← Book details Hayatul Mahayat Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 41

Sashe 26

Hayatul Mahayat Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Misalin 11:40pm Rayhana tanufi part d'in Ummi zaune take tana kallon TV babu kowa cikin parlour se ita'kad'e yara duk suna cikin bedroom wasu sunyi bacci wasu sunata chanting cikin waya Rayhana tale'ko ganin ita 'kad'ece yasata sauke ajiyar Zuciya nannad'e paper tayi tawurgo mata cikin sauri Ummi tami'e waigawa tayi amma babu alamar kowa cikin sauri da rawar jiki tabud'e parpar tun kafin ta'karasa karantawa zufa taji'keta shakaf dukda sanyin A.C dake cikin parlour duk Rayhana tana kallon ta cikin karfin hali Rayhana tashiga cikin parlour ganin mutun cikin fararan kaya yasa Ummi bud'e baki zatayi ihu cikin sauri Rayhana tajawota rufe mata baki tayi sannan tasha'ke mata wuya tashiga furgitata sabida tsananin tsoro yasa ummi sumewa cikin sauri Rayhana tasaketa tafita part d'in mami tanufa adede lokacin suna zaune su biyu itada umma suna tattauna yadda zasu billoma wannan al'amarin dankam suna cikin tsoro wurga paper tayi cikin mamaki
Mami tace " wannan kuma daga ina? kode iskace takawota " arazane umma tami'ke tace " ina garinda babu hadari taya iska kuma " d'aukar papar tayi tabud'e tare suke karantawa saurin ri'ke cikinta mami tayi sabida wani murd'awa dayayi cikin shihada Rayhana tashigo parlour sandar hannunta tad'aga tace

" duk wanda yayi ihu to tabbas yau zamutafi tare dashi dan haka kusanar dani yadda kuka shirya kasheni idan kukayi haka zanbarku natafi amma idan kuka'ki to babu shakka tare zamu tafi kunga de irin halinda kaka tashiga to nata mai sau'kine tunda babu hannunta cikin kisan sede 'kiyayyar datake yimin ina yarana ? Cikin razana Mami tace " Wallahi babu hannuna cikin sace yaranki Ummi ce da umma suka shirya haka kuma suka aywatar haka kisanki banibace d'anane Nura yayi yayi kibashi had'in kai kin'kin shine yayi miki fayd'e ganin idan yabarki zaki tonamai asiri yasa yakasheki amma ni babu ruwana sede nasashi yagudu " cikin raunin murya Rayhana tace yana ina ? yana cikin India kefa Umma ina yarana ? murya sha'ke tace " Allah bamu kashesuba amma munyi nesa dasu mun kaisu cikin wani daji dayake cikin 'kasar Cameroon amma Allah duk Hamdiyya ce tashirya hakan jin 'kamar motsin tafiya yasa Rayhana saurin cewa

" kuyi gaggawar sanarda maimartaba komi da Mijina Muzaffar idan bahakaba to zandawo kuma idan nadawo kasheku zanyi cikin tsoro " Rayhana tad'ago agogon hannunta tayi magana 'kasa 'kasa yaya Ibrahim akwai matsalafa ana shirin shigowa gashi zanfita saurin tashi yayi yafita dede lokacin da Jafar yashigo cikin parlour lokacin mami tasaki ihu kuma dede lokacin wutar cikin masarautar tad'auke duka aguje Rayhana tafita tana isa cikin part d'insu tashiga bedroom d'in Nabila toilet tashiga tana sauke ajiyar Zuciya sedata numfasa sannan tafito dede lokacin Muzaffar yashigo tamke fuska yayi yace

Tun d'azu nike shigowa cikin bedroom d'in nan amma sede najiki cikin toilet ko mai kikeyi cikin shi har yanzu ? seda kikaga wuta tad'auke sannan kika fito ajiyar Zuciya tasauke dajin bai san bata cikin part d'in ba cikin 'karfin hali tace

" ina ruwanka da zamana cikin toilet ? naga babu wani amfani danike dashi agareka tun safiyar yau kake wani shareni toya kakeso nayi nalura bakason ina shiga cikin hurumin ka dan haka daga yau nadena shiga kuma kuma kasani nakusa barma masarautar ku sabida aykin daya had'amu yakusa rabamu ayanzu mungano wa'inda suka kashe Nabila da 'batar da yaranka dan haka kashirya sakina daga yau natashi daga 'kar'kashin ikonka bakada hurumin takurani kuma auran yarjejeniya ya'kare daga yau "

