← Book details Kaine Sirrina Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 35 OF 43

Sashe 35

Kaine Sirrina Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Babban falon Daddy aka sauke bakin. Dad,Mummy,Amma,Barraq,sai Rufaida daya rike mata hannu gam kamar zata gudu. Bangaren su Alh kuwa daga shi sai Umma,sai Babban wanshi,da kannenshi biyu da mai gadi agefe. Ba abunda sukeyi sai kallon Rufaida. Rufaida ta rike hanun Barraq gam kaman za’a saceta. Dad ya kalli kanin Alh yace”Bismillah” Mutumin ya kalli Rufaida yace “zo,Al Qur’ani mai girma zan karanta akanki” Rufaida ta rike Barraq gam tana kuka,Barraq yakara riketa shima bayason taje danshi bai yarda da abinda zasuyi ba. Dad ya kalli Rufaida yace”Daugther na” ta kalleshi yace “jeki”. Da taimakon Barraq ta iya tashi yakaita gaban malam ya zaunar da ita, sanan ya koma wurinshi ya zauna mutumin yay isti’aza da basmala cikin kira’a mai dadi, cikin kuka Rufaida tace “Dan Allah tsaya,wlh ni banason karatunan dakake min, yana tadamin da hankali” mutumin yacigaba batare daya saurareta ba. Rufaida takara fashewa da kuka tana mikama Barraq hannu jikinta ko ina na rawa, Barraq yay kaman zai tashi Dad ya ballamai harara, yakoma ya zauna karatu yay karatu ayoyin Allah sun soma ratsa kan Rufaida ahankali ta sulale ta kwanta akasa flat idanunta suka kankance, Barraq ya zabura ya tashi Mum ta zaunar dashi ta rikemai hannu. mutumin ya kalli su Dad “dama nace da abunda akama yarinyar nan,sammu ne yanzu kuma zan karyashi da izinin Allah, sammun zai koma kan wanda yamata” kowa yay shiru mutumin ya dauko jakarshi ya dibi garin tafarnuwa dawani bakin magani da garin habbatus sauda ya hada yasama Rufaida abaki, ya diga ruwan zamzam so uku abakinta yahade mata bakin ya rufe ya matse hancinta nadan sakanni saida yaga tahadiye sanan ya saketa “Rufaida! Rufaida! Rufaida! Ki mantasu arayuwar ki! Ki manta Abban ki da Umman ki, ki shiga duniya karku sake haduwa…”Barraq ya mike”Dad do something I hate all dis stuff,wot is he doing to her? Wot is she saying?” Dad ya nunamai kujera alamun ya zauna yako zauna. Chan kuma saita shiru. Tana buga kanta akasa sosai Barraq ganin bazai iya juran ganiba ya chusa kanshi a tsakakanin kafafunshi yana goge hawaye. Dakin yay shiru Rufaida ta dena abinda takeyi. Mutumin ya cigaba da rera karatun Al Qur’ani a gefenta. Tadau minti talatin ahaka kafin ta bude idanunta ta kalli saman dakin. Saikuma ta zabura tamike tsaye har saida mutanen dakin suka tsorata, tadanyi kara ta rike cikinta”auch” idanunta arufe tace “Umma gari yay haske baki tashen daga bacci ba,uh cikina na ciwo,banasom nai lattin school munada test yau” da sauri Barraq ya daga kanshi ya kalleta. Barraq yataso yazo kusa da ita”Baby na are yhu ok?Dr yace cikin zai rage miki ciwo nan da gobe” ahankali ta cire hanun daga cikinta ta bude idonta ahankali tana kokarin ganin fuskar husky muryar dayay mata magana yanzun nan. Sauke idonta datayi akan wani kakkyawan bature,ga gashin baturai,ga wani hadaddan farin gilashi a idonshi yana mata murmushi yasa ta juya tana karema mutanen dakin kallo,waige waige tafara hango Umman ta datayi akan kujeran karshe rike da karamin yaro yasa tajuya da sauri tana rike da cikinta takarasa wurin tafada jikin Umma tariketa gam tana kuka, Umma ma kuka. Da karfi tace”Umma kalli-kalli”tace “auch Umma cikina ciwo yake” sanan ta nuna Barraq,Mummy,Daddy da Amma “Umma suwaye wayanan turawan?” Barraq ya zaro ido yana kallon ta, yatako zuwa gaban kujeran datake ahankali yace”Rufaida ” murguda mai baki tayi ta kalli Abban ta tace “Abba wai waye wanan baturen? Baffa a ina kuka samo turawa?”. Maman Abd Shakur😘

