← Book details Kaine Sirrina Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 40 OF 43

Sashe 40

Kaine Sirrina Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Suna fitowa suka tarar da Amma da Muzzammil da Auta dake zaune kusa dashi yana lallashinta. Dad ya zauna Amma ta tambayeshi ya jikin murmushi ya sakar mata “cikin nanan bai zube ba,nakusa zama grandpa”.
Farin ciki ya lullube fuskarta. Mum ta zauna gefen Amma tace”any news akan son ?”Amma ta girgiza kai “har yanzu Dr bai fito yamana bayanin komi ba”. Mum ta rike kuncinta tana sauke ajiyan zuciya damuwa ya bayyana akan fuskarta. Amma ta dafa kafadarta “Hey!don’t worry,Barraq is a fighter zai warware,komi zai koma normal kaman da I promise” Mum ta daura hanunta akan na Amma ta lumshe ido”thank yhu Amma,tashi muje mu duba daugther” suka mike atare Mum ta bude dakin da Rufaida ke ciki suka shiga har alokacin tana bacci ana kara mata ruwa. Suka zazzauna. Dad ya dauko waya ya kira iyayen Rufaida ya sanar dasu komi daya faru bayan tafiyar su salati Alh yayi ya sanar da ubangiji yace”Allah yabashi lpy, in sha Allah zamuzo gobe mu dubasu”. Dad yace”no need kaida kakeda maras lafiya” Alh ya sauke ajiyar zuciyar yace”Akwai abunda ban fadama ba jiya bayan mun dawo,cikin haukar ta ta sanar mana ita tama Rufaida asiri ta manta damu ta shiga duniya, she’s paying for wot she did,baruwana da haukan ta ramin muguntar data hakane tafada ciki nida Umman Rufaida zamuzo gobe, Allah kara musu lafiya yasa kaffara ne ” Dad yace”Ameen”. Dad ya kalli Muzzammil yace”son kaje gida mana Daugther na nemanka ” Muzzammil ya girgiza kai “sai B yatashi zan tafi, Dad ina sapayan gilashin shi? ” Dad yadanyi shiru “baida wani sapayan gilass ,normally a eye clinic dinshi na India idan gilashin sukai expire yaje biyu suke bashi,so lokacin dayay hatsarin nan a kauyen Duduwa da bikin ka har gilas dinshi ya kone na tahomai da sapayan yasa,yanzu dole mu fitar dashi a duba idon achan kafin sumai gilashin dayay suiting idon a yanzu, but dat will be bayan ya warke ” Muzzammil ya sauke ajiyan zuciya “Allah sa muji alkhairi” Dad ya amsa da “Ameen “. Suna zaune a wurin DPO da wasu polisawa guda uku suka shigo Muzzammil na hangoshi ya tashi ya shigo dasu inda suke ya kalli Dad yace”Dad nakira sune saboda na fadin musu abunda Barraq yafada min da iya abinda nasani,dan duk wanda yayma Barraq abunan saina kulleshi” DPO ya mikama Dad hannu suka gaisa kafin su zazzauna. Ahankali Muzzammil yamusu bayanin komi tun lokacin dayake office Barraq ya kirashi, harya iso yaga Barraq cikin jini da abunda yafadan mishi. Dad yay mamaki yace”Nana?Nana dai dana sani? ” Muzzammil yace”Eh ita Dad” Dad yay shairu. DPO yay rubuce Rubuce kafin ya kalli Muzzammil da Dad yace”kiran sunayen mutanen nan uku da Barraq yayi acikin jini makes dem our suspects, PA,Duduwa da Nana. Cus muna bama irin maganan nan amfani sosai,but still zamu so ji daga bakin Barraq idan ya tashi. And zamu nemo Nana,Duduwa PA dan interrogating dinsu,zamu tafi yanzu zamu iya dawowa any time dan yimuku tambayoyi idan mun shiga duhu akan binciken”. Ya tashi yamika ma Dad da Muzzammil hannu suka gaisa. Muzzammil ya taka musu zuwa wajen asibiti suka shiga mitarsu,kafin ya dawo ciki ya zauna kusa da Dad. Wuraren 12 na rana likita yafito daga dakin da aka shigar da Barraq, saida ya wanke hannu da fuska sanan ya zo wirinsu yace”congratulations sir,Barraq is safe and sound,mutum daya kadai zai iya zuwa ganinshi for now,saidai patient din nata kiran sunan Rufaida Rufaida sometimes yace”Baby na I suggest akai mai me sunan ya ganta gaskiya” Dad ya washe baki yacema Dr “thank yhu sosai”, Dr yay murmushi yace “Sir akaima patient dina abunda yaketa kira plz”,Muzzammil yace”Sure,yanzu ma kuwa”. Maman Abd Shakur😘

