← Book details In Bani Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 45 OF 101

Sashe 45

In Bani Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Aadil, Son" ahankali ya turo baki yace "uhm" murmushi tayi sosai dan Aadil ya iya shagwaban banza, kara saukar da murya tayi dan saiya iya cewa shiba yanzu zai tashiba.

"tashi my son time for subhi prayer, tashi kabi Baffa kuje masallaci kaga yanzu you are a married man, Hamida is your wife you need to be praying a jam'i" da sauri yabude ido jin Mami takira sunan Hamida, tashi yayi zaune yana mitsittsika ido agajiye yace "where's my Hamida Mami?" folding hannu Mami tayi akirji tana kallonshi batare data amsashiba, da sauri yakara bude idonshi yana turo mata bakin shagwaba yace "good morning Mami na, where's my Hamida" murmushi tayi tace "zaka ganta anjima, go brush ka dauro alwala kazo kai salla in the night zaka tafi chan part dinku" make mata kafada yayi yace "i want to shower first my body is itching" da sauri tace "to sarkin wanka, tashi to kaje kayi" tashi yayi ahankali cikin layin bacci yay hanyar bayin Mami tabishi da kallo, ya bude kofan ya shiga bathroom din yarufo sanan tai wajen wardrobe dinshi taciromai white jallabiya ta ijiyemai kan gado itakuma tahau kan dadduka tafara salla, yadan dade kafin yafito sanye da bathrobe blue hanunshi da dan karamin towel fari yana goge fuskarshi sai kamshi yakeyi, tsayawa yayi yana kallon kan gadon wurin Aabid sosai yake wani irin kewanshi, idar da sallan Mami tayi tace "get dress kazo katafi mosque bari naje naduba babanku" tabude kofa tafita ahankali yadau man yashafa sanan yacire bathrobe din ya shirya tsaf cikin jallabiyan dayamai kyau sosai ya cikashi dam yasa takalmin shi sai wani irin hadadden kamshi yake, zama yasake yi akan gadon yana kallon bangaren Aabid, ahankali yadau wayarshi daya gani kan side drawer yadanna yana turo baki yay dailing number Aabid din dayake fushi dashi sosai dan hakanan yaji yana missing dinshi ringing daya Aabid dake kwance akan gado Vanessa a gefenshi tana bacci, yana rike da wayarshi yana kallo yana tunanin dan uwan nashi wayar tai ringing yaga sunan Aadil.

Picking call din yayi yakai wuyan kunenshi kirjinshi namai wani irin ciwo murya chan kasa yace "hello" jin muryanshi yasa Aadil yakasa daurewa yasakin mai kuka ahankali yana goge ido batare dayace komiba, da sauri Aabid yature hanun Vanessa dake jikinshi yatashi ya zauna shikan shi baisan irin son dayake ma Aadil ba saisa yakasa yafema kanshi akan mugun dukan dayamai saisa kuma yabar gidan dan inhar akai auren agabanshi baisan mezai aikata ba, lumshe ido yayi yanajin kukan har ranshi yace "rascal" yakira sunan asanyaye kaman bashiba, makemai kafada Aadil yayi yana kuka batare dayace komiba, ahankali Aabid yace "I've tried many times nacema sorry but kanata fushi dani inka ganni guduna kakeyi, kakimin magana, ka tsaneni, kanata zuciya dani why are you calling me now kanamin kuka kana tadamin da hankali so kake ciwon zuciya yakamani namutu?" yay maganan yana dafa kirjinshi dakemai zafi sosai, da sauri Aadil ya girgiza kai cikin kuka yace "sorry" lumshe ido Aabid yayi kaman zaiyi kuka yace "am sorry too twin Bro, I've hurt you, am such a bad brother, am sorry Aadil, am so so so soo sorry" yay maganan while his tone was breaking kaman zaiyi kuka, da sauri Aadil ya share idonshi yace "are you crying?" girgiza mai kai yayo ya share hawayen daya zubomai da sauri yace "a'a" duk sukai shiru Aadil yanajin wani iri kaman something is wrong with Aabid, ahankali yace "are you fine?" gyadamai kai yayi ya gyara muryanshi trying to sound fine and normal yace "yes, where is your wife?" kaman zaiyi kuka yace "i don't know" gyadakai Aabid yayi yanajin wani iri sosai, ahankali Aadil yace "i miss you, you are not a bad brother, you are very good and I love you so much Bid, yaushe zaka dawo?" murmushi yayi hawaye ya gangaro mai daga ido, murya chan kasa yace "soon, don't worry i will buy something for you kaji, promise one thing" da sauri yay murmushi yace "what?" murya chan kasa ya runtse ido yace "take care of yourself and Hamida sosai, don't make her cry okay" washe baki yayi yay fari da ido yace "okay, i promise i will take care of Hamida my wife" murmushi yayi mai ciwo yace "je dakin Baffa kutafi masallaci is time for salat nima zantafi ne" da sauri yace "ok bye" bye yace yakatse wayan yatashi da sauri ya shiga bayi yana goge hawaye ya sakin ma kanshi shower.

Tashi Aadil yayi yana murmushi sosai yanajin dadin maganan dayayi da Aabid yafito daga dakin daidai Mami da Baffa sun fito Baffa yakama hanunshi suka tafi masallaci.

Already Big Mum nawajen masu girkin da aka dauko tana gayamusu mezasuyi Mami kuma ta wuce dakinta da sallama ta shiga dakin ganin babu Abie akan gado yasa tai shiru tai tunanin hala yana masallaci ne hakan yasa ta shimfida dadduma tai salla.

