← Book details Hayatul Mahayat Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 41

Sashe 11

Hayatul Mahayat Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wata irin dariya suka saki su duka wambai yace " godiya nike Sarki gobe "

Tofa Allah ya kyauta wato cuta zataci cuta kenan

Koda Yusuf yasami kaka akan maganar itama 'kin amincewa tayi sabida haka akayima mijinta daga zuwa gurin magani sede aka dawomata da gawarshi duk yadda Yusuf yayi akan sata baki amma ta'ki a'karshema cewa tayi yatshi yabata guri dole yabar parlour nata Zuciya shi cike da d'inbin haushi

Hankali tashe muzanbil yasake kallon Samha yace

" ke wai har yanzu babu wata alama ko ciwon mara baki fara jiba ? " jinjina mishi kai tayi alamar eh iska yafesar daga bakin shi yace " yanzufa watan shi 4 kenan tun yana wata 2 nake fama dashi akan yazu'be amma har yanzu babu labari yaya zanyi kenan " tashi yayi yafita afusace bayanshi Samha tabi da kallo cikin Zuciyarta tace

" in sha Allah bazai fitaba sena Haife shi dukda bansan waye ne uban shiba amma nikam inason baby na "

A'bangaran Arfar kuwa yanzu cikinta yakai 5 months cikin kissa take shafa cikin gaban mu'azzam tazo tatsaya cikin raunanniyar murya tace

" haba doctor jifa cikina harya fito amma ace ankasa sanarda muzaffar maganar cikin dolefa shine ubanshi gaskiya bazan iya boye wannan sirrin ba dan haka nizan kirashi nasanar d......... "

Cikin tsawa mu'azzam yace " karkisake kafara idan kuma kikayi haka koda bayan yadawone wallahi sena nuna miki irin mushin mu'azzam "

Tashi yayi yabata guri rai 'bace itama tashiga cikin bedroom

Tsawa kaka tadakama Zarah tace " zaki sanye wannan maganin kosena 'bata miki rai ciki wata 8 amma bakyason San magani se idan kun haifi d'anku kununa mana iyayi akan shin babu ko kunya maza ki shanye shi tass "

Dole zahra tashanye maganin badan ranta yasoba cikin tsananin damuwa kilishi tace

" haba Ahmad har yanzu ace ankasa samo wani cigaba akan rashin lafiyar mahaifinku innanillahi wa'inna ilaihirraju'uuun wannan wane irin ciwone da babu sau'ki kullum se gaba ? yakeyi ya Allah kakawo mana sau'ki cikin wannan masifar "

Amin Ahmad yace yami'ke yafita jiki babu 'karfi

Pakistan

Cikin rashin jin dad'in kwanciyar muzaffar yatashi zaune afili yace

" anya kuwa babu wata matsala dake faruwa a gida kuwa ? tsayin lokuta Zuciya ta takasa natsuwa gaskiya bazan iya bari senan da 1 month nakoma gidaba dukda babu shi'awar gidan cikin raina amma dole naje idan har lafiya to tabbas mahaifina yayi fushi dani tsayin lokaci banga kiranshiba idan nakirakuma baya shiga gashi su yaya Ahmad suna tabbatar min da kowa lafiya amma gaskiya nakasa gamsuwa in sha Allah cikin satin nan zan koma BIHAR zansa wani yamaye gurbin aykina nasan manyana zasu yarda dan 1 month tunda nayi har 5 months nasan bazan samu matsalaba "

Koma yayi ya kwanta addu'a yadingayi cikin ikon Allah bacci yayi gaba dashi babu jimawa dayin baccin shi yafarayin mafarkin Nabila amma wannan cikin wata siga ba wadda yasaba ganiba

Murmushi takeyimai cikin kyawun siffa tace

" Sojana ha'kika ina cikin farinciki wanda bazan iya misaltashiba please kamaye gurbina dawata idan har kanason farin cikina Sojana tahakane zaka samu nasarar gano wa'inda sukayi sanadin rabamu please kafin kabar Pakistan kayi aure shine zai zama babbar nasara akan gane wa'inda suka rabani da niyarka bazan dauwama cikin farin cikiba har se kagane yadda akayi aka kasheni kuma kad'aukarmin fansa dan bazan yafeba sun rabani da Sojana sun rabani da yarana dan Allah my soja kayi aure kodan samun wannan nasarar dakuma samun wacce zata kulamin da Twins d'ina

