← Book details Hayatul Mahayat Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 38 OF 41

Sashe 38

Hayatul Mahayat Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

murmushi Aunty Sumayya tayi tace " hmmm inayi dukda nasan babu abinda amaryar zatafini wajan mijina har Momy sedatace nazo ayimana gyaran jikin nida waccan banzar Raihan d'in amma nace a'a sabida banason duk wani abinda zamuyi tarayya akanshi nida Raihan nayi matu'kar tsanarta musamman yadda Momy takeji da ita wallahi inataya Islam kishin muzaffar kinga yadda Momy tasa aka maida Raihan ? Hmmm abin ba'ayin magana wallahi kamar kisaceta kigudu sabida yadda tayi masifar kyau dama gata kamar aljana sekuma gashi tasha gyara shine nima nasa agyara Islam yadda zata gigita nata mijin "

Wayyo Allah cikina 🤣😂😜💃🏻 Aunty Sumayya itake gyara kishiyarta tofa kenan wannan babbar gudummawace tabama yaya Ibrahim 😳😜🙈

Daga Al'kalamin.....🖋

NPEEDY A AJI 🌸🦚🌸

Comments and shire please

Love u all sisters 🥰😘🌸 *HAYATUL MAHAYAT* 🌸
🦚🦚🦚🦚
🦚🦚
🦚
Story and written
By
NPEEDY A AJI

Dedicated to
My Fatima Zahra yar amana

🌸NOORUL HAYAT🌸 WRITERS ASSOCIATIONS

🌹Expressions and heed Searching Sweet story Novels writer🌹
>>>>>>>>>>>>>>>>>>>
We are together all fans🤝🏻🥰
KAFA'DI ALKHAIRI KO KAYI SHIRU 🤫

My Novels
1-NAYI RAYUWA DAKE
2-SANADIN ACCIDENT
2019
3-SAKAYYAR CUTA
4-RUFAFFIYAR ZUCIYA

HAYATUL MAHAYAT
typing......✍🏻
And
🙆🏻💘 Mugun sartse!!!!! 💘🙆🏻

Coming soon after hayatul mahayat in sha Allah
Bismillahir Rahamanir Rahim

🅿 59 & 60

Tofa ayaune ake shirin d'aurin auran Yaya Ibrahim da Islam itako Aunty Sumayya ba'kincikine fal cikin zuciyarta fitowa yaya Ibrahim yayi daga cikin bedroom sanye dafatar shadda tass wadda tasha aykin zare coffee color hannun shi ri'keda hula kalar aykin kayanshi had'ida takalmi kalar hular sumarnan tashi tasha gyara sefama kamshi takeyi

Kallon Aunty sumayya yashigayi waddake zaune a parlour tasha wanka cikin wani tsadadjen les mai matu'kar kyau sekamshi takeyi namusamman kallonta yaya Ibrahim yayi yasaki murmushi 'karasawa yayi hannunta yakamo yasumbaceshi yace

" Woow gaskiya kinyi kyau uwar gidana kamar bakeba kode nafasa auran ne ? " wani irin kallo Aunty sumayya tayi mai azafafe tace " hmmmm namiji kenan uban yaudara wato ma kode kafasane to wannan kai tashafa kasani banajin tsoran kishiya tazo wallahi nagaba yariga yayi gaba saura zata tadda dan bazata ta'ba samunka matsayin saurayiba kamar yadda nasameka "

Murmushi yaya Ibrahim yayi yarungumota yamanna mata kiss yasaki dariya yace " hakane uwar gida amma nayima amarya tanadi namusamman wanda banyi mikiba sabida kunyar auran fari kumafa sabo sabone wai Allah kidenamin wannan kallon karkisani canza wanka kinsan amatsa nike yau d'innan jikina da zuciyata sun matsu sukasance da amarya " jin haka yasa Aunty sumayya juyowa afusace zata rungumo shi dan 'bata wankan nashi dede lokacin muzaffar yashigo cikin wata irin shadda mai kalar sararin samaniya woow gaskiya yayi matu'kar kyau yafito ango sak ganin muzaffar yasa Aunty sumayya juyawa tabar parlour afusace

Girgiza kai muzaffar yayi yace " yaya yakamata mutafi lokaci yakusa 'kurewa murmushi yaya Ibrahim yayi sukafita a part d'in momy suka had'u dasu mu'azzam harma dasu yaya Ahmad shiko muzaffar idanu yasaka ko zaiga Rayhana amma babu alamunta cikin siyasa yace Momy su Farooq fa Zahra tabashi amsa da yanzu aka shigar dasu wajan momyn su suna rigima " saurin nufar hanyar bedroom d'in yayi tamke fuska momy tayi tace

