← Book details In Bani Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 36 OF 101

Sashe 36

In Bani Complete Hausa Novel · about 6 min read

Gyaran murya Baffa yayi zai fara magana, Mami takasa daurewa ahankali ta zamo daga kan kujera ta saukar da gwuiwanta kasa ta hade hannayenta biyu alamun roko tana kallon matar da kamanin ta da Hamida yasa tagane itace mahaifiyar Hamidan tace "dan Allah, dan Allah ba danniba, ku dauki Aadil a matsayin danku kunsan duk abinda zaisa yaron nan farin ciki ya taimaki rayuwan shi, kome yakeso zaku iyayimai koma menene abin dan samun lafiyan shi" da sauri ta share hawayen daya zubo mata, zatai magana saikuma wani irin kuka yazo mata tafashe da kuka sosai tsabagen yanda zuciyarta kemata wani irin rawa, da sauri Mama da Anty Lami sukace "subhanallahi, hajiya dan Allah kidena kuka" cikin wani irin kuka Mami ta girgiza musu kai ta kalli Abban Ra'is da Abba ta kalli Kaka data kafeta da ido sanan tasake kallon Mama har lokacin hannayenta ahade tace "dan girman Allah badanni ba bakuma dan halina ba, alfarma nake nema dudda nasan mai girma ne, mai kuma wuya babu wanda zai dauki yarshi yabama mai kwakwalwan yara, amma dudda haka da Allah nake hadaku Maman Hamida da baban Hamida, ku dubi girman Allah, ku taimakama d'ana kubama d'ana Aadil auren Hamida karya rasa ranshi dan darajan All...Allah" tafashe da kuka sosai kowa na dakin saida kukanta yataba ranshi har Kaka, da sauri Mama ta dagata tama kasa magana Baffa yace "ku shiga ciki mu maza zamuyi maganan mu anan" tashi Big Mum tayi da Anty Lami da Mama suka wuce da Mami dake wani irin kuka sosai ciki tana sambatu bama tasan metake cewaba.
[11/21/2019, 6:39 PM] Aishat Muhammad: _
IN BANI
Maman Abd Shakur
32...
_This n
Gyaran murya Baffa yayi yabude taron da addu'a bayan yagama Kaka ta shafa tana gyara zama, ya fuskanci Abba da Abba Ra'is, a natse yace "da farko dai sunan Alhaji Gambo Sawaba, ga yarana nan maza sai babban aminina Ya Imam, kaman yanda mahaifiyar jikana tace haka abin yake, amma bari nafara da baku takaitattcen labarin yaron, Sunanshi Hassan Abdullahi, yan biyu ne su, shekarun su talatin da daya a duniya, tunda aka haifi Hassan yataso da kwakwalwan yara, sai kwatsam daga dawowan su Nigeria Allah ya dauramai son yarku Hamida, Amatullahi bana wasaba, yanzu haka yana kwance a asibiti rai a hannun Allah, alluran bacci akemai dan sabida kawai yadena kiran sunanta dan sosai yake tarin jini, nasan cewa abinda nake tambaya abune mai girman gaske dan babu wanda zaidau yarshi lafiyayya yabama mara lafiyan kwakwalwa auren yarshi, amma inaso ku dauki Hassan amatsayin danku nasan cewa zakuyi komenen ku nemamai lafiya, banda haka aure rahama ne saikuga ta sanadin auren ta ya warke yadawo kaman bashi yay ciwon ba, ku taimaka mana badan muba bakuma dan halinmu ba kubamu auren Hamida" yakarashe maganan ahankali akuma sanyaye cikin wani irin mugun sanyin gwuiwa ya fawwalama Allah komi dan yasan abu mai wuyane su yarda, gyara zama Abba yayi yadanyi gyaran murya ya kalli Baffan dayaji yana wani irin jin mugun nauyinshi zaiyi magana Kaka ta dagamai hannu.

"kamin shiru anan Sama'ila" sanan ta juyo ta fuskanci Baffa tana kallonshi tana warware kullin zanin jikinta tana ciro namijin goro, ta balli goron takai bakinta tana taunawa sanan tace "magana zan maka ta gaskiya" wani irin sanyi Abie yaji a aranshi yazaro ido yana kallon Kaka, dafa kirjinta tayi ta bubbuga harsau biyu tace "kaganni nan bazan taba daukan jikana nabama mahaukaci ba ana zaune lapiya?