Banajin farin ciki idan bana tare dake haka kuma bazanyi farinciba idan har ka kasa d'aukarmin fansa amma zanyi farin ciki idan kayi aure love so much my Soja ......... " tashi yayi afurgice yana kiran Nabilahhhhhhh

Jingina yayi da fuskar bed d'in shi yana sauke ajiyar Zuciya afili yace

" haba Nabila taya zaki sani yin aure bayan kinsan bazan iya kallon wata mace dasigar soba bazan iya ba ammafa nagamsu da kikace idan nayi aure zan gane wa'inda suka kasheki tabbas hakane sabida nasan zasu kumyin yun'kurin haka akan duk wacce zan sake aura hakane Nabila zanyi aurene kawai dan wannan dalilin badan inason hakanba amma bazan ta'ba kallon matar amatsayin mataba sede amatsayin wadda zatayimin ayki akan wannan binciken Nabila babusu farooq balle tayi dan kula dasu sede nayi dan cimma wancan burin nayi farin ciki dakikacemin kina cikin farin cikin my Nabila "

Kallon agogon bangon cikin bedroom d'in yayi cikin sauri yami'ke yana salati har 10 amma baikoyi sallah ba wannan wane iri baccine kodan nakwana 2 bansamun baccin ? sauka yayi daga bed d'in cikin sauri yashiga toilet alwala yayi yafito yagabatar da sallah sannan yakoma yayi wanka misalin 11:30 yagama shirin shi cikin kakin shi na Soja fita parlour yayi kamshin parlour yasashi lumshe idanun shi kan dining yanufa cikin sauri Rayhana tazo du'kawa tayi ta gaidashi beko amsaba se cewa dayayi

" ina yaran suke ? "
" Cikin ladabi tace suna cikin bedroom wasa sukeyi wasa ? gafa kukan su can inaji dallah jeki d'akkomin su barshi nizan zuba acincin da kaina shashanci kawai yarinya batasan darajar yaraba "

Cikin sauri yagama cin abinci bawani sosai yaciba sabida yatafi tunanin ida zai samu yarinyar dazatayi mai wannan aykin dan bawai zai zauna da ita bane dazaran yaci nasarar aykinshi zai saketa cikin parlour yadawo cikin murna yaran suka nufoshi rungumaisu yayi yace

" morning my Twice ina fatan lafiya kuka tashi ? " gwaranci suka shiga yimai dariya yasaki yace " inani ina jin wannan yaran naku sumbatar kumatun su yayi yan hannun su yayi yana musu tatata had zuwa kan custom shima zama yayi kallon Rayhana yashigayi takenan ya yanke shawarar itace zatayimai wannan aykin kiranta yayi cikin ladabi tazo seda yayi jim wata Zuciyar tana sake tabbatar mai zata iya wata Zuciyar kuma tana cewa wannan 'yar yarinyar saurin cewa yayi ay bazama zanyi da itaba nawani lokacine "

Tamke fuska yayi sosai yace

" kee zaki aureni ? " zaro ido Rayhana tayi tanajin wata irin fad'uwar gaba tsaki yaja yace

" Ke dalla zan aurekine sabida kiyimin wani ayki badan ina sonkiba dazaran kingama yimin aykin zan sakeki zamu koma masarautar mu kuma dole kafin mukoma yazama na aureki sabida wannan dalilin zan baki era million 30 nasan bazaki iya barin a'innan kud'ad'an ba sannan kinga zaki shiga cikin masarautar mu kina mai 'yanci kuma bayan kingamayimin wannan aykin zan baki damar tafita duk inda kikaga dama afad'in duniya sannan inaso idan muka koma gida duk wanda yatambayeki waye uban yaran kice nine nikuma zan tabbatar makowa ked'in matatace tunda dad'ewa sauran bayanin zanyi miki bayan nadawo kiyi shawara da Zuciyar ki koki shiga cikin masarautar HAYAT kiname cikakken 'yanci koki shiga kina baiwa tahar abada shigada yaran nan kinsan idan sukaga tafiyana kuka zasuyi "

