← Book details Hayatul Mahayat Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 41

Sashe 4

Hayatul Mahayat Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

" Doctor kataimakeni inajin motsin daban ganemishiba cikin part d'in nan dan Allah kasa Muzaffar yazo yadubamin kafin kashigo nima kar'a kasheni kamar yadda aka kashe Nabila " cikin 'kid'ima yace

" kwantar da hankalin ki karki fita bari nakira shi " wani irin murmushi Arfat tasaki takashe wayar kiran wayar Mu'azzam yashiga cikin wayar Muzaffar adede lokacin da Muzaffar yakejin wata irin muguwar shi'awa tataso mishi bayan shan wannan ruwan da 30 minutes da'kyar yad'aga wayar Mu'azzam jin abinda yake fad'i yasashi saurin tashi yafita kai tsaye yanufi part d'in Mu'azzam d'in adede lokacin Samir d'an gidan Ummi wato Hamdiyya yazo wucewa tagurin ganin Muzaffar yashiga cikin part d'in Mu'azzam gashi bai dawowa yasashi yin mamaki ganin dakadiya a gabanshi yasashi saurin cewa kinga abinda nagani kuwa ? "

Jinjina kai tayi alamar eh zanshi tayi suka koma gefe suka la'be sunajiran fitowar Muzaffar

Yana shiga yashiga dudduba cikin parlour cikin furgici Arfat tafito daga bedroom gashin kanta duk a hargitse saurin kauda kan shi Muzaffar yayi cikin kuka tace

" please Yarima cikin bedroom d'ina wani yashiga "

Batare da wata shakkaba yashiga cikin bedroom d'in yana shiga Arfat tayi saurin shiga rufe 'kofar tayi tajefa key d'in bayan wardrobe d'in ta azafafe Muzaffar yajuyo yace

" maiye haka ? Arfat kiyi gaggawar bud'e 'kofar nan tunkafin nayi mugun wula'kan taki Ar......... " saurin juyawa yayi ganin tasa'bule rigar jikinta babu ko fant rumtse idanun shi Muzaffar yayi tuni yaji shi'awar shi tasake tashi Cikin wata irin Arfat tace

" haba Yarima tsayin shekaru nakasa bama Doctor kaina sabida kai nakasa saka son wani cikin zuciya ta se sonka dukda kun kasance masu tsananin kama amma ni komi naka yafi burgeni kazo gareni nabaka kaina kafin nabama d'an uwanka " cikin 'karfin hali Muzaffar yajuyo fuskar shi atamke yace

" keeee Arfat kishiga cikin hankalin ki ni bazan ta'bacin amanar d'an uwanaba bazan iya bu'katar wata maceba har abada tunda Nabila tatafi kibani hanya kona tureki "

Cikin sauri Arfat tayo kan shi Hogging d'in shi tayi taturashi saman bed cikin azama tarufamai baya saman shi tahaye sosai jikin Muzaffar yamutu kai bakinta tayi cikin nashi cikin azama yajuyar da'ita takoma 'kasan shi wani irin mari yakifamana yayunkura zai tashi tayi saurin yan zip d'in rigar jikin shi har 'kar she hannun ta tasa tasa'kalo wuyan shi yasake fad'awa kanta

Gashin kanta yakamo dakarfi cikin azaba tasaki 'kara 'kara rungumo shi tayi takai hannu ta'balle belt d'in wandan shi jin haka yasa Muzaffar kaimata wani irin wawan naushi afuska dan danan bakinta yafashe cikin jin zafi da gigita tasake kai hannu wajan marar shi tayi rashin sa'a tacake da'karfan belt d'in shi tuni jini yarafa ziba daga hannun batare dasanin Muzaffar ba jinin ya'bata mishi gaban farin wandan itako saman mararta har dede 'kasan inda matantakar ta take jin ana buga 'kofa yasa Arfat sakin kuka had'ida sake ri'keshi kam

Amatu'kar furgice Mu'azzam yaciro wani key daga aljihun shi yabud'e yana bud'ewa jakadiya dake bayan shi tayi saurin shiga shima shiga yayi cikin azama ganin Muzaffar d'ared'are saman Arfat yasa Mu'azzam saurin juyar dakanshi tuni yafarajin wani irin jiri yana d'ibar shi itako Jakadiya salati tasaki wani irin kuka Arfat tasake saki tana fad'in

" Allah ya'isa tsakanina dakai Muzaffar ka ketamin haddi se Allah yasakamin "

Cikin wata irin zuciya da mugun ba'kin ciki Muzaffar yashiga sauke mata wasu zafafan maruka cikin azama Mu'azzam yafizgo Muzaffar yashiga marinshi yana fad'in

