← Book details In Bani Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 44 OF 101

Sashe 44

In Bani Complete Hausa Novel · about 8 min read

Misalin 10 nadare Abba ya shigo gidan, abinci Mama takaimai, sai bayan yagama ci yay wanka sunyi shirin bacci sanan Mama ta gyara zama ta fuskance shi fuskanta adaure, ahankali tace "tundazu kadawo kai shiru ina kallonka nazuba ido inji kozakamin maganan amma kai shiru ko kala bakace min bako, ka dauki y'ata kabama mahaukaci baka fadanmin ba baka shawarceni ba saidai naji abakin wasu sabida kaganni shiru shiru kome kakeso shinakeyi ina binka sau da kafa saika nemi ka takemin hakkina a matsayina na mahaifiyar Hamida gas...." da sauri Abba yatareta ta hahanyar cewa "Hamida ba yarki bace kadai ba nima y'ata ce, sanan yanda abin nan kemiki ciwo haka nima yakemin ciwo, yakike so nayi eh Haleematu?

Umma ita taje tahado komi kawai nima ganin mutane nayi yau da kayan saka rana sun taho, so kike na nabada Umma agaban su?

So kike amana kallon kananun mutane da basusan mesuke yiba?

Yayama zanyi eh" da sauri Mama tace "gaskiya bazan yardaba, nibazan bari Hamida na ta auri mahaukaci ba nafadama bazan bari ba kacema Kaka anfasa, nibazan bama y'ata mara lafiya ba" shima Abba cikin tsananin bacin rai kyace "sokike ta tsinemini?

Ke bakiga Umman bane?

Yaya zanyi da ita mahaifiyata ce dole kome tace namata biyayya, yaya zanyi Haleematu fadamin" fashewa da kuka sosai Mama tayi takasa cewa komi hakan yasa ya dafe kanshi yay shiru yasan Mama da mugun hakuri kuma yasan da gaskiyan ta amma yaya zaiyi?

Shi kanshi abin yafi karfinshi, ahankali ya janye hanunshi daga kan
goshinshi ya matsa kusa da Mama ya rungumota jikinshi yana shafa bayanta yana jijjigata harta rage kukan ahankali yace "kiyakuri Haleematu, i need your support more than anything ayanzu, kece karfi na, idan kika karaya haka ninai yaya eh?

Nasan Umma bata kyautaba amma kiyakuri, bamu miki adalci ba amma kiyakuri uwata ce dole nabi abinda tace, addu'a zamubi yarmu dashi, babu wanda ya isa yahana kaddara faruwa, kuma rabo na kisa bamusan me Allah yagani yahada suba, kawai mubisu da addu'a kinsan Allah na karban addu'an uwa akan yaranta, mumata addu'a kinji muga me Allah zaiyi, am sorry for hurting you kinji best wife, stop crying" gyadamai kai Mama tayi ahankali hakan yasa ya sumbaci gaban goshinta yasake rungumeta da kyau yace "akwai wasu kudi danake expecting once anbiyani zan baki kije ki siyo mata duk abinda yadace kinji" gyadamai kai tayi nan yadinga bata kalamai masu ddi da sanyaya rai harta sauko sosai ta share ta barma Allah komi kawai ta tasa addu'a agaba.

Kwanaki nataja sosai gidaje biyun aketa shirye shiryen biki, gabaki daya Aadil baida lafiya magungunan hausan da Baffa yasa akemai da in yasha ma amai yakeyi gashinan gashinan ne kawai mugun so yake yaga Hamida bana wasaba, gashi kullum yana dakin Mami inyaga Aabid wani irin tsoranshi yakeji yayta tuna yanda yamai mugun duka yay lamo koya kulle ido, Aabid gabaki daya yadawo wani iri shima saiyahau ciwon abun yama Mami yawa ga Aadil ga Aabid Abba yay wani irin ramewa shima haka dai suka dinga lallabawa Dr na zuwa treating nasu a gida, Aadil harda drip yasha kusan hudu.

