← Book details Hayatul Mahayat Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 41

Sashe 8

Hayatul Mahayat Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

" Salimat maiye haka wato kingama sayar da mutuncin ki awaje shine kika kawomin saura cikin gidana ko to wallahi ban kasance mazinaciba bazan zauna da mazinaciya ba nasan akwai matan da budurcinsu ke tafiya batare dasun yin ma'amala dawani d'ah namiji ba amma dole akwai banbanci kekam dagaji bama namiji d'aya kike ma'amala dashiba Allah sarki Zarah takawomin komi a irin wannan daran seda tasa namance waye Aliyu amma banko tausaya mata ba na adana komi akan ki ina jiran nabaki komi dana hana Zahra amma kasss Zahra tafiki daraja agurina yanzu "

Tashi yayi yafita afusace d'aga kafad'ar ta tayi alamar ko ajikina wayar ta tad'aga takira wani tajima tana waya tana dariya a'karshe tace

" gaskiya yakamata kasan yadda zakayi yashigo dan ina cikin matu'kar bu'kata kashe wayar tayi babu jimawa wani mutun yashigo cikin part d'in har cikin bedroom d'in yashiga tana ganin shi tayi saurin tashi tarungume shi kissing d'in shi tayi sannan tace

" ammafa banyi tunanin zaka iya samun damar shigowa cikin sau'ki hakaba ? "

Murmushi yayi yad'auketa yad'aura saman bed sannan yace "taya shigowa nan zebani wahala ina 'kanin sarki kuma matsayin uba agurin mijinki ayni wannan auran ni akayimawa kinga yanzu zamuci amarci "

Cikin shagwa'ba tace " to amma inajin tsoran karya sakenifa ? " murmushi yayi yace " ina hakan bazai yiyuba duk abinda nacema mahaifin mu dashi yake yarda dan haka kibarni dakomi har shi sarkin bai isaba balle d'anshi bari nakulle 'kofar nazo musha angonci "

Tofa lalle Aliyu ga sakamakon cin zarafin Zahra dakayi muje zuwa

Muzaffar nashiga cikin motar yasa akajata aguje babu inda suka tsaya se gidan shi sawa yayi aka shiga da ita ciki shikuma yatsaya basu umarnin wani ayki yana gama sallamar su yashiga ciki rai'bace

Hanyar bedroom d'in shi yanufa ji yayi an ri'ke mai 'kafa kallon 'kafar tashi yayi Sudees ne sefaman d'aga mishi hannu yakeyi alamar yad'aukeshi niyar janye 'kafarshi yayi amma seyaji duk jikin shi yayi sanyi tsayuwa yacigaba dayi agurin ganin haka yasa Rayhana tasowa d'aukar Sudees d'in zatayi amma ya'ki sabida yari'ke 'kafar wandon shi kam da'kyar ta 'banbare hannun shi tad'aukeshi ayko yasaka wani irin ihu cikin sauri Muzaffar yashiga cikin bedroom d'in sabida jin kukan yaron dayayi har cikin kanshi

Yana shiga yazauna bakin bed amma yakasa kauda hankalin shi daga jin kukan yaron wanka yashiga har yafito yanajin kukan su dan yanzu su duka sukeyin kukan shiryawa yayi cikin kananun kaya yafito parlour fuskar shi amatu'kar tamke nufo inda suke yayi du'kowa yayi yad'auki Sudees sannan ya yad'auki Shureem lafewa sukayi saman 'kirjin shi suna sauke ajiyar zuciya komawa cikin bedroom yayi dasu

Cikin zuciyar shi yace

" abun mamaki maiya suke kuka sabida na'ki d'aukar su ? OK natuna shidama yaro yanason namiji yad'aukeshi gashi har sunyi shiru Allah sarki Farooq da Haydar ko kuna raye Allah masani hmmm dole nahukunta mahaifiyar ku sabida tayimin abinda banta'ba tunani ba nafasa kaita gida ayanzu harse natashi komawa amma sabida kune dan naji ina bu'katar kasancewa daku gata 'yar 'karamar yarinya da Twins dan bazata wuce sa'ar Zarah ba tur Allah ya kyauta na iya auran kamar wannan Allah madeyasa 'ya'yan sunnane "

Babu jimawa bacci yad'auke su kwantar dasu yayi yazubamusu ido yarasa maiyasa yakejin yaran cikin zuciyar shi gashi yana ganin kamar suna yimai kama dawata fuska amma yakasa tuna wacce fuskace fita parlour yayi cikin sauri Rayhana tami'ke gurin shi tanufo batare dajin sakkaba tace

