← Book details In Bani Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 70 OF 101

Sashe 70

In Bani Complete Hausa Novel · about 8 min read

"shasu agabana" karba yayi yana murmushi sosai yasha sanan ya mikamai ruwan yana turo baki yace "ni massage nakeso ma" dunguremai kafada Aadil yayi yana murmushi yace "bara ayiba din" dariya dukansu suka hau yi gaban wardrobe yaje ya zaromai kaya kaman wanda yasa ajikinshi amma light blue t-shirt ne da black trouser yakawo mai yace "tashi kasa to" tashi yayi yasaka kayan Aadil ya karbi bathrobe din dayacire yawuce bathroom yaje ya ijiye Aabid yabi bayanshi da kallo sosai hankalinshi ya kwanta zuciyarshi tamai wasai, dawowa falon yayi daidai lokacin Aabid ya kunna system dinshi yace "zoka gani" kusa dashi yaje ya zauna system din Aabid ya dauramai akan cinyarshi yace "this is our company tunda aka haife mu Baffa yabamu kyautan shi inji Mami dan itane ma keta mana managing company kafin na gama karatu na cigaba, kampanin katako ne and is selling sosai u can go through it, yanzu dai yaro kanada chance kai amarcin ka da kyau dan once munkoma Nigeria you will resume office now that u are back akwai alot of things da zamu yi tare, akwai wasu kudin profits da kampanin ke making danake ta taramana awani separate account, inaso mu bude other side business dashi, sanan inaso mubude big islamiya da za'adinga koyar da yara free mai hade da masallaci zamuyi da sunan Abie ko ladan yadinga kaimishi how did you see?" ahankali Aadil yadaura kanshi akafadarshi yace "yes hakan nada kyau, Allah ya gafarta mai" daidai nan aka bude dakin aka shigo atare dukansu suka daga kai ganin Mami ce tana sanye cikin plain bakin doguwan riga fuskarta ba kwalliya looking simple ganin yanda take kallonsu yasa duk sukai murmushi, murmushi itama tayi dan sosai taji dadin ganinsu tare tsayawa tayi akansu tace "having brothers time, anyway Aadil oya kawo kudi inaso maid taraka Hamida saloon taje ta gyara gashinta ne driver ya kaisu, sanan inaso nasa amata shopping din kaya" turo baki Aadil yayi a shagwabe, shima Aabid turo baki yayi a shagwabe yace "Mami bakinada kudi ba saikin karbi kudin Dil" baki Mami tayi tana kallon su tace "ikon Allah nikuke ma iskanci, ba matarshi bace ni zanmaka abinda Allah ya daurama, common give me money kafin dagakai har wanda ke daurema gindin na sassaba muku" kaman zai mata kuka Aabid na danne dariyarshi ya tattaba aljihun jikinshi yace "ni babu cash ajikina nabar wallet adaki" kallon Aabid Mami tayi tace "kai aramai to" turobaki shima yayi yace "ni ko ficika bandashi Mami na" tafi Mami tafara tana salati.

"nizakuma iskanci yaran nan?" atare dukansu suka fashe da dariya kafin Aadil yafito da ATM card dinshi yamikama Mami yace "Mami wlh nidai nidai" hararanshi tayi tace "don't even waste ur saliva kaf abinda take bukata saina zare kudin ansaya, ja'irin banza" murmushi yayi yabi Mamin da kallo yana wani irin jin son ganin Hamidan yana kewanta amma hakanan ya daure ya danne, cigaba da nunamai abubuwa Aabid yayi a system har lokacin azahar yayi, salla suka fita suyi daganan suka shiga gari.

Saloon maid din tafara kai Hamida bayan tadau measurements dinta na waist da jiki tabiya kudin komi kaman yanda Mami tace harda gyaran jiki amata sanan ta wuce wani babban boutique ta kwasoma Hamida fitinannun english wears da jeans kala kala na mata, sai wuraren 4 suka dawo saloon din tareda driver ta tarar an gyara mata gashi sosai, koda ta shigo ta tarar an gyarama Hamidan gashi an mata jan lalle a hannayenta dasuka karama fararen hannayenta kyau sosai kaman wata sabuwar amarya, murmushi tayi tace "kinyi kyau sosai madam" dan murmushi Hamida tayi amma har cikin ranta jitake kaman karsu koma gidan ko kadan bataso taga Aadil, saida aka gama tsaf jikinta sai kamshi yake tai wani irin arnen kyau sanan suka tafi maid din sai kallonta take mota suka shiga driver yajasu koda sukakai gida lokacin ana kiraye kirayen sallan magrib.

