← Book details In Bani Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 86 OF 101

Sashe 86

In Bani Complete Hausa Novel · about 8 min read

"i will take shirun ka as No, tausayi ake cirewa agasa mutum da kyau inba hakaba bazata warkeba, in akwai any elderly person around mai experience haka please kacire son ranka kabari amata kodan ta warke inta warke dukdai kaine ta warkemawa ko" shiru yayi bai tankataba taja prescription sheet tarubu ta magungunan dazai psayo ta mikamai tace "jeka siyo kadawo kutafi" fita yayi bayan ya karba ta kalli Hamidan dake kwance tace "saura kuma dazaran yazo ya lallabaki yamiki dadin baki kibashi, mu matane mune da wahala su da morewa, make sure kin warke wajen yay healing tass kafin kikara bari yayi kinajina ko, u are a small girl so take care of yourself, ko fushi zaiyi yayi inhar kinajin zafi koya ya ne karki bari yayi maza kina ganinsu haka jarabarsu tafi karfinsu, karki biyemai kinji yar kirki ki kula da kanki please, in kina tare da wani atare idan kikaga bazai barki kihuta ba kitafi wajen su kihuta inkin warke kidawo kinji dan maza mugaye ne baiki kibude mai kafa anjima ba zaiyi duk yanda yaga damane dake yabarki da wahala" gyadamata kai tayi maganganunta na shiga ranta sosai suna zama, zata cigaba da maganan Aadil ya shigo dakin, murmushi tayi tace "yauwa zo dauketa kutafi, idan kukaje reception kayi clearing bill dinku" ta mikamai bill paper karba yayi yakaraso gadon yana kallon Hamidan dataki kallonshi yadagata ahankali yafita da ita daga dakin bayan yayma Dr godiya yana gama biyan komi yay waje da ita amota yasata ya kalleta yace "mekikeso cin nasiyo miki?" yay maganan ahankali cikin muryan lallashi, turomai baki tayi tace "banson komi" shiru yayi yana kallon ta nakusan 5min kafin yatada motar cikeda sanyin jiki Yay reverse yajuya yafita daga asibitin yahau kan titi hanunshi yamika yakama nata yadan matse cikeda damuwa ganin yanda take fushi dashi ahankali yace "am sorry Dewdrop, u were so sweet and warm zarewane kawai banyiba wlh i can't wait ki warke, let's do it again ko mai shegen dadi bazai miki zafi ba" shiru tamai ta fizge hanunta ta lumshe ido kaman maijin bacci, hira ya shiga mata duktai kaman bata jinshi ahaka har suka karako gida, horn yayi mai gadi yabude gate ya shiga, parking yayi yafito ya zagayo ta bangaren ta yabude kofan cikin siriruwar muryanta datai yaushe sosai tace "ni wurin Mami zani" shiru yayi yana kallonta ganin yanda take kumbure kumbure tana ciccin magani, yasan kuma shimai laifine yau dole ya lallabata yasa yace "okay your majesty hakan za'ayi" daukarta yayi ahankali yafitar da ita adaidai gaban shashin Mamin kaman zata sakinmai kuka tace "nika saukeni" da sauri ya kalleta murya chan kasa kaman wanda ke tsoronta yace "but u can't walk properly d place will hurt" makemai kafada tayi hawaye ya gangaro daga idanunta tace "nika saukeni nidai" ganin kaman zata sakinmai kuka yasa yasauketa ya rungume hanunshi a kafada yana kallonta, ance fadan dayafi karfinka saika maidashi wasa yau rigima takeji dole kuma yayta aikin lallashi danshine yay aika aika, turo baki tayi cikeda shagawa tace "nika dena kallona to" juyar da kanshi gefe yayi yana hadiye dariyan dake cinshi ahankali tabude kofa babu kowa a falo, daga kafa tayi da kyar ta shiga tana cije baki yabita da kallo ga tausayin ta gakuma dariya dake cinshi.

