← Book details In Bani Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 37 OF 101

Sashe 37

In Bani Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ba gaskiya nafada ba amma shine kuka mini rashin mutunci haka, innalillahi wa innailaihi raji'un, Sama'ila ni ka nuna ma iyakata, to wlh wlh yau zan mugun baku mamaki" mikewa tayi tsaye tai hanyar fita daga dakin da sauri Abba yatashi yabita yace "ina zaki Umma" juyowa tayi cikin fushi sosai tana zare ido ta nunashi da hannu tace "ba ruwanka, tunda haushina kakeji akan gujema Hamida tsiya danayi ai shikenan badai kai kaga masu kudi ba kana kwadayi ko yakara budema wasu manya manyan gidajen kaji ba, zan baka mamaki, kuma wlh ka biyoni Allah ya isa" tai hanyar gate da sauri, su Mama da Abban Ra'is suka fito, Abban Ra'is ya kalli Abba yace "ina zata?" ahankali Abba kamam zaiyi kuka yace "bansaniba wlh tace inna bita Allah ya isa" duk suka tsaya suna kallonta yanda take tafiya da sauri da sauri kaman ana ingizata tana kuka sosai, daidai zata bude gate Faruk dake sanye cikin uniform na sojoji ya bude gate din ya shigo, fashewa tayi da kuka sosai tana ganinshi tace "Faruk kaga ni ubanku Sama'ila yacima mutunci ai bainar jama'a ko, zoka kaini gidan Alhaji Gambo Sawaba ai kowa na kano ya sanshi" kafin ma yay wani magana ta fizge hanunshi cikin kuka tafita sukai inda yake parking mota akofar gidan tace "budemin" budemata motar yayi ahankali ganin yanda take kuka kaman wacce aka Zane ta shiga baya tace "ni tsoron gaba nake yan gaba ke mutuwa a hatsari bana bayaba wlh" murmushi yayi yatada motar yaja yace "ina zankai ki haka bako mayafi" hararan shi tayi tana share hawaye tace "uwarka bata siyamin mayafin ba saisa ban yafaba, kuma dan ubanka Sama'ila ai nacema gidan Alhaji Gambo Sawaba zaka kaini ko" yatsine fuska yayi tareda tabe baki yace "mekuma yahada ki da gidan babufa wanda kika sani awanan family tsohuwa" shewa tayi tace "da kenan kasani yaro, kajani da sauri nidai" tabe baki yayi bai kara cemata komiba ganin yau haukan nata takejin yima mutane haka har new GRA agaban gidan securities suka tsaida su, tabe baki yayi ya waigo ya kalleta yanda take zazzare ido tana kallon durmemen gate din gidan yace "aisai kimusu bayanin wanda kike nema" da sauri tana zare ido tace "har munkai gidanne kai wanan gida ai yay na ubanku sau hamsin, kaito saukar min da glass din kasa namusu magana" saukar da glass din Faruk yayi Kaka ta leko kai ta kalli security dayake jira suyi ya saukar mata yaga su waye tace "kai wajen mai gidan Alhaji gambon nazo, yasan da zuwana yana ina?" ganin yanda take maganan da confidence yasa security ya yarda yace "suna asibiti wajen jikanshi mara lafiya" da sauri Kaka tace "wani asibiti ne?" "prestige private hospital" "kaini asibitin Faruku" dogon tsaki Faruk yaja dakuwa tamai tace "uwarka kama tsaki bani ba ja'iri kawai" hararanta yayi ta madubin gaban mota yace "nifa ki kawo kudin mai nasa ato bazaki kararmin da mai a gantali ba" hannu ta tusa a cikin lalitan ta tace "nagode ma Allah dai niba matsiyaciya bace daka kwance min zani a titi" dubu daya ta zaro ta wurgamai tace "gashinan kasa" murmushi yayi ya dauki kudin yarike dukdan ya kular da ita sanan ya kunna motar yaja har zuwa asibitin parking yayi yace "nidai wlh bazan biki ciki ba rana yay yawa" bude motar tayi tafita tace "kuma wlh katafi ka barni Allah ya isa" tai cikin asibitin tana Kalle kalle, ta tsaya agaban wata nurse dake rubutu tace "ke inane aka kwantar da jikan Alhaji Gambo Sawaba" sama ta nunama Kakan batare data kalleta ba tana rubuta, tabe baki Kaka tayi ta wuce tace "mummuna sai masifar kafidiri Faruku ya kawomin ke yace kezai aura ai wlh saina fatattake shi, wayyo Allah kafafuwana wanan bene da shegen tudu yake" ta rike gwuiwa tana hawa matattakalan benen da kyar harta gama hawa, hango Baffa datayi yana dogara sanda sun shiga wani daki tareda likita yasa itama tai dakin da saurin ta, tura kofar dakin tayi daidai lokacin Aabid na kokarin cirema Aadil din oxygen daga hancinshi sabida wani irin tari dayake yi jini na fita yadagashi ya zaunar dan ance sudena barinshi yana tarin a kwance shikuma Dr yana kokarin hada wani allura da sauri da sauri Mami ta zauna akan wani kujera ta rufe fuskarta da handkerchief tana wani irin mugun kuka Abie na patting bayanta, shikuma Baffa na tsaye tareda Dr da Suleman big Mum da Muhammad sunje gida kawo abinci.

Tarin dataga yanayi ita karan kanta Kaka saida taji tsoro ahankali amugun galabaice ko ido baya iya budewa yace "Hamida my wife Mami, Hamida" batasan lokacin da hawaye ya zubo mata ba ta share da sauri, alamu Dr yama Aabid daya gyarashi yazo yamai allura nan aka samu bacci ya daukeshi.

