alh yamai magana ya tsaya suka gaisa sanan sukaja Dad gefe daya tiryan tiryan yayan Alh yama Dad bayanin komi tareda nuna mishi hotunan Rufaida tun tana karama har girmanta. Da kyar suka samu Dad ya yarda dasu saida shima tashi tambayar daya ce “maisa Rufaida ta manta dasu,maisa ta manta da iyayen ta? ” Sai alokacin kanin Alh yay magana yace”inaga aljanu ko sammu ne suka shafi Rufaida, dan mutum baya manta iyayenshi haka inbadai matsalar kwakwalwa yasamu ba,nataho da magani da addu’oin dazan mata in sha Allah zamuji gaskiyar abun,komi zai warware”. Dad yace “shi kenan bari nakira muku Barraq,saina nemi sallama wurin likita dan mutafi gida ayi komi achan”. Sukaima Dad godiya sosai. Dad ya shiga dakin ya tarar da Barraq naba Rufaida tea tana sha ahankali Mum na bandaki,Amma ta tafi gida yomusu abinci da sauri Rufaida ta kawar dakai ganin Daddy ya shigo murmushi dad yayi ya kalli Barraq “ana nemanka awaje son” Barraq ya amsa da to. Dad ya juya yafita yacigaba dabama Rufaida tea,ture cup din tayi tadan ya mutse fuska “am okey” Barraq ya ajiye tea agefe “saina miki dure tunda bakicin abinci yanzu”. tashi yayi daga kan gadon ya tsugunno yama goshin ta kiss “I luv yhu Baby na” ya juya zai fita harya bude kofa ya tsaya yana kulle boturan rigarshi yaji muryar Rufaida tace”Uncle B” da sauri ya kalleta “Naam Baby na” hannuwan ta tarufe fuskarta dashi”I love you” kulle ido yayi ya bude,kafin yasa hannu ya mintsili kanshi so ba mafarki yakeba Ahankali yace “mekika ce??” Tajuyar dakai tana murmushi Mum tafito daga bayi tsayawa yayi agaban kofa yana kallonta Mum na zama agadon Rufaida ta tashi da kyar ta rungume Mum fuskarta na kallon Barraq ta bude baki ta Furta mai I love you, lips dinta ya karanta yagane abunda tafada. fita yay daga dakin yana M urmushin da saida duka hakoranzhi suka bayyana. Koda yaga su Alh ne yajuya zai koma “Umma tace dan girman Allah Barr ka tsaya” bai musu ba ya tsaya, ahankali kowa ya gabatar mai da iya gaskiyar su da hotunan, yakuma kara ganin kaman da Rufaida tayi da Rayyan kaninta but still yace “Alh mu shiga asibitin nan ayi DNA test,Dad dake karaso wa yace”Son shiga mota mutafi gida”Barraq ya juya yaga Amma riqe da Rufaida dake tafiya da kyar Barraq yace”But Dad…”Dad ya katseshi “No but Barraq,is time to know d actual Truth,is time dazamu san maisa dat old woman hate Rufaida sosai,less go” kowa ya shiga mota Rufaida na jikin Mum tana numfashi da kyar ita yanzu tsoron mutane take bana wasaba. Maman Abd Shakur😘

[7/14, 23:15] Aishat Muhammad: *KAINE SIRRINA* 76
Chapter 34 · 0% Book details