Hamidan tawa ce zan dauka nabama tababbe haba adinga adalci Alhaji to tama yaya abin zai yuwu..." da sauri Abba yaja gefen zaninta ganin rashin mutunci datake shuka musu wanda bai daceba da girman su da kuma darajan su, nakama hanunshi duka tayi batare data kalleshi ba tace "barni nafadi musu gaskiya Sama'ila kadena hanani" tasake kallon Baffa tace "ku masu kudin nan kunada son kanku dayawa na rantse da girman Allah, yanzu fa da ace mune mukeda tababben yaro mukazo neman auren lafiyayyar yarku, da wlh, billahillazi, da bazaku badaba koda dan namu mutuwa kuwa zaiyi, amma dayake mune zakuzo nema, to bari ma na tambaye ka idan muka dauki Hamida muka bama mara lafiyan dan naku wani irin zama zasuyi iye?

Shikenan saidai ta dinga ganin sa'ointa da yara ita banda ita haba mana anya baku so kanku da yawaba kuwa Alhaji, gaskiya ku tattara yinaku yinaku kubar mana gidan mu bazamu baku yarmu ba, bazan bada jikata ga mara lafiya na, shidai mara lafiyan ubangiji Allah ya bashi lapiya yakuma tada kafadar shi, sai anjiman ku" tunda Abba yake Kaka bata taba bashi kunya irin nayau ba hatta Abban Ra'is sunnar dakanshi yay kasa dan Kaka tagama dasu bahaka ake magana ba ko kadan, murmushi sosai Baffa yayi irinta manya dan ko kadan baiji zafin maganganun Kaka ba dan gaskiya tafada, dama yasan saman ma Aadil aure abune mai wuyan gaske, gaskiya babu mahaifin dazaiso yadau yarshi yabama mara lafiya bakowa ne zai iyaba, murmushi yasakeyi yace "shikenan angode sosai mun gode da lokacin dakuka bamu" yataso zaizo ta wajen su Abba da kansu ke kasa yabasu hannu da sauri Abba da Abban Ra'is suka tashi suka mika musu hannu, Abba yama kasa magana sabida yanda Kaka ke binsu da kallo yasan gwara yay shiru inba hakaba bakaramin aikin Kaka ba tasake yanko wata maganan yanzun nan ba, ahankali Baffa yana rike da hanunshi yana kallonshi ganin yanda duk kunya tarufe shi yaki yarda su hada ido yace "bakomi karka damu, arziki ta hadamu kuma in sha Allahu amfara kenan" murmushi Abba yayi yana kara kai kanshi kasa, Baffa yace "to Amana sallama da matan, su samemu awaje mun barku lafiya" to Abba yace Baban Ra'is yarakasu shikuma Abba yay corridor ya kwalama Zainab kira tafito yace "jeki fadama su mamanki su fito zasu tafi" da sauri ta juya bayan ta amsa da to ta tafi shikuma yawuce yafita batare daya kalli Kaka daketa rakashi da ido ba, fitowa su Mami sukayi suka gaishe ta Kaka tace "Allahu akbar, kidena kuka haka baiwar Allah addu'a zakimai Allah yana amsan addu'an bakin uwa, wuce kutafi suna jiranku awaje" waje duk suka fita bayan sunyi sallama suka shiga mota suka tafi Abba da Abban Ra'is kuma suka dawo cikin gidan.

Zama duk sukai a palon Abba ya kalli Kaka yace "gaskiya Umma abinda kikayi bai daceba, kince bazaki basu ba bai isaba saikinci musu fuska, babu kyau fa aibasu suka dauramai ciwon ba ko naga, haba mana Umma" kallonshi Kaka tayi saikuma tafashe da kuka sosai tasa bakin zaninta tana share ido tace "nika zaga Sama'ila, nikake ciwa mutunci akan nafadi gaskiya?" sakin baki Abba yayi yana kallonta cikin mugun takaici, Anty Lami dai murmushi tayi Mama kuma girgixa kai kawai tayi kanta akasa, da sauri Abban Ra'is yace "a'a Kaka ba zaginki yayi ba tayaya ma zai zageki eh Kaka, cewa yayi dakince musu kawai bazaki basu ba basai kin ci musu fuska ba anan ne baki kyauta ba" rushewa tayi dawani irin masifaffen kuka tace "nikuka tasa agaba harku biyu kunmin taron dangi kuna cimini mutunci, d'ana wanda na haifa ya zageni kaikuma kana gayamin baka akan nafadi gaskiya" da sauri Baban Ra'is zaiyi magana Abba ya girgiza mai kai alamun karyayi yabarta kawai, fashewa tayi da kuka sosai tace "sabida banso Hamida ta cutu nafadi gaskiya shine kukamin taron dangi?

Yo inda sune mukaje nemama tababben mahaukaci danmu yarsu bamu zasuyi?
Chapter 36 · 0% Book details