mamanshakur Is all about novels.
Skip to content
Home
About
TSAFI 1to 11
← KAINE SIRRI NA 70 to 76KAINE SIRRI NA 88 TO D END →
KAINE SIRRI NA 77to87
Posted on July 25, 2016 by mamanshakur
​[7/25, 20:28] Aishat Muhammad: *KAINE SIRRI NA*
77

Kafin Umma tabama Rufaida amsa takara jeho wata tambayar “Umma maisa naga duk sunsa gilas?Umma daga ina zukazo? “Tafadi maganar tana kallon fuskar Mum. Umma takasa magana tarasa maizata yi awanan gaban farin cikin ganin yarta,harta tunasu ko bakin cikin ta manta wayanda suka taimaketa, ciki harda abin kaunar ta,mijinta. Umma takara kecewa da kuka, Alh yay jarumtar yin magana ta hanyar kallon kanin nashi yace”Young malam meke faruwa? ?explain kasamu aduhu? Maisa ta manta mutanen dasuka taimaketa da mijinta?” Mutumin ya gyara zama yace”yaya amma Rufaida sammu ta manta iyayen ta gabaki daya,da rayuwar ta nada,ta shiga duniya kaman yanda kukaji tafada dazu, duk wani Rayuwa datayi bayan ta bar gidanku tayishi ne bata cikin asalin hankalin ta,tana cikin sammu,saisa ta manta su,amma zata tunasu nan bada jimawa ba,tashin ta yanzu taganine kaman daga bacci ta tashi,rayuwar datayi kaman mafarki ne,sai ahankali zata dinga tunasu kadan kadan,kubata lokaci zata warke duk zata tunaku,wanan bawata babbar matsala bace” Rufaida data kwantar da kanta ajikin Umma ahankali tace “maganar wa Baffa yakeyi Umma?” Umma tadan shafa kanta “zan fada miki anjima”. Sai alokacin Mum tai magana “nakasa gane dis whole thing,suyawe iyayen Rufaida dahar suka mutu?ita Duduwa data kira kanta kakar Rufaida who is she then??a ina suka san Rufaida?”. Dad yay gyaran murya” d only person dat can answer that question is Duduwa! Barraq cikin fushi yace”babu wacce zai kira matar nan gidanan, juyamin kwakwalwar mata sukayi ,dey did something to her” yakama kwalar malamin “mekama Rufaida?”kowa na falon ya mike tsaye Dad ya rike hannu Barraq “son let him go,ka sakeshi,ba abunda yama Daugther,I said let him go” da kyar Barraq ya sakeshi idanunshi sunyi ja Dad ya zaunar dashi yadawo yana bama malamin hakuri wanda ya nuna bakomi. Dad yakoma kan Barraq yana mai fada”nasha fadama idan rai ya baci kar hankali ya gushe,idan kai tunanin komi everything make sense zaiyu yaron Duduwa ya tsinci Rufaida ya dauketa saisa ma Duduwa hate her soo much,understand and get it once rayuwar da daugther tayi damu tayishi ne kaman amafarki,she will remember us amma ba yanzu ba” Barraq yay shiru ya daura kanshi akan cinyar shi,yarasa mezaiyi yaji dadi,zuciyarshi na mugun zafi,kanshi kaman an zuba garwashi” Karan wayar dayaji yasa ya dago kanshi ahankali suka hada ido da Rufaida harara ta balla mishi saboda taji haushin yanda ya shake baffan ta. Jin maganar Alh yasa kallon yakoma kanshi arude yace”garin yaya?ganinan dawowa,kuhadu ku kamata a kulle yanda bazata fitaba” ya katse wayar tashin hankali ya bayyanah karara a fuskarshi Umma ta fara tambaya “lafiya Alh?” Share gumin kanshi yayi