Gefan shi tabi tabar bedroom d'in parlour takoma tazauna tana kuka mai tsuma zuciya dede lokacin wutar gidan tadawo cikin mamaki yaya Ibrahim yake maimaita " auran yarjejeniya kuma Muzaffar da Raihan to su Shureem kumafa kay a'a " part d'in yanufa kai tsaye

A'bangaran ummi kuwa fitowar yarta daga bedroom yayi dede da farkawarta cikin ihu tana ambaton Nabila kiyi ha'kuri dan Allah karki kasheni nayi Al'kawari zandawo miki da yaranki dandanan sauran 'yayan suka furfito idanunta arufe amma se bama Nabila ha'kuri takeyi tana fad'in yadda tasa aka sace Farooq da haidar dan danan parlour yacika a'bangaran su mami ma haka abin yake cikin tashin hankali maimartaba yami'ke dajin wannan labari sawa yayi aka tattarasu cikin parlour kaka yaransu da manyansu ganin babu Muzaffar yasa maimartaba ayka mu'azzam kiran su jin kiran yasa yaya Ibrahim barin maganar dake cikin shi har zuwa bayan amsa kiran maimartaba cikin bedroom Rayhana tashiga wannan zoban ta d'akko had'ida kayan sanyin dake jikin su Haidar lokacin data tsincesu jin maganar wannan aljanar tayi

" Rayhana lokacin barinki cikin masarautar nan beyiba domin akwa wani kullin nadaban bayan wannan sannan yin karatunki yanada matu'kar amfani dan haka karki sake kibari kibar gidan yanzu kisan abinda zaki fad'a idan kinje cikin taron sannan karki sake kice auran yarjejeniya kukayi keda Muzaffar ki kiyaye shiko Muzaffar fita yayi shida yaya Ibrahim yana jinjina karfin halin da Rayhana tasamu da 'kwarin gyuwar fad'amai magana sedata dakko yaran tagoya daya ta d'auki d'aya sannan tafita nishi kawai takeyi sabida duk sunyi bacci nauyinsu ya'karu

tana shiga Momy tayi saurin tashi ta amshi Sudees tana fad'in " mai makon kibarsu cikin bedroom tunda bacci sukeyi "Murmushin 'karfin hali Rayhana tayi tace " ina gudin karsutashi suyi kuka " jinjina kai Momy tayi tana sakin Murmushi gyran murya maimartaba yayi yayi addu'a sannan yafara dacewa

" wani tashin hankali yashigo cikin masarautar nan naganin fatarwar Nabila jiya mama tagani yau kuma su Hamdiyya har su 3 hakan yana nufin cewa Nabila tanason ayimata adalci to amma Allah yana ganin yadda muketa faman yin bincike akan gano wanda yayi kisan amma har yanzu shiru yaranma har yanzu ko gawarsu bamu samu damar ganiba to amma abin mamaki yadda wa'innan suketa wasu maganganu kamar sunada hannu wajan wannan lamarin ko gaskiya ne ko furgicine oho " cikin sauri Ummi tace

" furgicine kawai maimartaba fatalwa fa ? " cikin sauri suma su mami sukace haka Murmushi yaya Ibrahim yayi yami'ke yace

" Allah ya'karamaka lafiya inada magana sannan inaso kowa ya kalleni a matsayin jami'i na musamman ba Ibrahim ba sannan inaso kowa yasaurari wannan d'aukar " kunnawa yayi tuni maganganun su suka fito ras cikin tashin hankali Ummi tami'ke zata 'karyata Rayhana tami'ke tace

" Allah yataimakeka nima inaso abani dama nayi magana " jinjina kai maimartaba yayi kunna wani recorder tayi cikin wayarta lokacin da ummi da umma suke magana akan wannan box d'in sannan tace kowa ya kalli wannan zoban " cikin sauri Muzaffar yami'ke ya amsa yace " wannan ay zoban Nabila ne " Murmushi Rayhana tayi takwance ledar hannunta taciro kayan sanyin Farooq da haidar tace " ko akwai wanda zai iya gane wannan kayan mi'kewa momy da Aunty Sumayya sukayi sukace " tabbas wa'innan kayan Farooq da haidar ne nice nasamusu su aranar "