" ina yarana ? " tamke fuska yayi sosai hannu yad'aga yakifa mata mari had'ida tureta cigaba datafiya yayi baiko waigaba dining yanufa zama yayi yabud'e abinci cikin tsawa yace

" keee zonan " cikin tsoro Rayhana tanufi inda yake dan kam ayanzu tafarajin tsananin tsoran shi danta lura bashida sassauci kwata kwata tana isowa ta tsaya gefan shi cikin zafin rai yafizgota wani irin ran'kwashi yakafa mata wada yasata durkushewa tace

" ya subahalallah " sabida wani irin zafi dataji har cikin ranta murya cike da izza yace

Kina ganin zanci abinci amma bazakizo kisamin ba ko bakisan ayanzu matsayin baiwa kike agurinaba ? haka zaki dauwama kina yimin bauta har 'karshen rayuwar ki "

Cikin sanyin jiki tazubamai abincin komawa tayi gefe sake kiranta yayi yace " zama zakiyi kidinga bani labarai masu dad'i har nagama "

Zaro ido Rayhana tayi dan kam ita batawani iya bada labariba zama tayi tatakure jikin ta gefe d'aya cikin tsoro da shakka tashiga bashi labari shikam bama jinta yakeyi ba hankalin shi yatafi wajan tunanin Nabila

Bai wani ci abincin sosai ba yami'ke taku d'aya biyu yayi yatsaya yace " zaki iya cin abincin " cikin rawar murya tace

" banajin yunwa amma dan Allah naji zan kasance a 'kar'kashin ikonka amma dan Allah kar hukuncin dazaka yimin yashafi yarana sannan kabarni nakoma na d'akko musu kayan sawa "

Rai 'bace Muzaffar yajuyo komawa yayi ya zauna fuska tamke yace

" ke ko kunya bakijiba nafurta cewa yarana ? dubekifa yar 'karamar yarinya dake to waima ina mahaifin yaran ? "

Du'kar dakanta Rayhana tayi tace " yagudu yabarmu ayanzu bansan ina yake ba gashi banida kowa se yarana inajin idan wani abu yasame su tabbas zan iya mutuwa "

Ta'karashe fad'in maganar cikin kuka tashi Muzaffar yayi yabar gurin dan shikam bayason kukan mace fita yayi daga gidan gaba d'aya cikin sanyin jiki Rayhana tami'ke komawa tayi tsakiyar parlour jitayi ance

" masha Allah Rayhana yau Allah yakawoki gurin mahaifin su Farooq wannan shine yarima Muzaffar Abdurrahaman Al'amin d'ah mafi soyuwa gurin Sarki Abdurrahaman da Sarauniya Kilishi dukda kasancewarsu su 3 amma sunfi sonshi karki damu Rayhana komi zai wuce Muzaffar bazai tsani yaran shiba sabida jini dabanne amma ke zakisha wahala agurin shi sabida ayanzu yatsani mace babbar matsalar ma sekin shiga cikin masarutar su sabida akwai munafukai dayawa aciki zan sanar dake wasu kalmomi wanda Nabila take yimai magana dasu hakan zaisa kisamu sassauci agurin shi

Sannan kisamu kariya agurin shi kafin ku koma cikin masarutar HAYAT sabida ana matu'kar jin tsoran shi cikin masarutar su sabida bashida sassauci darajar wannan kalaman zasusa yahana acimiki mutunci inde agaban shine sannan ki'kara adana wannan box d'in dan idan wani yaganshi to wallahi zakishiga cikin masifa zamu hana kowa gane fuskar yaran har zuwa wani lokaci mai tsayi dukda sunyi matu'kar kama da mahaifin su shima bazai gane hakan yanzu ba sabida idan har aka gane akwai matsala ga kalaman kamar haka "

Sanar da ita komi tayi sannan tayi mata sallama wani irin farinciki Rayhana taji ko babu komi su Sudees zasu kasance tare da mahaifin su har Muzaffar yadawo su Sudees suna bacci wasu kaya yasa aka shiga shigowa dasu cikin wani bedroom yasa aka kai kayan le'ka bedroom d'in shi yayi har yanzu bacci sukeyi parlour yadawo yazauna kiran Rayhana yayi gaban shi tadu'ka tsayin lokaci yana latsa wayar shi sannan yace