"oh Allah!

Yanzu shiyay wanan aika aika haka? jibi yanda yakomar da Hamida mai koyon tafiya, kaman mai tatata" kaman ance ta juyo dan jitayi ajikinta ana kallonta, hada ido sukayi kaman zatai kuka tace "kallona kake ko" da sauri ya girgiza mata kai yace "a'a your majesty bari ma naje nadauko magungunan ki kisha nabarsu amota" yarufo kofar yana danne dariyar shi yay hanyar tsakar gida, karasawa ciki tayi so kawai take ta kwanta dan yanda take tafiya kaman ana watsa mata barkono a wurin, karasawa tayi tabude kofar dakin Mami ahankali tai sallama chan kasa ganin dakin da duhu yasa tasan Mami bata ciki hala ta zaga backyard kokuma tana wurin yan aiki, maida kofar tayi ta rufe ta zare hijabin dake jikinta, jikakken gashin kanta dakeda lema har lokacin ne suka barbazu akan kafadarta tana sanye da doguwan rigan daya sakamata dazu takawa tayi har wajen gadon bamata gani sosai dan babu wani ishashen haske adakin, ahankali tafada kan gadon sabida zafin datake ji, jin tafada kan mutu yasa ta tashi da sauri tai baya tace "laaaa Mami bansan kina kan gad......" garin komawa baya yasa tai baya zata fadi gabaki daya tai kara a tsorace.

"Mamaaa!" da sauri Aabid da ihunta ya farkar da shi dan firgita yayima yadaga kanshi ganin zata fada kasa ga gadon Mami nada tsayi yasa da sauri yasa hannu yarike hanunta ya janyota da karfi, fadawa jikinshi tayi tana numfashi wet gashinta ya mari fuskarshi, sama sama take numfashi sabida zafin datakeji a wurin, ta kwantar da kanta akan kirjinshi daidai lokacin Aadil yabude kofar dakin Mami cikin cool voice dinshi yace "Dewdrop here are the dru...." yay maganan yana kunna wutan dakin, dakin yay haske, kasa karasa maganan yayi ya tsaya chak yana kallon Aabid dake sanye da singlet da Hamida dake kan jikinshi atare daga Aabid har Hamidan suka kalli Aadil din daya shigo sabida hasken da dakin yayi da sauri Hamida tajuya ta kalli Aabid datake kan jikinshi dan bama tasan waye kwance ba tadauka Mami ce, juyawa da sauri tayi ta kalli Aadil kirjinta nawani irin bugawa tama kasa koda motsi, sosai Aadil yaji wani abu ya tokaremai kirji ganinsu ahaka, dauke kai yayi da sauri yama rasa mezaiyi ya kalli maganin dake hanunshi muryanshi nadan rawa sosai yace "yo...ur...magungunan ki" ya ijiye da sauri kan saman cupboards din dake wurin ya juya da sauri yafita daga dakin, da sauri Aabid yature Hamidan daga kan jikinshi kara tayi sabida zafin dataji hawaye nazuba daga idanunta, matsawa yayi gefe ganin yanda takeyi har lebe tana cijewa sabida turatan dayayi yasa yace "sorry" share hawayen dasuka zubo mata tayi batare data kalleshi ba tace "bakada lafiya ne Ya Aabid?

Jikin ka zafi" sauka daga kan gadon yayi batare daya kalleta ba dan baiso yamata second look ayanda take dinan yace "eh nasha magani" "Allah kara sauki" tafada kaman zatai kuka, Ameen yafice daga dakin da sauri.

Da Mami Aadil yaci karo zai shiga kitchen tsabagen yanda baiganin gabanshi da kyau da sauri Mami takoma baya tace "kai lafiyan ka baka gani ne?" jingina yay da bango ya lumshe ido da sauri kirjinshi namai mugun zafi.

