Sashe 36
Kaine Sirrina Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read
Shigowa su Dad sukayi kowa yanemi wuri ya zauna Barraq idanunshi nakan Rufaida dayaga tana kuka sosai kaman yay magana saikuma yay shiru ya dukar da kanshi akasa. Alh yay gyaran murya yace “Alh zamutafi” da sauri Barraq ya dago kanshi ya kalli Alh. Alh ya sakinma Barraq tattausan murmushi kafin ya juya ga Dad yace”mun gode da kula da yarmu dakukayi da zaba mata miji nagari dakukayi nagode Alh. Babbar gaisuwata da fatan alheri gareka Barr Allah yakara daukaka ka yabaka zuri’a nagari, nagode da bama yata so da kulawa”. Barraq ya sadda kanshi kasa,Alh ya cigaba “ga Rufaida nan, in sha Allah zamu dinga zuwa dubata,Allah ya saka muku da alheri” ya juya ya kalli Rufaida yace “kima mijinki da iyayenki biyayya, inhar aka kawomin karanki saina saba miki kinajina ko?” Ta gyada kai tana share hawaye. Dad yay magana “bazaku tafi da ita tadan zauna daku ba?munsan kuna bukatar yarku itama haka,abun zai mata yawa ta warke kuma tacigaba da zama da wayanda batasani ba” Alh yay murmushi “tasan ku, saitana zama daku dinne ai zata tunaku,yanzu bata karkashin mu tana karkashin inuwar auren Barraq ne, haka Allah ya kaddara, mun gode kwarai,”ya kalli mum yace mun gode ma ya kalli Amma yace mun gode ma Umma da su Baffa suka goggode musu kafin kowa ya mike tsaye zasu tafi duk suka tashi Rufaida tarike zanin Umma tana kuka “ni wlh kidawo,banason gidanan,zan biku” Umma ta shafa kanta “banace zan dawo ba? kiyakuri kinji Baby na” Rufaida ta make kafada tana kuka. cikin Bacin Rai Baffa sarkin masifa ya daka mata tsawa “yimana shiru kafin nafasa bakinan,sake ta” bakinta tarike tana hawaye, Ya kalli Barraq yace”kaita daki tasha maganin ta tai bacci, bata gama warkewa ba bata bukatan all dis stress”. Ahankali Barraq yatako inda take ya mika mata hannu make kafada tayi da Baffa yamata wani mugun kallo batasan sanda tabashi ba tana tafiya ahankali suka fita daga dakin part dinshi yakaita yabude suka shiga. sukama su Alh sukabar gidan Dad dasu Amma suka dawo ciki kowa yana mamakin abunda yafaru yau. Suna shiga dakin ta fizge hanunta tana turo baki”kuma ni mutum yasake ni tunda dai ba hanunshi ya rike ba” Ta nemi kujera ta zauna ahankali tana cije lebe. Barraq baice komi ba saidan Murmushin dayayi aranshi yace so real Rufaida nada masifa O God save me!. Fita yayi daga dakin yatafi bangaren Amma yaganta tareda Mum yace”Mummy ina magungunan ta?” Mum ta dauko tabashi ya juya zai fita takirashi Son ya dawo “kabi Daugther ahankali, kayi hakuri dakome zatayi kaji, karka bata mata rai, kadaiga batada lpy anjima zan shigo naganta” ya juya yafita koda ya shiga dakin ya tarar da ita a zaune tadena sai kumbure kumburen datakeyi. ya dauko goran ruwan faro da maganin daya kamata tasha ya ballo ya mika mata “sha maganin ki Baby na”ta kalleshi ta ballamai harara “ni bazan shaba malam, kumani kabani kayan sawana zanyi wanka na chanza kayan nan” yadade tsaye yana kallon yanda take murguda mai baki. Tsugunnawa yayi agabanta yace”naji but plz take it and drink,baki da lafiya” “ance baza ashaba,wai ni dole ne wlh niba ruwana da mutum, wai mijina ne, aibani nace inaso ba, nigidan mu zaka kaini gobe ehe” tana karasa maganan tabi ta gefenshi tayi hanyar wata kofa data gani,tasa hannu ta bude tabi wurin takara ganin wani kofa ta bude taga bedroom takarasa shiga dakin tanemi bakin gado ta zauna da kyar. Ta sauke ajiyan zuciya tana shafa cikinta “wai meyasa cikina ke ciwo?wayyo zapi wlh” tafada araunane. zip din rigarta ta zage, ta cire rigar daga jikinta dan warin asibiti rigar yake mata wanda hakan keson yasata amai. Yarage daga ita sai sket da Bra, ta tashi tsaye tana kokarin zage zip din sket din taji an bude kofa an shigo ganin Barraq dauke da maganin ahannunshi yana wani irin kallonta yasa tafara neman rigarta dake kan gado. Barraq yamata kuri rabon dayaga jikinta harya manta. Sa hannu yayi ya tura kofar tarufu sanan yakara sa shigo wa dakin “wai mehaka?can’t u see dat am changing,kafita? ” Rufaida tafada a masifance, Barraq ya sakin mata murmushi tareda lankwasa kai alamun a’a kaman yanda takeyi. Daukar rigar tayi tasa agaban kirjinta tana nunashi da yatsa “wai kai baturen nan wani irin maye ne? ” saida takai bango sanan yasa hannu shi ta bayanta yahada ta da jikinshi, Rufaida ta rufe ido gam jikinta ko ina na rawa murmushi yasake yi aranshi yace”one character in common Rufaida den and now duk matsorata ne” duko da kanshi yayi yakai bakinshi saitin kunnenta yace”ni mayen Rufaida ne ” Rufaida ta sa hannu ta rufe kunnenta rigar tafadi akasa. Bude ido tayi suna hada ido tasake kulle idonta “let me go,wai mehaka,I hate dis stuff,plz let me go ” Barraq yasa hannu yakai wuyan ta yanama ta waiwayi zuwa kasa “only if u take ur drugs ” jin hannunshi nagab da kaiwa kirjinta ta rike hanun muryar ta na rawa sosai tace”to bani zansha “. Maman Abd Shakur😘
[7/25, 20:28] Aishat Muhammad: *KAINE SIRRI NA*
80
[7/25, 20:28] Aishat Muhammad: *KAINE SIRRI NA*
80