← Book details In Bani Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 29 OF 101

Sashe 29

In Bani Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wani irin tsayawa Aabid yayi agabanshi yay folding hanunshi akirji yana wani irin kallonshi, ahankali Aadil ya saukar da kanshi dake rawa sosai kasa hakanan yaji yana wani irin shakkan Aabid din for the first time in his life, ahankali kanshi na rawa sosai ya matsa ta gefenshi batare dayace komiba yazo zai wuce shi da sauri, wani irin fizgo hanunshi Aabid yayi azuciye yadawo dashi inda yake har saida yabuge bayanshi da bango cikin tsawa yace "where do you think you are going?" sosai idanunshi suka cicciko da hawaye kaman maison kara tantance anya Aabid ne wanan yadan dago kai ya kalleshi ganin shine dai yanamai wani irin mugun kallo yasa ya saukar da kanshi dake rawa sosai kasa cike da tsoro dawata irin murya chan kasa yace "i want to go to Hamida My wife's place" wani irin fizgoshi Aabid yayi yarikemai wuyan riga yace "karka kara cemata your wife" makemai kafada yayi ahankali atsorace hawaye na gangarowa daga idanunshi yace "i don't want to stay here, i want to go to Hamida my wife's place" cikin wani irin bakin zuciya Aabid ya sakeshi yadaura hanunshi kan belt din jikinshi yana kwancewa yana zarowa yana kallonshi yace "karka kara cemata your wife" makemai kafada Aadil yayi hawaye na fita daga idanunshi sosai yace "she's my wife i will marry her just like Abie and Mam..." wani irin zaulamai belt din Aabid yayi da duka karfinshi cikin fushi sosai yace "karka sake cemata your wife" makemai kafada Aadil yayi yafashe da kuka sosai yana sosa kirjinshi da cinyarshi da belt din yasama sabida azaba da zafi dayaji yace "Hamida is my wife" zaulamai belt din yayi da shegen zafi hakan yasa yay ihu cikin kuka sosai yana sosa wajen yace "stop beating me Bid" shima Aabid cikin ihu yace "kaima stop calling her your wife and karka kara rungumeta, she's my Jewel" Make mai kafada Aadil yayi cikin kuka sosai yace "Hamida is my wife" wani irin mari Aabid ya daukeshi dashi da saida yaga wuta da jiri cikin wani irin layi idanunshi najuyawa sosai yace "she's my wife" bugashi da bango Aabid yayi ya shiga dukanshi sosai yace "kai mahaukaci ne, Aadil kai mahaukaci ne bazaka taba aure ba danba abinda kasani kanajina, u are mentally unstable, kai pagal ne stay away from my Jewel kanajina mahaukaci" makemai kafada Aadil yayi yana fitar da numfashin da kyar yana kuka sosai yace "she's my wife" belt din daya yar yakara dauka ya shiga dukanshi sosai kaman uba da d'a yace "kai mahaukaci ne Aadil bakada lafiya bazaka taba auren ta ba, bakada any use a dis life, stop touching and hugging my Jewel, stop calling my Jewel your wife inba hakaba sainai ma shegen duka" make mai kafada yayi wanan karan yakasa magana tsabagen kirban shi da Aabid keyi, hakan yasa Aabid yajawo belt ya shiga dukanshi sosai Aadil na ihu yana kuka sosai yana rirrikemai riga yanaso ya rungumeshi.

"stop beating me Bid, stop beating me please" bude kofan akayi Mami ta shigo ganin yanda Aabid ke dukan Aadil da belt yasa tazo wajen da mugun gudu.