Daidai zasu shiga gidan Aadil da Aabid na fitowa zasu tafi masallaci, hada ido sukayi da Aadil daya bita dawani irin kallo kaman zai hadiyeta, saukar da kanta kasa tayi da sauri gabanta na faduwa suka shiga gidan, hanunshi Aabid yaja yace "wanan kallo haka aisaika cinyeta da ido Dil" dan murmushi Aadil yayi a kunyace ya dauke kai, murmushi Aabid yayi nothing beat his brother's happiness awurinshi, shiyasan Aadil nama Hamida son dashi kanshi baisan iya son dayake mata ba, masallaci suka wuce da sauri ganin antada sallan.
fitowa sukayi daga motar sukai part din Mami, a falo suka tarar da Mami kan dadduma ta idar da salla ta kishingida da kujera, murmushi tayi ganin Hamida tare da maid din sun shigo, kanta akasa takaraso kusada Mami ta zauna akasa kanta akasa tana wasa da bakin hijabinta tace "ina yini Mami" hanunta Mami ta karba tana kallo tace "iyye daughter na anyi kyau, wanan lalle ja haka badai kyauba, ya kan an gyarashi shima?" gyadama Mami kai tayi tana kokarin cire hijabin dan ta nuna mata Mami tace "barshi basai kin budeba kin gaji tashi kitafi shashinki kiyi wanka kiyi bacci kihuta abinki, bari Mard tabiyoki da abincin ku, nasa anmiki slicing fruits make sure kinsha kinji daughter na" gyadama Mami kai tayi tace "to Mami na" tamike tsaye maid din kuma tai dining ta kwaso big warmers din guda biyu tabita dashi har shashin su, a dining ta ijiye abincin sanan ta shigoma Hamida da manya manyan jakunkunan kayanta guda uku sanan tamata saida safe tafita dan murmushi Hamida tayi dudda she's so happy da kayan amma fargaban Aadil yasa takasa murnan yanda yakamata, a gurguje tai bathroom wanka tayi sanan tai salla wani maxi doguwan rigan bacci tasa na silk daya tsaya mata a guwiwa pink yabi fatarta sosai yanada open neck, ta chusa gyararen gashinta dake kamshi sosai cikin net, ta feffesa jikinta da turarukan ta sanan tafito dining ko ina na kamshin turarukan ta, warmers din kan dining ta bude taga tuwon shinkafa ne da miyan egushi akayi, sai sliced fruits dakeda sanyi sosai acikin wani while ceramic bowl, kasa cin tuwon tayi dudda ya burgeta sosai tadau fork tasa a bowl din tafara shan fruits din, sosai tasha dan sun mata dadi, kadan kawai tarage tabude fridge tasaka sanan tawuce falo kayan ta tatare ta gyara wurin takoma falo tadauko wani blanket daban tadawo falo ta kwanta kan kujera ta lulluba da bargon ta lumshe ido danta gaji sosai yautaci kuka kanta sai sassara mata take ko 20min batai da kwanciya ba bacci yay awon gaba da ita.

Dawowa daga masallacin sukayi around 8:56 suka shigo gidan, zaiyi part dinsu Aabid ya ballamai harara yay pointing din shashinsu yace "go to your house, Allah ko innai aure kafin ka ganni haka chab saidai idan na fito salla, zanci amarci sosai bana wasaba kaganni nan, zanci amarci na bama da tsinke ba da toothpick znci" ware ido Aadil yayi cikeda isgili yace "kadinga mene to?

Me toothpick zaima?" hararanshi Aabid yayi yatura bayanshi yace "gud night jor, greet our wife, Allah bamu alkhairi" ahankali yace "Ameen" Aabid yajuya ya shiga part dinsu shikuma yay hanyar part dinsu baida burin daya wuce yasa Hamida a idanunshi, ahankali yamurda door handle ya shiga cikin dakin wani cool sassanyar kamshi ya daki hancinshi, kafe Hamida dake kwance kan kujera ta lulluba da bargo harkai yayi da ido yayi heart dinshi na beating fast wani irin force kaman magnet na pulling dinshi to her, cold feet dinshi yadaga yafara tafiya haryakai wurin dogon kujeran, tsugunnawa yayi agaban kujeran yana kallonta ahankali yasa hanunshi yaja bargon kasa kadan haka ya bayyanar da fuskarta tareda wani kamshi dayamai sallama dake tashi daga jikinta, kafe fuskarta yayi da ido tai wani haske bau lips dinta sunyi pink sosai da dogon hancinta da tip dinshi yay ja kaman wacce take mura, net din data saka akai ya zamiye yay baya hakan ya bayyanar da black gyararren gashinta dake kamshi, gashin gaban goshinta sun kwanta lub, she was looking breathtaking and very innocent kaman ka dauketa ka gudu yanda heart dinshi ke bugawa yasa yakai bakinshi ahankali yama kumatunta Light kiss sonta na ratsa kowani jijiya na jikinshi, tashi yayi yaja bargon jikinta ya ijiye a gefe yanabin dogayen santala santalan fararen cinyarta da kallo kafin ahankali cike da dabara ya dauketa a hannu zaiyi bedroom da ita, firgita tayi tabude idanunta cikin bacci ta kallai, hada ido sukayi.
[12/22/2019, 10:14 AM] Aishat Muhammad: .......
_Masu fitarmin da novel kuda Allah, ban yafeba_
_masu karanta min novel batare dakun biyaba ban yafeba kuda Allah, pay anan ko pay achan, your choice_
_novel dina nakudi ne just 300,in kinaso chat me up a watsapp ta number na 07012181461_
Hada ido sukayi da Aadil dake kallonta kaman zai hadiyeta afirgice tasake ware idanunta ta kallai duka baccin dake cinta na clearing daga eyes dinta duka heart dinta na racing sosai, hanunshi dake ta bayanta ta ture da sauri tana kallonshi tana kokarin sauka kasa lips dinta na rawa amma yaki bata chance din, bude kofa yayi ya shigar da ita bedroom dinsu ahankali ya zaunar da ita abakin gado kaman ya ijiye kwai da sauri ta mike tsaye zata gudu hanunta ya rike gam da sauri yana kallonta asanyaye dan yasan shimai laifine, ahankali yay kneeling yakai gwuiwowinshi duka kasa yakama dayan hanun nata yarike yana kallon fuskarta yanda har lokacin kanta ke kasa takasa kallonshi jikinta sai rawa yake, sosai yaji zuciyarshi ta tsinke ahankali yakira sunanta.
Chapter 70 · 0% Book details