Kaka takawo yar buzuwa anata ma Hamida gyaran amare bana wasaba, gabaki daya Hamida duktai zuru zuru kullum saitaci kuka, ko kadan batason auren nan dudda kullum tunanin Aadil take bana wasaba takuma rasa mesa take tunanin shi, tasan yana chan yana nemanta yanzu yana kuka rabonta dashi tun yana asibiti.

Kuka, kukane aikinta gashi tai wani irin kyau tai haske bana wasaba, fatarta dama yanada taushi saiya kara wani extra ordinary taushi, ga sheki ga kamshi datake yi, ana saura sati daya biki family Aadil suka kawo akwati nagani nafada guda 12, Kaka harda rawa tama manta da Faruk da rabonta dashi yafi sati, dasuka tashi tafiya aka hadamusu shatara na arziki, Hamida kin duba kayan tayi Zainab da Ihsan sai rawa suke sunata murna Hamida zatai aure, Mami dai kullum bayan magrib takan koya mata yan dabaru na zaman gidan miji, ko kadan tarasa sukuni bama ta iyacin abinci hakan yasa wani irin ciwo yakamata tafara zazzabi bana wasaba, har aka fara sha'anin biki yayyinta duka harda su Ayush duk sunzo sai mamakin aurenta suke yaushe Hamida tai miji, yaushe tai saurayi kawai sunji bikin ne, ranan walima saida Abba yakira wata likita sabida yanda ta dinga kwara amai hankalin Mama duk yabi yatashi sai sannu kowa yake mata.

Ana gobe daurin auren Abie yakusa karamin hauka adakinshi, baisan me Ozo zaimai ko Aadil gobe idan an daura auren ba, baisan wani hukunci Ozo zai yankemai ba, dudda dai har yau baisan meye dalilin dayasa Ozo yace kar Aadil yasake yay aure ba amma yadamu, abinda haryau yake bashi mamaki shine Ozo yariga ya maidashi yaro ababba to menene dalilin shi nacewa karya sake yabari yay aure, kodai aure zaisa Aadil yadawo normal ne?

Ajiyan zuciya ya fuzar yana fifita kanshi da hulan daya zare daga kanshi yacigaba da tunani, gashi yanzu Ozo bai bayyanar mishi ba koda warning ne yabashi ba, kawai yay shiru yasakamai ido kome yake planning oho.
********
Hausawa sunce rana bata karya!

Yau asabar misalin karfe biyu na rana dubbanin jama'an dake cikin babban masallacin janbulo suka shaida dauren auren Hassan Abdullahi Aadil da Amatullah Isma'il akan sadaki dubu dari inda jama'a da dama suka hallarci auren suka shaida, Aadil dayaci gayu sosai ya rame kaman bashiba yana tareda su Baffa da Suleman dan tun safe yau ba'aga Aabid ba sai murna yake yana tsalle, yau yay wani irin kyau na musamman yawani irin cika yafito sak cikakken namiji dashi kodan yau auren shine oho amma dai yau akwai wata irin haiba da kwarjini daya kara na musamman dahar abin saida yabama Baffa mamaki yadai share yacigaba da attending to jama'a, Abba ma sai neman Faruk yake bai ganshi ba dan rabon shi da Faruk tun sati daya daya wuce.

Misalin karfe nine nadare akazo tafiya da amarya Hamida kuka kaman zata shide harsaida tasa Mami kuka da kyar yayyinta da yan uwanta suka rakata gidan mijinta daya mugun hadu.
[12/1/2019, 8:44 PM] Aishat Muhammad: _
IN BANI
39 - 40
Maman Abd Shakur
Da yatsa Ozo dake jikin bangon dakin yasake daga Abba yabugashi da kasa yafesomai wani abu dayake nan kaman hayaki daga bakinshi jikin Abie, wani irin ihu Abie yayi.

"wayyo Ozo wlh, wlh, wlh natuba dan Allah azabar nan tamin yawa bazan iya daukar taba, narasa yanda zanyi nahana auren ne mariki nane yahada, saisa narasa yanda zanyi, wayyo Ozo" dawani irin gudu Mami tazo ta tsugunna daidai inda yake kwancen akasa dagashi saidan gajeren wando tarike mai hannu arude takirashi.