" ina zaka maza kadawo kutafi lokaci yana tafiya dole muzaffar yajuyo suka fita Aunty Sumayya tana shiga cikin bedroom d'in ta tafad'a saman bed tasaki kuka sosai takejin ba'kinciki cikin zuciyarta wai ace yau itace za'ayima kishiya " lalle nayi mugun sakaci

Misalin 2:30 aka d'aura auran Yaya Ibrahim da Islam cikin farinciki su yaya Ibrahim sukadawo gida kai tsaye part d'in maimartaba suka nufa wanda shi yarigasu dawowa daga wajan d'aurin auran sosai yasakamusu albarka had'ida nasiha mai ratsa zuciya godiya sukayi sannan suka nufi part d'in momy

Itama nasihar tayi takuma saka albarka daganan suka nufi part d'in kaka suna shiga kowa yashiga rige rigen rungumeta tamke fuska kaka tayi had'ida dakatar dasu da hannu tace " kar wanda yasake yayi yun'kurin kasheni " zaro ido sukayi sudukansu sukace " kisa kuma kaka ? jinjina kai tayi tacigaba dacewa " wato kunanufin nabarku kuhayeni 'katte daku to idan ba kisaba maizakuyi ? "

Dariya suka saki suduka yaya Abubakar yace " haba kaka waiku tsoran mutuwa kukeyi duk irin dad'ewar dakukayi a duniya duka takawo mishi suka saki dariya cikin zolaya muzaffar yace " amma kaka waima shekaru nawa kikayi aduni......" fitowar Rayhana daga cikin bedroom d'in kaka yasa muzaffar kasa 'karasa maganar shi mi'kewa yayi itako cikin sauri takoma ciki dabida yadda taji zuciyarta ta'buga datasan suna parlour dabata fitaba

Tsawa kaka tadaka mishi tace " inakuma zaka " batare dajin kunyaba yace "wajan matata mana kaka " baijira maizataceba yayi gaba shima muzalbil tashi yayi yace nima natafi gurin tawa matar shima mu'azzam mi'kewa yayi ba'ki kaka tasake haka kowa yafita ciki haddasu yaya Ahmad kallon kaka yaya Ibrahim yayi kafin yayi magana kakatace kaima tashi kaje wajan taka matar kafin amaryar tazo " murmushi yaya Ibrahim yayi yami'ke yafita dariyar da zahra take kuntsewa tasaki kallon kaka tawatsa mata tace

" badariya zakiyiba neman mafita zakiyi kingade yadda kowa yakeji da matarshi hakama matan sukeji da majajen nasu Aliyu yakirani yakuma sanar dani komi amma bazan matsa miki akan kikoma gurinshiba amma yakamata kiyi abinda yadace dan baikamata kitazama hakaba ke muke saurare sannan musan hukuncin dazamu yanke "

Cikin sanyin jiki Zahra tami'ke tabar parlour muzaffar yanashiga cikin bedroom d'in ya hangi Rayhana saman bed d'in kaka tarufe fuskarta cikin sauri muzaffar ya'karasa gareta zama yayi kusada ita wata irin ajiyar zuciya muzaffar yasauke har Rayhana tana'iya jiyo sautin sauke ajiyar zuciyar shi hannunta yakama wani irin yarrrr yaji cikin jikinshi cikin sauri Rayhana tami'ke saurin mi'kewa shima yayi kafin yayi magana kaka tashigo cikin fad'a tace maza kafita uban rashin kunya idan kayi ha'kuri zuwa anjima kawoma ita za'ayi maza fitarmin daga d'aki "

Cikin jin kunya yasosa kanshi kallon Rayhana yakumayi yakashe mata ido yafita tun 6 Aunty sumayya tashiga cikin bedroom d'in ta anyi anyi tafito amma ta'ki bayan sallar magrif aka kawo Amarya part d'in momy aka kaita sannan aka kira Aunty Sumayya dan yimusu nasiha amma Aunty Sumayya ta'ki zuwa sede momy tace akai Amarya kawai zuwa gobe ta zaunar dasu

Aunty Sumayya tanaji akashigo da Amarya kasancewar part d'ayane zasu zauna sabida 'katon part ne mai d'auke da parlour 3 ko wanne akwai 3 bedroom aciki da kitchen se babban parlour wanda yazama yana tsakiya ankai Amarya kowa yawatse daga ita se 'kawarta guda d'aya itama shirin tafiya takeyi kallonta 'kawar tata tayi tasauke ajiyar zuciya tace