yace “mai gadin gidan hajara(kishiyar Umma) yakirani wai Hajara ta haukace, tafito sai raye raye take tana cire kaya tana kiran Rufaida,ankasa kamata dole natafi Abuja yanzu” ya kalli Dad yace”Alh dan Allah inason keban cewa da yan uwana da Rufaida Alh” Dad ya washe baki “to ba matsala”. Yatashi Mum da Amma sukai gaba Barraq yaki matsawa daidai danan da chan Dad ya rike hanunshi suka fita daga dakin. Alh ya fuskanci yayan shi yace”yaya inaso ku saurare ni, munga Rufaida shine kuma abunda muketa addu’a akai ko?”Suka amsa da haka ne. “Amma da muka ganta mun tarar da ita a matsayin matar aure, kuma ga miji salihi mai taimako ga tausayi maikuma sonta”, tashi yayi ya matsa kusa da Umma dake kallonshi ya rike hanunta “abunda nake shirin fada nasan zaimiki wuyan yi, amma inaso ki duba mutuncin mutanen nan, dakuma abunda sukama yarmu na nuna mata so,kulawa,suka aurar da ita ga miji nagari” yadanja numfashi kafin yacigaba”Alhamdulillah mun godema Allah daya bayyana mana yarmu, dudda Rufaida bata tunasu ba bazaisa mutafi da itaba,bata karkashin mu yanzu,tana karkashin mijin ta, hukuncina shine zamu barta anan mutafi madinga zuwa dubata” yakarasa maganar yana kallon Umma dake hawaye. Ahankali ta girgiza mai kai,”na yarda da abunda kace na amince,bazamu taba karbar Rufaida daga hannun Barraq ba” ya kalli Yayan shi shima ya nuna amince warshi. Kowa na dakin ya nuna amincewar shi. Alamu Alh yay ma Umma da ido. Umma ta share hawayen ta tajuya ta kalli Rufaida tarike mata hannu tace”Baben Mama” Rufaida ta kalleta Umma tace”inaso ki zauna a gidanan da wayanan turawan zamuje gida Anty ki batada lpy zamu kaita asibiti kinji” Rufaida ta lankwasa kai”Uhm Uhm Umma nidai bazan zauna dasuba, bana sonsu banason gidan,inason naje school gobe tunda nariga nai latti yau ” Umma ta mikama Alh Rayyan dayay bacci ta juyo ta fuskanci Rufaida tace “Bebin mama inaso ki saurare ni kiji abunda zan fadan miki,…”Umma tafadin ma Rufaida komi,kan Rufaida yay chaji kalma daya kwakwalwar ta yafi rikewa “ke matar aure ce!matar Barraq!. Kanta ta chusa a cinya tafara rafka uban kuka bana wasaba, “wlh bazan yardaba,Allah bana sonshi, mutumin daya shake wuyan Baffa yanzu nan wlh bana sonshi,nibazan zaunaba, kuzan bi muje gidan mu”. Yayan Alh yatashi yazo gabanta yace”Rufaida! Ya daga mata tsawa,jikinta yafara rawa dantana mugun tsoron Baffa Yaya yacika fada,ga fushi.”idan naji kin kara cewa bakison Barraq saina karyaki,young Malam yace zaki tuna komi so dolenki ki zauna dasu,yanda kika zauna dasu da haka zaki zauna dasu yanzu,shashanci banza kawai, yanzu bamu da iko dake sai yanda mijinki yace, muba butulu bane da zamu goya miki baya ba,bazamu taba godema mutanen nan tahanyar tafiya dakeba kinajina” ta dagakai da sauri tana zaro ido. ya kalli mai gadi yace”kirasu mungama” mai gadi yafita dan kiransu. Maman Abd Shakur 😘

[7/25, 20:28] Aishat Muhammad: *KAINE SIRRI NA*
78
Chapter 35 · 0% Book details