← Book details In Bani Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 101

Sashe 19

In Bani Complete Hausa Novel · about 8 min read

Narabaka dasu kakiji, tun baban ka nada rai wanan mayyar wicked Kakan taka tasa aka sakeni dan haka nafa and am going to say it again, jinina bazai kara hada wani abu da wanan family ba, tun wuri kacire yarinyar nan aranka inba hakaba wlh fushin dazanyi dakai wanan karan saiyafi na wanda nai dakai ranan dakaje Lagos ka daukota stubborn boy, and come back home rightaway Dr na jiranka" tai tsaki ta katse wayan, ahankali ya zare wayan daga kunenshi kirjinshi namai wani irin zafi, he don't know where all this hate is coming from but one thing is for sure yasan idan har abinda Ammi ke fada gaskiya ne, Kaka tasa aka saketa dan Kaka batai laifi ba dan ko kadan Ammi batada kirki yana ganin yanda takema yan aiki wani zubin ma shiyake hanata, yasan mahaifiyarshi sosaisosai.

Yakai kusan 5min a wurin yana tunane tunane sanan yaja mota yabar wajen yadau hanyar gidansu.

Faruk yaron kanin mahaifin su Hamida ne, shika dai suka Haifa shikadai ne kuma jikan Kaka namiji, inda Baban su Hamida yahaifi yara bakwai dukansu mata, baban Faruk ya rasu a plane crash ne, his Mum is from a rich wealthy family, bayan rasuwan baban Faruk Faruk yadawo hanun Abba da Kaka, rashin mutunci Ammi tazo tai dasu Kaka akan abata danta, in other to maintain peace yasa Abba yacema Faruk yakoma wurinta but dudda haka kullum yana gidansu, weekend yana yawan zuwa gidan kajin Abba yana tayashi aiki dan sana'ar baban su Hamida kenan saida kaji da Kwai and he's making it Alhamdulillah Allah ya sanya mai albarka a sana'ar.

Dan lekowa tayi daga inda ta labe ganin yatafi babu yasa tafito ahankali tana tafiya da sauri da sauri wani kantin taje dayake safiya ne ba mutane sosai, take away abinci merai da lafiya tayi guda biyu tabiya kudi ta karba tafito tafita daga school din gabanta na faduwa sosai, kasa samin Keke tayi hakan yasa tafara tafiya akasa tana kakkare fuskarta, saida tai nisa sosai tamugun gaji da tafiya takai junction din wani layi keke napep ta tare ta shiga tace "old railway" "hajiya dari uku" ahankali kanta akasa tace "muje" tada keke napep yayi suka shiga hanya, sukayi tafiyan kusan 15 minute yakaisu wurin, ahankali ta sauko taciro dari uku tabashi batare data kalli fuskarshi shi tajuya ta shiga wajen tana kallon kan kujeran da Baba yake zama yanajin yar radio shi ganin bashi yasa ta karasa wajen, takeaways din ta ijiyemai ta ta wuce ciki hango wasu samari tayi kusan biyar ko shida zaune a inda ta saba zama suna kokarin kunna wiwi da sauri ta juya kafinma su lura da ita, cin karo tai dawani abayanta idanunshi jajir da alamun yasha yai tatil yace "ke waya kiraki nan?" kwalama sauran dabama su lura da ita kira yayi yace "babaa jimana, tawaye ne tazo?

Ba munce babu wacce zai kira tashi nanba yau" da sauri amugun rude tai gefenshi zata wuce yatareta yace "ki tsaya mana baby nakira miki su, hala wajen Sani kikazo dan nasan mayen da shegen iya zabo zafafan mata" arude tana dan waigen bayanta jin sahun mutane suna zuwa ta kwalama tsohon dake gadin wajen kira.

"Baba, Baba" daidai lokacin sauran sun iso wajen fashewa sukai da dariya dayan yace "Baba wai me gadi kike kira?

Ke yarshi ce?" daya daga cikin su yace "kaima jibeka dawata magana ina Baba mai gadi yakeda kyan haifan irin wanan lu'u lu'un?" daya daga cikinsu yace "kodai me zuwa bashi kayane?" kulle bakinsu sukayi suna zaro ido irin na isgilanci atare sukace "tsoho yaji chakwai" fashewa tai da kuka ta duka a tsakiyan su tana kwalama Baba kira.

"Babaa" daya daga cikinsu yace "ankai Baba kauyen su Baba ba lafiya muma fanshi Baba yau, kingan mu mushida kici har ki koshi ko yan mata" yay maganan zai kama mata hannu boye hanunta tayi ajikinta tafashe da kuka, hijabinta ya fizgo ya mikar da ita tsaye fasa wani irin ihu tayi a mugun tsorace ta bugamai kafarta hakan yasa yay baya yasaketa yana tsaki dan yaji zafi da sauri sauran sukayo kanta tawani irin kwasa da gudu tana kuka wanda ta hambaran yawani irin tadiyota tafadi akasa hancinta ya shiga cikin dan kasan yashin dake wurin.
[11/5/2019, 10:07 PM] Aishat Muhammad: _
IN BANI
Maman Abd Shakur
16....
_This novel is for sale, karki karanta in baki biyaba_
_in kinason novel dinan zaki turo 300 access fee to 3107021073 first bank aisha Muhammad saiki turo evidence of payment ta watsapp number na 07012181461_
_you can also send MTN card 300 ta watsapp number na 07012181461_
Kafafunta yajawo tafasa ihu sosai tana kuka ta dibi kasan wajen da hannuwanta biyu ta juyo da kanta cikin kuka, watsa musu kasan tayi a idanu hakan yasa ya saketa da sauri yay ihu shida sauran suna sosa ido suna kokarin budewa sun kasa, dawani irin sauri ta tashi tadau jakanta taruga aguje suka biyota, fitowa tayi tana gudu sosai tana kuka, black hijabin ta gabaki daya ya baci da kasa tana gudu suna binta....