[7/25, 20:28] Aishat Muhammad: *KAINE SIRRI NA*
84

Karfe 6 na safe taima Mum da Amma harda Auta da fuskarta tai suntum ya kumbura saboda kuka a asibiti. Duk suna zaune Dad ya dauki Auta dake kuka yana lallashin ta wata likita tafito daga wani hadadden Daki. Tana sanye da farin coat data daura akan riga da wandon dake jikinta,hannayeta sanye da hand gloves,tasanya iD dinta a wuyanta da aka rubutu sunanta ajiki “Dr Rukayya Sadau”. Takaraso ta tsaya agaban su Dad tace”Ina iyayen Patient Rufaida? ” Dad ya mike da sauri tace”ku biyoni office ” Dad da Mum sukabi bayanta. Ta zauna su Dad suka zauna bude file din Rufaida tayi tana yan dube dube da karance karance. Kafin ta kalli Dad tace”Sir jiya kace bata dade dayin bari ba da ina tambayarka akanta?” Dad ya gyada kai “yes tai bari 2 days ago” “an mata wankin ciki ne bayan tai barin?” Dad ya girgiza kai”no,Doctor yace cikin yariga yafita basai anyiba, kawai mu dinga bata abinci mai kara jini ajiki da magungunan daya bamu” Dr Rookey Sadau tadanyi rubutu acikin file din kafin ta dago kanta ta kalli su Dad murmushi Kwance akan fuskarta tace”Cikin bai fita ba,sun tsayar da jinin da wuri,maybe saboda yanda tai bleeding din yasa basu gane da wuri cikin nanan ba,but cikin yarku nanan for now inhar zakubi kaidodin dazan baku ” Dad yama kasa magana saboda farin ciki Mum ce tai magana “menene kaidodin?” Dr Rookey tace”ku hanata daga any object ko abu mai nauyi,sanan any exercise irinsu tsalle-tsalle,guje-guje da dirke-dirke tadena yi saboda suna kawo zuban jini hakanan ko zubar ciki ma. zaku kiyaye abubuwan cinta tana yawan cin abinci mai kara jini sanan ta guji abinci mai siga sai shawarwarin dazan baku shine Mai ciki ta dinga yawan cin wake saboda yana karama yaron cikinta kaifin kwakwalwa sanan yana bama maiciki ruwan Nono sosai. Shan kankana yana gyara fatar yaro acikin ciki,kuma yana karama yaro kaifin kwakwalwa. Cin ganyen irinsu ugu da alayyahu yana kara jini ajikinsu,Sanan alokacin da mace keda ciki wanda ke yawan sata amai tadinga cin kwakwa (coconuts)da rake(sugar cane) yana rage yawan amai. And suna hana yaro ya dinga kurjaren zafi, wutar dare and d rest bayan an haifeshi,kuma suna rage ciwon nakuda. Cin dabino(Dates) strengthen the muscles of the uterus akarshen watan haihuwa. Kuma Yawan cin dabino yanasa mace ta bude ta cikin sauki batare da an karata ba a lokacin haihuwa. Cin dabino ga mai ciki dama wacce ta haihu yana karama ruwan Mama elements din da ake bukata na karama yaro lafiya da kariya daga kowace irin cuta. Sanan sai shawarwarin kula da yanayi (mood)din datake ciki. Yanada kyau mai ciki ta kasance cikin farin ciki kowani lokaci,ta kalli abu mai kyau,taji abu mai kyau,ta sha abu mai kyau,ta shaki kamshin abu mai kyau. Dan ko wani hali mai ciki ke ciki haka dan cikin ta ke ciki. Yanada kyau mai ciki ta nisanci bakin ciki ko bacin rai,sanan kartaji haucin kowa kota tsani wani abu,ko ta dinga bakin ciki dawani. Dan duk hali /yanayin damai ciki ke ciki yana affecting yaron cikin ta. Ta kalli Mum tace” Ma ko film din ban tsoro baaso mai ciki na kallo inhar suna bata tsoro irinsu vampires films,Horror films and d rest duk bai kamata ba. (It is important to have good feelings,good thoughts, and not to carry grudges,have fear of something or be unduly worried about something. A pregnant woman should remain calm,happy and should not be allowed to be over concerned and allow herself to be overtaken by grief. The thoughts you generate within urself will affect the kind of disposition the child will have. If u are sad and miserable the child will be equally affected. REMEMBER! it is the mother’s womb that is carrying the baby and that the baby is affected by whatever she is thinking, feeling, reading and listening to. It is better and advisable for a pregnant woman to keep a good company, to read good books. Example The Holy Qur’an.) likita tace “zaku iya tafiya sai jibi zamu sallameta dan 16prime ce,we need to monitor her” Dad da Mum sukai godiya suka fita. NOTE:Duk abunda nafada akan mai ciki yakama ta tayi hakane,gaskiya ne,Allah sa wasu su amfanu da my little ilimi, Ameen. Maman Abd Shakur😘