"Allahu akbar kabiran wanan yaro nashan wahala" da sauri kowa na dakin ya dago kai ya kalleta harda Mami da rinanun idanunta, cike da mamaki Baffa yace "hajiya?

Ya akayi kikasan nan?" karasowa cikin dakin tayi tana kallon Aadil dake bacci awahale akan gado ta kalli Aabid tace "sannu kaji kaima dukkai zuru zuru dan uwanka ba lafiya kaine Hassan ko Hussaini?" ahankali yace "Hussain" kujera Suleman ya miko mata zama tayi tana kallon Aadil din tace "wlh daga gidan ka nake nida jikanane ma yana mota awaje yana jirana, magana nazo muyi, alkhairi yakawo ni wanan karan ba shairi ba, share hawayen ki maman yan biyu" tai maganan tana kallon Mami dawasu sababbin hawaye suka zubo mata, dan murmushi Mami tayi ta share hawayen Kaka tai murmushi ta kalli likitan tace "abamu waje likita" murmushi likitan yayi yace "sorry" yajuya yafita saida yarufe kofan sanan Kaka tajuyo ta kalli Baffa tace "bayan kun tafi naji abinda nayi ban kyauta muku ba koba komi ai kaga d'a nakowa ne ko?" Baba Suleman da Abie da gabanshi ke mugun faduwa sabida fargaban abinda tazo dashi sukace "hakane" Kaka tace "kuma ai kaga Allah shike daurama bawan shi ciwo, da Allah yatashi dauramai ciwo ai bai nemi shawaran kuba kuma lokaci daya yakan iya warkan dashi, banda ma haka bamusan alkhairin dake tattare da auren su ba, dan haka ne yasa nai tattaki nabiyoku dakaina nazo na shaida muku kuzo gobe in sha Allahu sai asaka musu rana kuma nida kaina a goben nan zan shiryo jikata Hamida nataho da ita yaganta koya sami lafiya, kidena Kuka kinji nabaku auren Hamida" wani irin faduwa gaban Aabid da Abie sukayi atare, wani irin jiri ne yadibi Aabid da sauri ya dafa bango yana kara kallon Kaka, Mami kuma cikin wani irin murna da tsananin farin ciki ta zamo daga kan kujera tai sujjada tana godema Allah, Baffa da Baba Suleman kuma kaman anmusu kyautan makka, Kaka ma ta washe baki ganin yanda suke farin ciki, Tashi Mami tayi daga sujjadan tazo gaban Kaka da kneels dinta akasa tarike mata hannu zatai mata godiya kuma sai kuka ta daura kanta akan cinyar Kaka, dariya sosai Kaka tayi hawaye na cika idonta dan sosai ayanzu taji tanajin tausayin su tace "ya isa ya isa, ai yanzu Allah zamu gode mawa ba wani abu ba, babu zancen kuka kuma sai fatan samun lafiyan shi taso kiga" ta dagota tana share mata hawaye, murmushi Mami tayi tace "nagode Umma, nagode Umma, Allah ya kara lafiya ya kara arziki" baba Suleman ma da Baffa sukace "mun gode" tashi Kaka tayi tace "kunga jikana Faruku dan banza ne saiya iya tafiya ya barni sai anjiman ku Allah kara sauki" dariya akayi, ta tashi tana gyara zani tace "gobe in zakuzo karku manta da kudin kagani ina so, kudin gaisuwar uwa da uba, kudin saka rana da kayan sa rana" dariya Baffa yayi yace "shikenan hajiya angama" suka dunguma zasu rakata tace "dukku koma ku zauna gaku da mara lafiya, Allah kara sauki sai anjiman ku" tawuce tafita ta sauka kasa sai uban murmushi take kaman ba itace tagama Kuka dazuva ta fita daga asibitin tai wajen motan Faruk ta tarar dashi yacika kaman zai fashe daure fuska tayi ta shige motan ta share shi, kwafa yayi ya kunna motar yaja dawani irin shegen gudu dukdan tai magana aiko ta fashemai da kuka tace "ka tsaneni ko, dan Allah kawa Allah karka kasheni kagadai yanzu inada biki agabana, gobe dazaran ankawo kudaden dana lissafa musu nizan karba na likama Halimatu dubu biyu sauran yar sudan zan dauko afara gyaran amarya".

Rage gudun motar yayi yajuyo ya kalleta yace "wace amarya?" .
[11/23/2019, 2:45 PM] Aishat Muhammad: _
IN BANI
Maman Abd Shakur
34 - 35
_This novel is for sale, karki karanta in baki biyaba, in kika karanta ina binki bashi pay anan or pay achan_
_in kinason novel dinan zaki turo 300 acess fee to 3107021073 first bank aisha Muhammad saiki turo evidence of payment ta watsapp number na 07012181461 sainai adding dinki a group din danake posting_
_you can also send MTN card ta watsapp number na 07012181461 for those da basu da account sainai adding dinki a group din danake posting kullum_
Da asuban fari Kaka ta tashi tana mitsike ido tana salatin annabi ta wuce bandaki tayo abunda zatayi tafito daure da alwala tadau charbin ta tasaka hijabi tahau kan sallaya ta kabbarta salla, saida gari yay haske sanan ta sallame ta ijiye hijabin kan kujera tafito tabude kofar sasan ta tafita tai dayan sasan indata tarar da Hamida da Zainab suna sharan compound din, Hamida ce tafara gaisheta tana murmushi tana sunnar dakai.
Chapter 37 · 0% Book details