"Aabid, subhanallahi, innalillahi wa innailaihi raji'un, Aabid zaka kashe dan uwanka ne" tarike mai kafada tana kokarin rike belt din hanunshi tureta yayi ta hanyar fizge kafadarshi yacigaba da dukanshi Aadil dake ihu daidai lokacin Abie da Baffa sun shigo sabida hayaniya da salatin Mami dasukaji, wani irin fizgoshi Abie yayi yace "Aabid kana hauka ne?" fizge kanshi yayi daga hannun Abie yacillar da belt din yafara dukanshi da hannu Abie najanshi amma dukanshi yake yana neman gagaran Abie tsabagen karfi, wani irin tsawa Baffa yadakamai ganin numfashi na neman gagaran Aadil din, da gudu Mami ta daga Aadil din ta rungume tace "ka dakemu tare kaji Aabid" hannu Aabid yadaga zaikara kaima Aadil din duka dudda Abie na rikeshi Baffa ya daga sandarshi ya rafkamai akafa.
_Slm Fanmily_
_Daga yanzu typing system dina will change, zan dinga skipping a day but duk ranan posting zan dinga yin 2pages in sha Allah_.
_Thank you_
[11/15/2019, 8:41 PM] Aishat Muhammad: _
IN BANI
Maman Abd Shakur
25.....
_this novel is for sale, karki karanta in baki biyaba, in kika karanta ina binki bashi, pay anan or pay achan, your choice_
_masu fitarmin da novel waje kuda Allah_
_in kinason this novel zaki turo 300 ta 3107021073 first bank aisha Muhammad saiki turo evidence of payment ta watsapp number na 07012181461_
_you can also send MTN card ta watsapp na 07012181461 sainai adding dinki a group din danake posting_
Har Aabid yajashi yafitar dashi daga dakin wani irin faduwa gabanta yakeyi takasa daina kallon kofan kirjinta nawani irin bugawa tanajin wani irin tsoro, ihun dataji na Aadil yasa ta dafe chest dinta danjin ihun tayi har karkashin zuciyan ta, sakejin ihun tayi tareda kuka hakan yasa tawani irin zabura ta sauka daga kan gadon tai hanyar kofa dagudu.

"auchhhh" tai wani irin kara sabida yanda taji allauran dake jikinta yawani irin chakanta, ita gabaki dayama ta manta dashi, komawa da baya tayi ahankali jikinta na rawa sosai tasa hannu ta cizge kanulan dudda hanunta na jini amma ko damuwa batayiba, tai hanyar kofa tabude ahankali kaman wacce tazo sata tana kallon ko'ina, tunda take bata taba ganin hadadden palo hakaba, hanyar inda taji kukan Aadil sosai tayi zuciyar ta namata wani irin rawa babu kowa a shashin daidai gaban kofan datakejin kukan sosai ta tsaya takasa budewa.

"kai mahaukaci ne, Aadil kai mahaukaci ne bazaka taba aure ba danba abinda kasani kanajina, u are mentally unstable, kai pagal ne stay away from my Jewel kanajina mahaukaci" da sauri ta runtse idanunta ta dafe bangon da sauri harcikin zuciyarta taji zagin.

"she's my wife, Hamida is my wife" taji muryan Aadil saikuma taji wani irin karan saukan belt ne ko bulala oho, ihu da kukan Aadil taji sosai yafashe da kuka itama kukan tasaki batare data saniba ta daura hanunta akan kofan tanajin wani irin radadi da ciwo aranta, kwas, kwas, karan takalmi da alamun gudu dataji yasa arude tafara waige waige tana kuka sosai jikinta na rawa tana neman inda zata buya, wani babban hadadden flower verse silver data gani gefen kofar su ga hadaddun flowers aciki yasa tai sauri taje bayan verse din ta tsugunna talabe ta daga kanta ta flowers tana kallon kofan dantaga wazaizo ya wuce, Mami ce tazo da gudu hartana neman faduwa ta bude kofar dakin ta shiga da gudu taji Mami ta kwala kara.

"Aabid, innalillahi wa innailaihi raji'un, Aabid zaka kashe dan uwanka ne" wani irin taushe bakinta tayi da hannayenta duka biyun dan bataso kukan datakeji yafito, karan bude kofan datasake ji yasa tasake dagakai ta leka ta tsakakanan flowers wani tsoho tagani da dan magidanci sun shiga dakin cike da tashin hankali, taji muryan namiji yace "Aabid kana hauka ne?" kukan Aadil tacigaba da ji dake fita da kyar kanajin sautin kukan zakasan ya galabaita bana wasaba, muryan Mami taji tace "ka dakemu tare kaji Aabid"....

