← Book details In Bani Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 101

Sashe 24

In Bani Complete Hausa Novel · about 8 min read

I want rice with meat balls, i want yam fritata, i want smoked prawns" zaro ido tayi ta kalleshi dan wlh wasu abincin ma daya kira batasan suba hakan yasa tabuga uban tagumi ta lankwashe kafa tana kallonshi inda ace za'a gwada jinin ta yanzu sai anga yahau dan wlh fargaban gobe take, kukan shi ne yasa ta dago kai da sauri ta kalleshi sosai yabata tausayi dan ayanda yayi gaskiya baisan abincin bane, da sauri tace "zakaci biscuit to?" gyadamata kai yayi yana neman fadowa jikinta da sauri ta tashi tabude sip dinta, chan saman kayan ta taboye biscuit din sabida kar Ihsan tagani ko Zainab ta dauko guda biyu ne short bread biscuit tadawo ta zauna agabanshi ta mikamai, karba yayi da sauri yana murmushi yana kallonta sanan yabude daya ya ijiye daya agefe yasa hannu yaciro biscuit daya ya dago kai da sauri ya kalleta kaimata dayan bakinta yayi da sauri ta kalleshi, murmushi yamata yana wani irin kallonta kaman wani mai lafiya ya ware manta manyan idanunshi dake cike da bacci gashin idon duk sun tattare sabida lema leman ruwan hawaye yace "eat my wife yay" zaro ido tayi ta kallai, fari yamata da ido yana goga mata biscuit din a lips kaman yana shafa mata jan baki yace "eat, haaa, haaa, hamm" yay maganan yana bude mata baki kaman yanda akema small baby yaci abinci, dan murmushi tayi ganin yanda yake bude mata baki bama tasan lokacin data saki murmushin ba sabida yanda yay maganan dan har yasa ta manta da fargaban datake ciki na gobe, ahankali tasa hanunta ta karbi biscuit din daga hanunshi takai bakinshi tai murmushi tace "kaika ci kaine kejin yunwa, eat" bude bakin yayi da sauri kaman jira yake ya balli kadan yanaci yana kallonta lumshe ido yayi yana taunawa saikuma yabude idon ya kalleta suka hada ido yace "is very sweet" ya fizge rogowan daya rage daga hanunta yakai bakinta yace "eat my wife" dan kallonshi tayi dan duk idan yace my wife"sai gabanta yafadi tadan balli kadan da sauri yatura sauran bakinshi yataso yadawo kusada ita kaman an jehoshi ya kwanta ya daura kanshi kan cinyarta yanacin biscuit din yana kallonta yana mata murmushi sosai wani irin farin ciki yakeji idan ya kalleta fiye da misali dan ko damuwa dasu Mami ma baiyiba shi kawai bayason ta barshi konan da chan, tagumi tabuga itama tana kallonshi tana tunani sosai, maganan shine yadawo da ita daga duniyar tunani yace "water" pure water daya ta dauko ta mikamai, tashi yayi ya zauna ya karba yana kallon ruwan yana juyawa dan bai taba shan irin wanan ba, ganin haka yasa ta karbi ruwan tabude mai takai bakinshi da sauri ya kafa baki tareda daura hannayenshi kan nata yakara rike ruwan da kyau yanasha, wani irin sanyi taji har brain dinta da sauri ta lumshe ido saida yakusa shanye ruwan sanan ya janye kai yana murmushi yana kallonta, dan murmushi tayi itama ta dauke kai tadau marfin kulolin abincin tana rudewa tace "jeka kwanta akan gado" make mata kafada yayi ya nuna mata kan dadduman data kwanta akai dazu yana turo mata baki yace "lets sleep there" kallonshi tayi saikuma ta chusa kanta kan kafarta tai shiru abin duniya yay mata yawa, wanan wani irin kaddara ne tahadu dashi, shima shiru yana kallonta duk sai yaji wani iri kaman baida lafiya sabida yanda ta kifa kai taki kallonshi, ahankali ya share hawayen daya zubomai kaman maraya ya kwanta akasa a gefenta ya jefar da ragowan biscuit din dake hanunshi yana kallonta yana lumshe ido yana goge hawaye, ahankali kaman matsoraci ya dafa kafadarta yakira sunanta "my wife" ture hanunshi tayi cikeda masifa data dade batai irinshi ba dan tagaji da yanda yake tabata yace"leave me alone" ta turemai hanun tasake maida kanta kan guwiwa, matsawa baya yayi atsorace yana kallonta yasaki kuka ahankali yana share ido da bayan hannu, ahankali ya kwanta akasa awurin yana kuka sosai yana kallonta so kawai yake tadago kai ta kalleshi, haka bacci yasake daukan shi kaman zaiyi ihu.
[11/11/2019, 6:48 PM] Aishat Muhammad:
IN BANI
Maman Abd Shakur
21...
_this novel is for sale, karki karanta in baki biyaba, in kika karanta ina binka bashi, pay anan or pay achan_
_in kinason novel dinan zaki turo 300 access fee to 3107021073 first bank aisha Muhammad, saiki turo evidence of payment ta watsapp number na 07012181461_
_you can also send MTN card ta watsapp number na 07012181461, sainai adding dinki a group din danake posting_
Saida tajishi shiru sanan ta dago kai idanunta sunyi jajir ta kalleshi, sosai taji wani irin tausayinshi yanda ya dukunkune kaman wani maraya, zanin lullubanta tajawo ta lullubeshi dashi sanan ta tashi tahau kan gadon ko minti biyu baya karaba wani bacci mai nauyin gaske yay awon gaba da ita.