Jinjina kai Rayhana tayi tace " to inaso kowa yasani Sudees da Shureem sune Farooq da haidar idan har kuna tantama kuduba tabon dake jikinsu nice natsince su cikin wani daji dake 'kasar Cameroon kud'in da akasa cikin box d'in sune sukasa nasan 'kasarda yaran suke ciki hakan yasa nasha alwashin had'asu da iyayensu se Allah yabani sa'a nahad'u da Mahaifin su a Pakistan nakuma gane hakanne sabida tsananin kamarsu dakuma irin zoban dake hannun shi naga iri d'ayane dana cikin wannan box d'in tabbas ni 'ban ta'bayin aureba balle har nahaihu amma su Farooq sukasa nazama tamkar matar aure wadda ta haihu nabi hanyoyin dazansa ruwan jikina yakawo danna shayar dasu sabida Allah ya d'auramin 'kaunar Farooq da haidar nakuma samu nasarar haka dukda ina had'a musu da madara amma ina shayar dasu har yanzu nashigo cikin masarautar nan amatsayin 'kanwar Muzaffar amma nidashi kawai mukasan haka dan mugano wa'inda suka kashe Nabila amma babu ala'kar aure a tsakanina da yaya Muzaffar to Alhamdulilh tunda angane gaskiya zankoma 'kasarmu dukda banida kowa nacigaba da ri'ke marecina tabbas zanyi kewar yarana Farooq da haidar "

Kuka Rayhana tasaki cikin mamaki Muzaffar yake kallon Rayhana amma yakasa furta komi tashi Momy tayi tarungumo Rayhana tace " babu inda zaki Raihan kinadani dan haka bakida marayci kuma bazaki rasa su Farooq ba zan ri'ke'ki tamkar Zarha nizan aurar dake ga mijin dakika za'ba da kanki zanbaki rayuwa ingantacciya dan Allah Raihan ina ro'konki daki zauna gurin Momy ki dan Allah "

Ri'ke hannunta Rayhana tayi tace " kibar kukan Momy na ha'ki'ka ked'in uwace kuma nayi al'kawarin cigaba dazama dake amatsayin 'ya kuma mai biyayya agareki nagode da wannan kyautar yaya Muzaffar ina matu'kar godiya agareka sanadin ka nasamu uwa da uba harma da yayye musamman big brother na yaya Ibrahim "

Cikin farin ciki maimartaba yace

" tabbas kincika 'ya Raihan Allah yayi miki albarka mungode ma Allah daya nunamana munafukan cikin masarautar HAYAT kuma za'ayima kowa hukunci dede da lefinshi Ibrahim Muzaffar Mu'azzam da kai Muzanbil inaso a kawomin Nura duk inda yake asafiya gobe sukuma su Hamdiyya akaisu cikin kurkuku a ajesu kafin karbar hukuncin su dole naji cikakken bayani daga Nura naji mahaifiyar shice tasashi ko ra'ayin kan shine "

Kuka sosai sukeyi cikin kuka Hamdiyya tace " kayimin afuwa maimartaba tunda gasu Farooq d'innan babu abinda yasamesu " wani irin kallo maimartaba yayi mata ita kuwa Mami ri'ke 'kafar mijinta tayi wato Yusuf tace

" kana gani za'a kaini kurkuku wannan ay abin kunyane abban Nura " cikin fushi ya kalli kaka yace " haba mama kiyimai magana mana " murtuke fuska kaka tayi tace " lallema Yusuf wato nagoyi bayan zalunci ko kunaganin yadda aka furgitani wajan bincike to sune baza'a hukuntaba sabida sunfi kowa nikam ama fitarmin dasu daga parlour "

barin gurin kaka tayi shiko kawu idris cewa yayi '" tur da irin wannan halin kowa ya aykata to shima a aykata mai dan haka nima babu ruwana sosai samha da Arfat suke kuka ganin iyayen su cikin wannan halin itako arfat sake shiga tetayinta tayi d'aukar Sudees Momy tayi itakuma Rayhana tad'au'ki Shureem suka nufi part d'in Momyn tashi kowa yayi yabar parlour masu farinciki sunayi masu ba'kinciki sunayi har kowa yabar parlour amma shi Muzaffar yakasa tashi yarasa wane irin tunani zeyi

Ganin yarasa mafita yasa yami'ke yanufi part d'in Momy cikin mamaki Momy tace
Chapter 26 · 0% Book details