" Cikin wancan bedroom d'in zaki zauna duk abinda yaranki zasu bu'kata akwai aciki sannan daga yau ki boye maganina sabida banason kallon fuskar mace inba ta mahaifiya taba ki tabbatar kin kiyaye dokokina aduk lokacin danazo cin abinci yazama nasameshi a dining kullum zaki garamin bedroom d'ina sau 3 koda banshigaba sannan aduk lokacin dana shigo nasamu kaf cikin part d'in nan a gyare tun asuba zaki fita kibama duk wata tsirre dake cikin harabar gidan nan ruwa kuma ke zakidinga wankemin motar dazan fita nahutar dakowane ma'aykaci daga yau "

Dukda razanar da Rayhana tayi sabida jin wannan uban aykin duk ita kad'ai amma seta dake tace

" in sha Allah bazakasami matsala agurinaba Sojana "

A razane Muzaffar yadubeta ga tsananin mamaki daya bayyana cikin idanun shi danjin mai Muzaffar zai cema Rayhana kubiyini

Waziri da Alhaji Yusuf 'kanin Sarki zaune gaban boka 'yan zanezanan shi boka yayi yabushe da dariya sannan yace ayki zai yiyu

Wani abu yami'ko mushu cikin kwalba yace " kunga wannan kuje kusashi 'kasan gadon Sarki dazaran ya kwanta shikenan bazai 'kara yin lafiya ba shida fitowa fada babu rana daga nan seka samu damar ri'ke masarutar har kagama cinmma burinka tashi kubani guri "

Tashi sukayi suna godiya baki d'auke da sallama Arfat tashiga cikin part d'in Kilishi cikin ladabi tagaidata zama tayi gefan Mu'azzam dake zaune gaban mahaifiyar tashi kafin Kilishi tace wani abu

Cikin sauri Arfat tami'ke cikin toilet tanufa tafara kwara amai hankali tashi Kilishi tabi bayanta zuciyarta tana tsananin bugawa

Daga Al'kalamin........✍🏻

NPEEDY A AJI 🌸🦚🌸

Comments and shine please

Love u all sisters 🥰🌹
[10/9, 9:33 PM] NPEEDY A AJI: 🌸 *HAYATUL MAHAYAT* 🌸
🦚🦚🦚🦚
🦚🦚
🦚
Story and written
By
NPEEDY A AJI

Dedicated to
My yar amana

🌸NOORUL HAYAT🌸 WRITERS ASSOCIATIONS

🌹Expressions and heed Searching Sweet story Novels writer🌹
>>>>>>>>>>>>>>>>>>>
We are together all fans🤝🏻🥰
KAFA'DI ALKHAIRI KO KAYI SHIRU 🤫

My Novels
1-NAYI RAYUWA DAKE
2-SANADIN ACCIDENT
2019
3-SAKAYYAR CUTA
4-RUFAFFIYAR ZUCIYA

HAYATUL MAHAYAT
typing......✍🏻

Bismillahir Rahamanir Rahim

🅿 15 & 16

Tsayin lokaci Arfat tana amai sosai tagalabaita Momy ta taimaka mata wajan gyara gurin bata nemi kowaba ri'ke da ita Momy tafito daga toilet d'in kwanciya tayi saman cushion cikin tashin hankali Momy tace

" Mu'azzam kadubamin Arfat dan tabbatar da abindake shirin tarwatsa zuciya ta "

Cikin wani yanayi Mu'azzam yace " Momy ay basena dubataba cikine da ita tun tuni nafamimci haka "

Salati Momy tashigayi cikin damuwa tadubi Mu'azzam tace " wannan wace irin 'kaddara ce ? sunan wa wannan yaron ko yarinyar zai amsa a cikin ku ? "

Murmushi 'karfin hali Mu'azzam yayi yace

" sunana mana Momy nida Muzaffar d'ayane hakama yaranmu d'aya ne Momy dan Allah karku bari Muzaffar yasan cewa wannan cikin yanada ala'ka dashi nayi al'kawarin ri'keshi tamkar nawa "

Tashi Arfat tayi zaune tace

" Momy tayaya za'ayi haka kuyi ha'kuri amma dole Muzaffar yasan cewa wannan cikin nashine " kukan munafurci tasaki lallashin ta momy tashigayi shiko Mu'azzam fita yayi daga part yanajin zafi cikin zuciyar shi

Cikin matsanancin ciwon ciki Samha take juyi saman bed wanka Muzanbil yafito bayan yagama shirin shi tsaf yafito parlour zama yayi yana kallon news jin shiru babu motsin Samha yasa Muzanbil yace

" anya wannan yarinyar lafiya take kuwa ? yau tunsafe ban gantaba abinda bata ta'ba yiminba "
Chapter 8 · 0% Book details