"Aadil" Mami takirashi, ahankali yabude idanunshi ya kakalo mata murmushi, Murmushi tamai cike da so tace "yunwa halan kakeji wanan dabaka ganin gabanka kashigo kitchen kaman tababbe, sai kace wanda ake ingizowa" dan murmushi yamata da muryanshi dahar ta chanza kala yace "mekika dafa mana?" "yana dinning tuntuni nagama na shigo duba cake dake oven ne, ya jikin Hamidan tana ina?

Dan uwanka baida lafiya yanama dakina yana bacci hala ka duboshi adakinshi baka ganshi bane, wlh yana dakina bacci yake sonake ma naje natada shi yanzu yazo yaci abinci tun safe yake bacci baici komiba" daidai lokacin Aabid shima ya shigo kitchen din yana kallon Aadil, murmushi Mami tayi tace "talking of the devil kaganshi yatashi Aadil" juyowa Aadil yayi ahankali ya kallai asanyaye Aabid ke kallonshi shima, murmushi sosai Aadil ya sakin mai ya matso kusa dashi yana kallon fuskarshi kafadarshi ya daka cikeda wasa yace "rascal, meke damunka ummm, come here" yabashi hug ta hanyar sashi a jikinshi, wani irin ajiyan zuciya Aabid yasaki ya rungume dan uwan nashi back tight, murmushi Mami tayi tace "kunga ku wuce muje kuci abinci" tai gaba abinta, dagoshi Aadil yayi kaman zaiyi kuka yace "let's go kaci abinci am taking you to the hospital dakaina and i don't wanna hear anything inba hakaba i will call Uncles dinmu nafada musu komi" yay maganan yana hararanshi, ahankali yace "kasha maganin ka?" gyadamai kai Aabid yayi trying to be strong yace "yes nasha" shiru Aadil yayi yana kara kallonshi kafin ahankali yasake hugging nashi sosai he's so jealous kaman zai shide yakeji duk in yatuna yanda yaga Hamida akan kirjin Aabid gashinta a barbaje tasaka dogon riga and she's not wearing any bra dan baisaka mata ba, he's so jealous abu yatokare mai wuya but he can't help it dudda yasan is none of their fault is just accidental, and he's feeling guilty dan yasan why his brother is sick but baida wani maganin rashin lafiyan shi dazai iya bashi ayanzu, and yana son dan uwanshi more than life itself, he's just praying Allah yabama Aabid wacce zata maye gurbin Hamida azuciyar shi even more, babu randa zaiyi salla dabazai mai wanan addu'an ba and he knows lokacin yakusan zuwa, sakinshi yay ahankali idanunshi yay ja sosai yace "let's go and eat" gyadamai kai Aabid yayi dan baida karfin magana yau suka fita daga kitchen din.

Zama duk sukai akan dining Mami ta zuba musu abinci ta kalli Aadil tace "ina Hamidan maisa baka kawota nan ba kabarta a shashin ku?" batare daya kalli Mami ba yana kokarin debo abinci yakai baki yace "tana dakin ki" "au tana dakina shine baka fadamin ba" tai maganan tana tashi daga kan kujera, duka ta dakamai abaya tace "Allah shiryeka" ta kalli Aabid take juya coffee tace "sha son am coming bari naduba Daughter na" gyada mata kai yayi Mami tawuce daki.
[1/7, 1:34 PM] Aishat Muhammad: ......

Bude kofa Mami tayi ta shiga dakin tana kallon Hamidan dataga ta lulluba da bargo harka, da sauri takarasa jikin gadon.

"subhanallahi daughter na jikin ne" tai maganan tana yaye bargon data lulluba dashi takai hanunta tadaura akan wuyanta, sanyin hannun da Hamida taji ajikinta dake running temperature yasa tabude idanuwanta dasuka mata nauyi ahankali, ganin yanda idanuwanta suka kumbura yasa Mami kaman zatai kuka tace "Hamida na sannu kinji, meke damunki?
Chapter 86 · 0% Book details