Anatse Mami ke tuki taci gayu sosai tasa wani hadadden exclusive atampa brown da yellow dayay mata kyau tayafa wani babban mayafi brown tana tuki, gefenta kuma Aadil ne yana zaune agaba yana wasa da fingers dinshi yana counting dinsu one, two, three, yana sanye cikin wani Fendi white t-shirt daya kama jikinshi sosai, hanun rigan are dark brown, yana sanye da dogon brown pant yasanya white sneaker na Fendi, wrist dinshi daure da agogo na rolex gashin kanshi a kwance yana kara bubbude manyan idanunshi yana magana kasa kasa yana counting yatsunshi sai wani hadadden kamshi dake tashi ajikinshi, murmushi Mami tayi tadan kalleshi ta maida hankalinta kan tukin datake yi tana tunani Aadil kenan, Ball fa suke bugawa a compound shida Aabid Baffa kuma na zaune acikin bukkan dake compound din yana kallonsu yana murmushi, yana ganin Mami tafito rike da car key gidan BigMum zata yafashe da kuka ya yarda kallon zai bita shine ta taho dashi.

Ahankali takira sunanshi.

"Son" dan juyowa yayi ya kalleta da manya manyan idanunshi yadan daga cikakken gyararren giranshi sama kaman na tamace yana kallonta, itama dan kallonshi tayi ta maida hankalinta kan tuki tace "wat are you counting Son" turo mata baki yayi kafin ya maida kanshi kan hanya yana lankwasa kan yana cizan wet lips dinshi batare dayace mata komiba yafara counting motocin gabansu.

Dawani irin mugun gudu Hamida tafado kan titin tana waigen baya saura kiris Mami ta bigeta ta gitta, dan batakai ga taka birki ba ta buga salati.

"subhannallahi wanan lafiyanta kuwa" wani irin ganin gittawan ta yayi kaman flash of light, dasauri yakara ware ido yabi bayanta da kallo harta karasa tsallake titin da gudu tana waigen baya tana kuka tana share fuskarta da hijabi dan gani tayi kaman suna binta, da sauri cikin wani irin rudewa kirjinshi nawani irin bugawa kaman zai tsage yasaki lips dinshi daya rike da hakori tun dazu dayake wasa yana waigenta ta baya dan sunriga sun mata dan nisa, arude yay pointing saitin Hamida yana kyafkyfata ido kaman mai stammering yace "s...s...she Mami" wani irin juyawa yayi batare daya damu tafiya suke akan titi ba ya tuge sitbelt din jikinshi yawani irin bude kofan motan iska yaja kofan, kofan ya bude gaba daya ya daki wani mai machine dake tafiya, salati Mami tayi arude dan bama ta lura dazai bude motar ba saida taji wani irin iska, kafin kyaftawan ido yafita daga motan kanshi na rawa sosai yawani irin fadi akasa sosai dan da wuya in baiji ciwo ba, ihu Mami tayi tawani irin taka brake din motarta duka tana kallonshi kar wani abin hawa ko babban mota yatakeshi before you know it motar dake bayan Mami dat was on speed tazo da gudu ta bugi boot din motan Mami danta taka burki ne unexpectedly ta tsaya, motar Mami tai gaba kan Mami dayake ta lekone tana kallon Aadil arude kanta yawani irin bugu da starring, cikin ikon Allah mota bata bugeshi ba, da sauri batare daya lura da Mami bama yatashi yana waige waige kanshi na rawa sosai yana yarfe hannu danya bugu sosai akafa baima damu da mutanen dake salati ba ana kallonshi ana kallon mai machine dayay hatsari da two cars ya shiga gudu yana hango Hamida datamai nisa sosai yana yarfa hannu yafashe da kuka yace "she noo, don't go" yacigaba da gudu, gajiya yayi sosai kaman zai suma yafashe da kuka yana kallon titin dan baitaba gudu hakaba a rayuwan shiba, wani mai machine ne dayazo wucewa ya tsaya yana kallonshi cikeda mamaki yace "malam amma mutuwa ne kake kuka haka miyau na zuba" cikin kuka sosai yamai pointing Hamida dake shirin yin kwana tai nisa sosai yace "she" kallon inda yake nunamai yayi sanan ya kalleshi ganin yanda yake kaman mara lafiya sanan wanda yake nunamai itama gudu take yasa yakawo aranshi halama mai gudun shi take nema itama, tausayi yabashi hakan yasa yace "hauna kaikah wurinta to" tsayawa yayi yana kallon machine din yana kuka hannu mai machine din yamika mai da sauri yarike shi ya dafa shi sanan ya iya hawa kan machine din, mai machine din ya kunna yaja machine din, rikeshi yayi a tsorace yana kuka, adaidai bakin layin lokacin harta shiga layin mai machine din ya tsaya yace "sauko ka bita bazan shiga layin nanba, machine dinan daga wajen wanki na karbota yanzu haka, layin nan duk chabalbali" lekoshi yayi da kai yana kallon fuskanshi dan baicika gane manyan hausaba, ahankali mai machine din yace "come down" saukowa yayi yana kallonta yana kuka da karfi ya kwala mata kira.

"sheeee" arude Hamida dake gudu har lokacin tana kuka sosai tafada wani uncompleted building ta tsugunna tana kuka sosai tana addu'a Allah yasa basu ganta ba, tabude jakanta arude ta shiga neman wayanta tanaso takira Ya Faruk amma bataga wayanba hala tafadi awurin, tafashe da wani sabon kuka tana kare fuskarta ta hijabi ta.
Chapter 19 · 0% Book details