" banyi tsammanin hakaba d'an uwana ashe zaka iya cin amanata ? "

Azafafe Muzaffar yaturashi yace

" dama zaka iya yarda zanci amanar ka Mu'azzam ? Wallahi koda babu mata aduniya Arfat bata isheni kalloba "

Yana gama fad'in haka yafita afusace kai tsaye part d'in shi yanufa shikuma Mu'azzam fita parlour yayi yanajin kanshi yana juyawa itama Jakadiya fita tayi kai tsaye tanufi part d'in maimartaba

_________________________

Cikin wani yanayi Mu'azzam yami'ke zuwa yayi yakulle 'kofar part d'in freezer yanufa ruwa mai sanyi yad'akko 'balle bakin robar yayi bai tsaya d'aukar cup ba yakafa kai seda yakusa sanye ruwan zuba sauran yayi saman kanshi koda zaiji sanyi cikin zuciyar shi jin yadda Arfat take kuka yasa Mu'azzam shiga cikin bedroom d'in hawa yayi saman bed d'in yajawota jikin shi yana lallashin ta wani irin yanayi yafaraji jiyayi hankalin shi yafara gushewa kafin wani lokaci baisan inda kanshi yakeba ashe ruwan dayasha Arfat tasaka wata mahaukaciya 'kwaya wadda zata gusar da hankalin Mu'azzam yakusanceta a wannan daran batare dasanin shiba tayadda dole Mu'azzam zeyarda Muzaffar yaketa mata haddi haka kuwa tafaru

Mu'azzam yakusanci Arfat a wannan daran batare dayasan ya aykata hakan ba dukda mugun zafi daciwon da Arfat keji haka tadaure

Cikin tashin hankali Sarki da Kilishi suka mi'ke sabida jin wannan mummunan labarin Sarki dakan shi yanufi part su Mu'azzam d'in amma akulle bugawa yafarayi cikin taushin murya Kilishi tace

" Allah yahuci zuciyar ka inaga kabari sezuwa safe kallonta yayi rai'bace yanufi part d'in Muzaffar yana shiga yasameshi zaune kan cushion idanun shi arufe wani irin mari Sarki yasauke mishi guda 3 ajere cikin matu'kar 'bacin rai yace

" wane irin abune ka aykata Muzaffar kana d'an musulmi kuma d'an babban gida yanzu idan wannan abin yafita ciki da wajan masarutar nan yazamuyi kenan Muzaffar sedanace kayi aure kace bazakayiba amma ga irin abunda ka aykata " Dad kai makayarda zan'iya aykata haka..... "

Mari Kilishi tasauke mishi wanda yasashi yin shiru dole idanunta cike da hawaye tab tace

" idan 'karya akemaka ina kasamu wannan jinin najiki wandanka Muzaffar kabamu mamaki matar d'an uwanka "

Kukane yaci'karfin Kilishi tayi saurin fitowa daga part d'in shima Sarki nufar hanyar fita yayi Dede lokacin mahaifiyar Arfat tashigo Cikin fad'a take fad'in

" wallahi bazan yarda da wannan cin zarafin ga 'yataba dole ayima Muzaffar hukunci agaban kowa "

waigowa Maimartaba yayi yace

" gobe tunda safe kasameni filin sukuwa dan amsar hukuncin daya dace dakai "

Fita suka a wannan daran babu wanda yarintsa cikin su kafin gari yawaye duk illahirin cikin masarutar babu Wanda baiji wannan lamarin ba zuwa safiya duk inda kagifta cikin masarutar zancan ketashi 'kasa 'kasa Kilishi dakanta tashiga ta gyara kayan Arfat tawanke bedsheet d'in dukdan rufe sirrin amma kas ita batasaniba zancan yagama garad'e gidan misalin 8 Muzaffar yashiga filin sukuwar kamar yadda Sarki yace iya iyalan sarki ne kawai cikin filin se 'kananshi da matansu itako Kilishi kasazuwa gurin tayi Sarki yabada umarnin ayima Muzaffar bulala 100 batare da hutawaba shida kanshi yacire rigar jikin shi

Wata irin murtukekiyar bulala aka shiga zuba mishi kwata kwata bayajin zafin bulalar cikin jikin shi se cikin zuciyar shi shiko Mu'azzam tuni yafara zubda haye abinda shi Muzaffar bai zubdaba shiko Muzanbil cikin sauri yabar gurin mamaki kowa yashigayi ganin yadda Mu'azzam yake kuka dukda irin cin amanar da'ake ganin Muzaffar yayi mishi shima barin gurin yayi cikin wani irin yanayi