Wuraren karfe biyar na asuba Kaka tazo tabuga kofarta.

"Hamida, Hamida wai bazaki tashi kiyi salla ba iyye yarnan?" da kyar ta iya bude ido cikin bacci ta kalli inda take kafin ta kalleshi ganin har lokacin yana kasa bacci yakeyi sosai ya dukunkune kaman maijin sanyi yasa ahankali tace "natashi inakan dadduma ne Kaka" kwafa Kaka tayi ta wuce dakinta tana masifa tace "yau bazaki zo dakin nawa muyi tareba, kyaji dashi mai bakin hali" tahau kan dadduma takabbarta salla, yunkurin tashi tayi daga kan gadon takasa takara komawa ta kwanta wani banzan bacci ne yakara tafiya da ita dan tamugun gaji gashi batai baccin kirki da daddare ba sabida Aadil dinan.

Wuraren bakwai ta iya farkawa daga baccin da kyar, ahankali ta karanto addu'an tashi daga bacci tabude idanunta ahankali tana kallon window dakin yanda rana ya hasko har zuwa tsakar dakin ta tashi zaune tana dafa zanin katifar gadon abune taji ya soke mata hannu hakan yasa ta kalli gefenta da sauri ledan biscuit din data bashi jiyane tagani ya ninnike ya maida shi suffar flower da sauri tadau ledan biscuit din tana juyawa tana kallo tadanyi murmushi ta mika hannu zata ijiye idanunta suka sauka akan yar takarda akan gadon da sauri ta dauka tajuyo da paper, zanen fuskan mutum ne yana kuka saiya rubuta sorry my wife a gefe, dan murmushi tayi saikuma ta tabe baki ta juyo dakai da sauri danta kalli inda yake taga bashi awurin, da sauri ta mike tsaye tana kalle kallen dakin ganin bashi yasa tai kofar bayin ta tsaya tai knocking har sau biyu, jin ba'a amsaba yasa tabude kofan da sauri ta leka amma babu kowa cikin bayin, dawani irin sauri tai hanyar kofan ta tana karanto addu'a aranta ta kalli sakatan data saka ganin babu sakata ko daya yasa gabanta yawani irin mugun faduwa, juyowa tayi ta kalli tsakar dakin ganin har lokacin akwai sneakers dinshi akasa yasa taji cikinta yawani irin yamutse ya kulle sosai tsabagen tsoro, kaman daga sama taji Kaka taja wani dogon ihu tabuga uban salati.