Rafkamai sandar Baffa yayi akafa da karfi, hakan yasa Aabid da idanunshi sunyi jazur ya dago kai ya kalli Baffan dan yaji zafin bugun, wani irin mari Baffan yadauke shi dashi kafinma ya farga.

"pa, pa, pau" yamai guda uku, dafe kucinshi Aabid yayi ranshi a mugun bace kanshi akasa, Baffa ya nunashi da sandarshi yace "kasheshi zakayi Hussain?

Nace kashe shi zakayi?

Koma meyamaka bazaka iya hakura ba sanin halin dayake cikiba, jibi irin dukan dakamai saikace ubanshi ne kai, bai girmeka ba?!" Baffa ya dakamai tsawa yace "Hassan yarigaka shan iskan duniya sanan saigaka kaima kafito, kai wani iri ne, bakada imanine Hussain?

Uban wa yataba dukanka haka aduniyan nan tunda aka haifeka?

Hassan dake bala'in sonka kama mahaukacin duka haka Hussain?" Baffa yay maganan yana nunamai Aadil dake kuka sosai jini nabin gefen pink lips dinshi bama ya iya kuka tsabagen kukan dayaci sai ajiyan zuciyan kuka yake ajikin Mami, Abie kuma yadauko first-aid box yana kokarin budewa dan sharemai jinin dakenbin lips dinshi, shatin jini-jinin da Mami tagani ta jikin white shirt din dake jikinshi yasa ta daga Aadil din daga jikinta da saura taja riganshi sama shatin belt dahar dan jini jini ke fita daga fatanshi, daga ita har Abie dagokai sukayi suka kalli Aabid din da kanshi ke kasa, hawaye Mami ta share ta kira sunanshi cikin wani irin raunanniyar murya.

"Aabid" dago kanshi Aabid yay ya kalli Mamin da jajayen idanunshi, hawaye ta kara sharewa tasake rungume Aadil din dake nishi da ajiyan zuciyan kuka ko motsin kirki baya iyawa idanunshi a kulle yay lamo a kirjinta yarike mata hannu gam yana nishi, ahankali tace "Aabid d...dan uwanka kama dukan mu...g..." kasa magana tayi sabida wani irin kuka dayazo mata sosai bakaramin tausayi Aadil din yabata ba jitayi da ita Aabid yama dukan nan dayafi mata sau dubu akan Aadil mara lafiya wanda baimasan zafin kanshi ba, yaron da kullun suna hanyar asibiti dashine yama wanan dukan rashin imanin, share mata hawayen daya kasa daina zuba Abie yayi tsabagen bakin ciki da kuncin datakeji, kana Abie shima kasan ranshi abace yake, janye hanunshi yayi daga fuskar Mami bayan yagama share mata hawayen yace "is okay, barshi" ya dago kai yama Aabid din wani irin mugun kallo yace "wuce katafi abunka" kasa daga kafa Aabid yayi yafita daga dakin ko motsi yakasa saima kanshi dayakai kasa, cikin wani irin ihu Mami taja belt dinshi dake gefenta ta wurgamai belt din yafada kanshi tace "ance ka wuce kafita daga dakin nan, kozaka hada damune kadaka eh zalim?" dan dago kai yayi ya kalli Mami zuciyarshi namai wani iri da sauri yajuya yafita daga dakin kaman zai tashi sama yay tsakar gida ya shiga mota yaja motar yabar gidan da shegen gudu.

Ahankali tafito daga bayan verse din tana kuka sosai ta tsaya abakin kofan so kawai take taga Aadil din da zuciyarta ke mugun kwadayin ganinshi.
Chapter 29 · 0% Book details