[7/25, 20:28] Aishat Muhammad: *KAINE SIRRI NA*
86

Dr Rookie Dad yay ma bayanin komi babu bata lokaci tasa nurses suka gungura Rufaida zuwa dakin da Barraq yake batare da anbar su Dad sun shiga dakin ba.

Da kyar Barraq ya furta “My Rufaida kece?”Jin motsin dayayi a dakin Dr Rookie tai murmushi takama hanun Rufaida ta saka a cikin hanunshi tace”ga Ruffy dinka anan,bacci take,karkai magana da yawa cus of ur condition,take care” tajuya ta mayar musu da kofa tafita. ahankali Barraq ya murza hanunta tareda lumshe ido “get well soon Baby na,naso zan iya ganinki yanzu”yakai hanunta kan bakinshi ya sumbaci hanun ahaka bacci yay gaba da shi.
Washe gari akabar Su Dad suka shiga ganinsu har alokacin bata tashiba sai Barraq da idonshi biyu Mum ta rungume shi gam tana kuka Auta ma haka da kyar sukai shiru. Dr yabama Dad takardar transfer zuwa India saboda yimai gilash.
Karfe 12:Am na Rana Rufaida ta farka ahankali ta tashi zaune daga gadon da kyar tana yatmutse fuska. Kallon dakin tafara bataga kowaba,daga hanunta dazatayi da zumar sosa fuska taji kaman an riketa, da sauri ta juyo ganin Baturen da tasan ance yamutu yasa taji kanta yafara juyawa yayinda zuciyarta ke tashi tanajin wani irin amai na taso mata, bata ankara ba tafara kwara amai da bakomi ciki sai ruwa yellow Mum dake zaune wajen dakin tana karanta jarida ta ajiye a gefe ta shigo dakin da sauri ganin Rufaida na amai yasa takoma waje da gudu takira Dr. Dr da Nurses suka biyo bayan Mum aka shigo dakin daura Rufaida sukayi akan gado suka fita da ita zuwa dakinta. Barraq yace Mum maiya sami Rufaida? ?ta rike hanunshi Son karka damu amai ne kawai.

**********

Bayan sati biyu.
Chapter 40 · 0% Book details