Shigowa Anty Lami tayi ta tadata da kyar ta iya ta bude idanunta dasuka kumbura dan bacci bai dade da kwasheta ba ahankali ta tashi ta zauna tana sosa ido Anty Lami tace "yi sauri jeki dauro alwala kizo" bayi ta shiga ahankali bata wani jimaba ta fito daure da alwala komi atsanake takeyi dan ko kadan batada karfi tadau hijabin tahau kan dadduma tafara salla itakuma Anty Lami ta shiga bayin tahada mata ruwan wanka da turarukan da ake samata mai zafi sanan tafito taje gaban wardrobe dan ciro mata kayan dazata saka wani hadadden lace pitch tadauko an mata dinki riga da skirt ta ijiye sanan taciro undies din dazatai amfani dasu dukta ijiye ta juyo ta kalleta jinta sallame tace "yauwa inkin gama azkar din kiwuce bayi kiyo wanka ga kayan dazaki saka inkin saka sai zainab tazo tamiki kwalliyan" gyadamata kai tayi ahankali hawaye na taruwa a idanunta Anty Lami tawuce tafita, tana gama azkar din ta linke dadduman ahankali tana kara kallon dakin yanda dakin keda kyau sosai ta share kwallan daya zubomata da sauri tawude ta shiga bayin ahankali, tajima dan taji dadin ruwan zafin sosai kafin tafito daure da towel duk jinta take wani iri she's not just happy, zama tayi ta shafa mai, sanan ta shirya cikin kayan tsaf dasuka mata kyau bana wasaba, sun kamata sun mata chass ajiki, shigowa dakin Ayush dasu Zainab sukayi suna ihu, Ayush tace "wo amaryan Aadil, amaryan malam Hassan, wanan glow haka aisai kisa angonki ya suma, zee yimata makeup" da sauri Zainab tace "to bari nadauko makeup bag din" Ihsan tazo da sauri tarike mata hannu tana murmushi tana kallonta tace "kinyi kyau sosai Anty Hamida" dan murmushi tamata hawaye na shirin zubowa Anty Ayush ta harareta.

"wai kukan bai isabane" daidainan Zainab ta shigo dawata katuwar jaka tazo tafara tsara mata makeup, subhannallah tsarkiya tabbata ga ubangijin daya tsara wanan hallitan! bakaramin kyau Hamida tayiba kaman ka saceta kagudu, sai hotuna suke daukan ta ganin abin nasu bamai karewa bane suna neman su kara sata kuka yasa Anty Lami ta kadasu duk kowa yaje yay wanka dan yau zasu bar gidan nan sukai wanka aka cici gayu kafin Mami ta turo ma'akatan part dinta aka fara jera musu abinci kala kala sanan sukabar shashin da kyar suka tasata agaba tadansha tea da chips aka ccici abinci sanan suka sake gyara gidan ko ina na kamshin turaren yan maiduguri, haka suka wunin mata ranan har yamma jama'a sai shigowa suke suna dubata duk wanda yaga Hamidan saiyay mamakin kyawun matar Aadil din, yan gulma nayi suna cewa hala iyayenta kudi sukagani saisa suka yarda suka bama mahaukaci inba hakaba ina mahaukaci ina wanan shuwa arab din.

Bayan isha'i suka shirya tsaf zasu tafi bayan sunsa tasake wankan ruwan turare ansake mata hadadden gayu, kuka, kuka Hamida bana wasaba takeyi kaman ana yankata dan harda bubbuga kafa akasa hankalinta yawani irin tashi dansai yanzu ta yarda yes anmata auren dan gashi yan uwanta zasu tafi su barta bada ita zasuba, janta dakinta Anty Lami tayi tama yan uwanta da duk sukai wani iri sabida tausayin Hamidan alamu dasu tafi waje su shiga mota sanan ta zauna kusa da Hamidan dake kuka sosai takama hanunta tarike ahankali takira sunanta.

"Amatullah" dago jajayen idanunta tayi ta kalli Anty Lami, ahankali Anty Lami tace "kindai tuna fadan da mahaifinki da mahaifiyar ki suka miki ko, still shi zan kara tunatar dake, karkice dankinga matsalan mijinki yasa kikimishi biyayya kokin bin umurninshi, a'a, koyaya yake aljannar ki na karkashin kafarshi, kome yakeso kimishi, komeye bayaso karkimai, ki rufama mijinki asiri sanan ki rike sirrin shi, matsalar mijinki matsalar kice, farin cikinshi farin cikin kine, kikuma dage damishi addu'a nasan koba yanzu ba, koba yauba watarana zai bude ido yay alfahari dake dan kin kasance mace data soshi takuma zauna dashi da lallurarshi, kidau auren ki amatsayin jahadin ki, ki rike Allah nasanki da karatun Alqurani da yawan azkar karki sakesu ki kara rikesu da kyau kinji, kina tare da yan uwan mijinki ne kidinga musu biyayya tsakanin ki da kowa should be mutunci, respect and peace kinji Hamida na" gyadamata kai tayi ahankali tawani irin fadawa jikinta tasaki kuka sosai mai tsumma rai bubbuga bayanta Anty Lami tayi tana murmushi danji tayi kaman zatai kuka itama kafin ahankali ta janyeta daga jikinta tana kallon yana take kuka take haki tace "ina zuwa bari naduba wani abu a kitchen dinki nai plugging abu" da sauri tafita daga dakin tai waje duksu Mami na tsakar gida suka sallama na mutunci sanan ta shiga mota bayan sun hada musu shatara na arziki suka tafi.
Chapter 45 · 0% Book details