" gaskiya Islam kin more sosai wallahi Allah yabaki miji mai nagarta ga kyakkyawar nasaba ga kyawun hali ga kyau ga kud'i ance shikad'e ne wajan mahaifinshi gashi yarasu shiya yazama d'an gata sosai gaskiya Momy tacika uwa tagari kigafa 'yarta yake aure amma babuwani ba'kin ciki atare da ita tamkar ba sirikintaba "

Murmushi Islam tayi tace " 'kawata kenan ay Momy uwace gakowa inada tabbacin batad'auki yaya Ibrahim amatsayin sirikiba sede d'ah d'anma babban d'ah shiyasa banajin damuwa dan na auri mijin Aunty Sumayya dan nasan Momy bazata bari Aunty Sumayya taci zarafinaba " jinjina kai 'kawar tata tayi sukacigaba da hira

Cikin farinciki yaya Ibrahim yakamo hannun muzaffar yace " aboki zomuje karakani shiga d'akin Amarya " zaro ido muzaffar yayi yace " nikuma tawa Amaryar fa ? kaga yaya Ibrahim gasu yaya Ahmad can kaje sune yakamata suyimaka rakiya dan nima su mu'azzam ne zasuyimin rakiya kuma yan uku muma haka " daga haka muzaffar yanufi part d'in momy dan duk su muzalbil d'in sunacan

Tare dasu yaya Abubakar yaya Ibrahim yanufi part d'in shi sefaman tsiya sukeyime bangaran Aunty Sumayya sukafara shiga amma ko sallamarsu bata amsaba balle tadubesu sosai yaya Ahmad yafusata amma yaya Ibrahim yahanashi cewa komi zama yayi kan cushion d'in datake zaune yace " haba uwar gidana yakamata kiyi ha'kuri haka kidaure ki sassauto zuciyar zankawo Amarya yanzu tagaidaki " tashi Aunty Sumayya tayi cikin fushi tace

" bana bu'katar ganinta dan haka kartasake ta takomin 'bangarena " daga haka tajuya tanufi cikin bedroom d'in ta sosai yaya Abubakar yaji haushin abinda Aunty Sumayya tayi dafa yaya Ibrahim yayi yace " kayi ha'kuri yaya kabarta ay yazama dole taga Amarya muje nasan yanzu haka tanacan ita 'kad'e " ajiyar zuciya yaya Ibrahim yasauke yatashi suka nufi bangaran Amarya

Dan Allah kuyi ha'kuri dani abubuwan ne se sannu amma in sha Allah zanyi 'ko'karin dawo da typing kullum kamar da kafin zuwan saban book in sha Allah kude kutayani addu'a Allah ya'kara lafiya nagode sosai masoyana

Daga Al'kalamin....🖋

NPEEDY A AJI 🌸🦚🌸

Comments and shire please

Love u all sisters 🥰🤝🏻🌸 *HAYATUL MAHAYAT* 🌸
🦚🦚🦚🦚
🦚🦚
🦚
Story and written
By
NPEEDY A AJI

Dedicated to
My Fatima Zahra yar amana

🌸NOORUL HAYAT🌸 WRITERS ASSOCIATIONS

🌹Expressions and heed Searching Sweet story Novels writer🌹
>>>>>>>>>>>>>>>>>>>
We are together all fans🤝🏻🥰
KAFA'DI ALKHAIRI KO KAYI SHIRU 🤫

My Novels
1-NAYI RAYUWA DAKE
2-SANADIN ACCIDENT
2019
3-SAKAYYAR CUTA
4-RUFAFFIYAR ZUCIYA

HAYATUL MAHAYAT
typing......✍🏻
And
🙆🏻💘 Mugun sartse!!!!! 💘🙆🏻

Coming soon after hayatul mahayat in sha Allah
Bismillahir Rahamanir Rahim

🅿 61& 62

Aunty Sumayya najin fitarsu tafito parlour ganin leda aje wajan cushion yasata jin wani irin 'bacin rai harta d'auka zatabisu sekuma tatsaya afili tace " hmm wannan ledar daka aje tun asuba zankaima abunka har cikin bedroom d'in amarya dan nanunamaka amarya kebu'katar kaza da sauran abubuwan amma ba Sumayya ba badansu yaya Ahmad ba Allah dasenasa kagagara shiga d'akin Amaryar " 'kwafa tayi takoma tazauna
Chapter 38 · 0% Book details