Ana gamayima Muzaffar bulala yabar gurin cikin wata irin suyar zuciya yana shiga part d'in shi yashiga had'a kayan shi ko wanka baiyiba sabida ciwukan jikin shi dan duk anfasamai baya ta 'kofar baya yafita kai tsaye ticket yasiya babu jimawa jirgi yad'aga dashi zuwa Pakistan

Sosai kowa yashiga cikin ba'kin ciki amma masoyan su Muzaffar ma'kiya kam dariya suke da murna sun samu abin yayatawa

Wani irin sanyi Rayhana taji yana shigar jikin ta alamar sanyin asuba yagabato kukan Sudees da Sureem yasata saurin tashi afurgice jin wannan muryar datace ta d'auki yaran yasata saurarawa

Rayhana kufita daga cikin wannan bukkar sabida masu nemanki suna kusada gurin idan kin fita zakiga wani 'karamin rami kishiga mubar 'kasar dake zamu kaiki kusada 'kasar mahaifina wannan yaran daganan seki shiga neman ubansu

Daga Al'kalamin.......✍🏻

NPEEDY A AJI 🌸🦚🌸

Comments and shine please

Love u all sisters
[10/9, 9:31 PM] NPEEDY A AJI: 🌸 *HAYATUL MAHAYAT* 🌸
🦚🦚🦚🦚
🦚🦚
🦚
Story and written
By
NPEEDY A AJI

Dedicated to
My yar amana

🌸NOORUL HAYAT🌸 WRITERS ASSOCIATIONS

🌹Expressions and heed Searching Sweet story Novels writer🌹
>>>>>>>>>>>>>>>>>>>
We are together all fans🤝🏻🥰
KAFA'DI ALKHAIRI KO KAYI SHIRU 🤫

My Novels
1-NAYI RAYUWA DAKE
2-SANADIN ACCIDENT
2019
3-SAKAYYAR CUTA
4-RUFAFFIYAR ZUCIYA

HAYATUL MAHAYAT
typing......✍🏻

Bismillahir Rahamanir Rahim

🅿 7 & 8

Haka kuwa Rayhana tayi tana rufe idanunta kamar almara taji tace tabud'e idanun ta tana bud'ewa taganta gefan wani gida mai matu'kar kyau da tsari waige waige tashigayi jitayi ansake cewa

" kishiga cikin wannan gidan kuyi rayuwa keda Twins kafin isarki ga mahaifin su amma kifara yin sana'a abakin wata kasuwa dake d'an nan gabada wannan gidan tahakane zaku had'u dashi Rayhana aduk lokacin dakika isa cikin masarutar HAYAT toki 'boye wannan box d'in da zoban ciki da wannan yad'in da'aka d'aure wannan kud'in dashi sabida shi wannan zoban na mahaifiyar su Farooq ne hakama wannan yad'in wani yankine nakayan jikinta lokacin da'aka kashe ta zaiyi miki amfani amma anan gaba sosai idan kikabari aka ganshi anan kusa to zakishiga cikin masifar dazaki 'kasafita sabida duk wanda akaga wannan zoban da shi yad'in to babu shakka shine za'a ri'ke amatsayin mai laifi amma dole sekinyi ha'kuri sabida zaki fuskanci matsala sosai acikin masarutar HAYAT zaki shiga cikin masarutar bayan su Farooq sunyi wayo dan sauya kamanninsu dana yanzu

Sabida idan har akasan sune to babu shakka kashesu za'ayi kema ahad'a dake dan haka seki kiyaye "

Ajiyar zuciya Rayhana tasauke tace

" nagode sosai da irin taimakon da kikayimin amma yazanyi dasu wajan shayar dasu ? "

"Karki damu da wannan idan suna bu'katar abinci kibasu nonon ki kamar yadda kowace uwa takebama d'inta bazakiga fitar ruwan nono ba amma suzasujishi wannan kuma daga garemune Rayhana babu abinda zaisameki munyi hakanne sabida dasa tsananin soyayya irinta d'ah da uwa atsakaninki dasu karki sake kodawasa wani yasan bakece kika haifesuba aduk lokacin dazaki basu nono yazama kinsasu cikin mayafi kar wani yaga shi nonon naki kishiga akwai komi cikin wannan gidan bazakirasa wani abuba

Zakijini shiru nawani lokacin zankoma wajan mahaifiyar ki dan kulada ita kamar yadda mukayimiki al'kawari nabarki lafiya "

Cikin sauri Rayhana tace

" yaya maman tawa take dan Allah ? " jin shiru babu amsa yasata cewa " kintafi to Allah yakaiki lafiya kema Allah yakareki Allah katsare mahaifiyata daga sharrinka Abba "
Chapter 4 · 0% Book details