"innalillahi wa innailaihi raji'un jama'a, Sama'ila, Sama'ila" ta kwalama Abban su kira, arude ta dafa kirjinta dake neman tarwatsewa yadena aiki koina na jikinta na rawa "jama'a gardi a sasa na kufito, Sama'ila" karan bude kofan sasan Kaka taji saikuma taji muryan Abban su yace "lafiy..." bai karasa ba taji yay shiru, muryan Mama taji itama bayan ta turo kofan sasan Kaka arude tace "Umma lafi..." jitayi gabaki daya jijiyoyin jikinta sun dena aiki tsabagen wani irin shegen tsoro da fargaba dasuka dirar ma zuciyarta, ahankali take matsawa tana jan kafarta dasuka mata wani irin nauyi sosai tana komawa baya, maganganun dataji afalo da tsabagen tsoro yasa tama kasa gane me'ake cewa yasa ta sanya hanunta akan bakinta tana kokarin taushe wani irin kukan dake shirin kufce mata, tura kofar dakinta akayi da karfi suka hada ido da Aadil, da gudu Aadil dake sanye da dogon wandonshi da farin singlet ya shigo dakin hanunshi duk ruwa kaman yay wasan ruwa, da gudu yayo wurinta kafin ma tai yunkurin matsawa ganin kanta yayo ya shige bayanta ya riketa gam gam ya sakin mata kuka awuya kirjinshi na bugawa sosai, daidai lokacin su Abba suka bude kofan dakin suka shigo, da sauri ya daga hanunshi yana rikiketa yanuna mata su Kaka yace "my wife see this people they're scary, sunata kallona am sacred, hide me" yay maganan yana kara komawa bayanta hanunshi duka biyu akan cikinta ya riketa gam cikin tsananin tashin hankali ta fara kokarin turashi daga bayanta da kafadarta take amma ya riketa gam ta bayanta yana make mata kafada yasakin mata kuka ahankali yana kara kankameta, daga idanunta tayi dasukai jajir tahada ido dasu Kaka, Abba, Mama, dasu Zainab daduk sun kasa magana sunyi suman tsaye sun kasa gasgata abinda idanunsu ke gane musu, sai Ya Faruk dake sanye da kayan sojoji shigowanshi gidan kenan ganin yanda su Abba suka shigo dakin Kaka da gudu yasa yabiyo bayansu shima ya tsaya a gefen Zainab ya zubama Hamidan ido kirjinshi nawani irin tafarfasa, fashewa Hamida tayi dawani irin kuka ganin yanda yan gidansu ke kallonta ta fizge hanunshi daga kan cikinta da karfi tawani irin tureshi cikin tsananin fushi har yana buga bango tace "let go off me" da sauri tai wajen Abba ta kalli Abba cikin tsananin faduwan gaba tana kuka bakinta har rawa yake tace "A..bba wl..." cikin wani irin zuciya Abba ya dauketa dawani irin hadadden mari da baitaba mata shiba tunda ya haifeta jikake "pau!" tai wani irin tangal tangal tai baya zata fadi tsabagen yanda marin ya shigeta zaro ido Aadil yayi yazo wajen da mugun sauri yatare ta tafado jikinshi luuu kaman wacce ta suma, fashewa da kuka sosai Aadil yayi ya kalleta yanda take kokarin ta bude ido ma takasa, cikin wani irin tsananin fushi da zuciya yawani irin kalli Abba, fizge ta Abba yayi daga hannunshi cikin fushi yakara daga hannu zai sharara mata mari Aadil yawani irin fizgota da karfi ya rungumeta ajikinshi ya kankameta sosai kanshi na girgiza wa sosai jijiyoyin gaban goshinshi sun fito idanunshi sunyi jajir ya kalli Abba da jajayen idanunshi yay wani irin ihu ya nunamai hannu yace "stop beating her mugu".
Chapter 24 · 0% Book details