"Abie" kojinta Abie bayayi sai kuka dayakeyi yana sosa jikinshi dayay rudu rudu kaman anzane shi da bulalan inji, da sauri Mami tasake jijigashi ta kwalamai kira ganin yanda yake abu kaman mahaukaci.

"Abie, Abie" afirgice ya kalleta saikuma ya kalli bango dakin ganin Ozo yabace yasa yawani irin rungume Mami ya daura kanshi akan cikinta yana wani irin nishi kaman wanda ake shirin kashewa yagudo, ya ririketa gam yace "help me, Maryama ki taimakamin dan Allah kitaimaka min, Ozo zai kasheni na karya doka akaro nabiyu" sosai gaban Mami kewani irin faduwa all maganganun daya fadi na dawomata kaman yanzu yayisu da sauri tace "me kake nufi dakai kokarin hana auren kakasa marikin kane yahada auren Abie?" da sauri Abie yadago kai ya kalleta suka hada ido yana wani irin nishi yana sauke ajiyan zuciya "kai shiru bakace komiba, waye Ozo?

Wani doka ka karya" Mami ta tambaya kaman mai tuhuman shi akan wani abu lumshe ido yayi da sauri dan baimasan lokacin daduk ya faffadi abubuwan nanba, bazai iya jure kallonta ba hakan yasa yatashi ahankali yanadan dingishi jikinshi yay rudu rudu yafada gado yaja bargo tundaga kai har kafa ya lulluba Mami tabishi da kallon tuhuma zaitai magana saikuma tai shiru ta buga tagumi ahankali tana kallon kowani bangare na dakin kaman yauta fara ganin dakin, takai kusan awa daya ahaka kafin ta tashi tai wajen wardrobe tabude wardrobe din ta zaro wani doguwan riga na bacci mai dogon hannu ta zura tadau hula tasaka sanan ta maida sip din tarufe tadau hijabinta tasaka tasa silipas ta fita daga dakin, dakin Aadil ta shiga tana kallonshi har lokacin bacci yake maida kofar tayi tarufe ta shigo abakin gadon ta zauna ta daura hanunta akan kunenshi tana shafa kunen ahankali tana kallonshi maganganun Abie nadawo mata dasuka mugun daure mata akai, abinda ma yafaru gabaki daya ya daure mata kai, ihun me Abie yake, daga ina yake dan ai data shigo daki baya daki bata ganshi ba, tanadai cikin wanka taji kaman an wurgo abu daga sama, menene wai meke faruwa? wani irin ajiyan zuciya ta sauke kafin ahankali takama hanun Aadil din tarike gam tana kallon fuskanshi da sauri ta share hawayen daya zubomata ahankali tace "Aadil, My Hassan, my boy, i want you to be fine, Aadil ka warke, be fine and help me understand everything kaji, yau is a happy day for you, my not so little Aadil, my not so little yaro, Aadil dina is now a grown-up yaro magidanci mai iyalinshi" lumshe ido tayi da sauri jin hawaye zasu zubo mata da kyar ta iya ta hadiye kukan dan she really wanna be strong for her kids takai kusan 2min ahaka kafin tabude idanun ahankali ta kalli sama ahankali tace "Ya Allah, banda abin dogaro saikai, Ya Allah namika dukkanin al'amurana gareka nasan komi dayake faruwa jarabawa ce agareni kuma inaso inci jarabawan ka agareni, Ya Allah kabama Aadil lafiya Ya Allah ka sanyama auren nan dayayi albarka, Ya Allah ka kulamin kakuma tsaremini yarana aduk inda suke, Ya Allah ka tsaremin Aabid kadawo min dashi lpy Ya Allah kabama dan uwanshi lpy" ahankali tace Ameen kafin ta mike tabude bayinsu ta shiga ta dauro alwala tafito ta shimfida dadduma tafara salloli, sai wuraren uku da rabi sanan bacci yay gaba da ita, hayaniyan jama'a ne ya farkan da ita da asuba kallon gadon tayi ganin Aadil na bacci yasa ta tashi ta shiga ta dauro alawala tazo wurin gadon ta bubbugamai kafa tana murmushi yanda yay kyau da bacci.
Chapter 44 · 0% Book details