Cikin sanyin jikin Rayhana tad'aukesu zuwa cikin bedroom amma dukda haka seda sukasaka ihu saurin fita yayi sabida yadda yakejin kikan yaran har cikin ranshi yarasa maiyasa hakan cikin matu'kar damuwa Rayhana tace

" tabbas dana shiga ina baiwa gara nashiga ina mai 'yanci nasamu girmamawa wajan wasu amma nasan zansha wahala wajan Muzaffar ayanzuma yana'kare balle ina matsayin matar shi matarma dan wani ayki badan cikakkiyar mata ba towaima wane irin aykine wannan ? Allah kabani ikon zurewa zanyi komi wuyar shi in sha Allah amma dan Allah dakuma su Shureem badan kud'iba dan bazan iya amsar koda neraba daga hannun ka dan wani abuba Allah katsaremin mahaifiyata kasa watarana mugana "

Cikin sigar lallashin yaudara Alhaji Tanimu yace

" haba Fatima yakamata kisancewa nayi nadama nabar wannan muguwar har'kallar kiyimin murna dan Allah kicema Rayhana tadawo ina matu'kar kewarta nashirya bata kulawa irinta uba wadda nakasa bata awancan lokacin dan Allah Fatima kiceceni "

Tashi tayi afusace tace " wallahi Alhaji se Allah yayima sakayya akan cutar dakayi mana kayi sanad'in rabani da 'yata 'kwaya 1 ni bansan inda Rayhana takeba kuma koda nasani wallahi bazan fad'i makaba dan ni banyarda katuba ba "

Shigewa kitchen tayi tabar shi yana binta dawani irin kallo cikin Zuciyar shi yace

habawa wallahi sena baki mamaki Fatima duk wannan lalla'bawar inayimiki itane sabida cimma burina dazaran nasamu bolama tafiki daraja agurina kuma nasha alwashin se gunkiya tasha jin Rayhana "

Daga Al'kalamin.......🖊

NPEEDY A AJI 🌸🦚🌸

Comments and shire please

Love u all sisters 😘🥰
🌸 *HAYATUL MAHAYAT* 🌸
🦚🦚🦚🦚
🦚🦚
🦚
Story and written
By
NPEEDY A AJI

Dedicated to
My yar amana

🌸NOORUL HAYAT🌸 WRITERS ASSOCIATIONS

🌹Expressions and heed Searching Sweet story Novels writer🌹
>>>>>>>>>>>>>>>>>>>
We are together all fans🤝🏻🥰
KAFA'DI ALKHAIRI KO KAYI SHIRU 🤫

My Novels
1-NAYI RAYUWA DAKE
2-SANADIN ACCIDENT
2019
3-SAKAYYAR CUTA
4-RUFAFFIYAR ZUCIYA

HAYATUL MAHAYAT
typing......✍🏻

Bismillahir Rahamanir Rahim

🅿 19 & 20

Kafin muzaffar yadawo Rayhana tagama komi wajan aykinta zaune take a parlour tana kallon wani fim su Sudees nagefanta sunyi lamo tamkar kallon sukeyi da sallama yashigo wata irin fad'uwar gaba Raihana taji wadda tasa har seda tadafe kirjinta yara sunajin sallamar shi sukayi saurin tashi suna d'aga hannu zuwa yayi yad'aukesu cikin sanyin murya Rayhana tace

" Barka da dawowa "

Bai kalletaba bai kuma amsaba yashiga da yara cikin bedroom zaunar dasu yayi yabasu kayan wasa dan kar suje wajan 'banna shikuma yashiga wanka yad'an d'auki lokaci sannan yafito ganin yafito yasa yaran nufar gurin shi da 'kyar sukabari yashirya ri'ke yafito tare dasu suna takawa suna dari cushion d'in datake zaune yakaisu yad'aurasu yawuce dining

Cikin sauri Rayhana tami'ke taje tazubamai abincin juyowa tayi zatabar gurin yace

" wace shawara kika yanke ? "

Cikin fad'uwar gaba tace " na amince amma bana bu'katar kud'inka dan bansan yadda zanyi dasuba idan na amsa zanyima dan Allah "

Saurin barin gurin tayi shuko aje spoon d'in yayi yabita da kallo yana nazarinta zuwa can yacigaba dacin abincin shi bayan yagama yad'aga waya yakira wani malami akan yadda d'aurin auran zai kasance washe gari misalin 12 Muzaffar yafito cikin shigar manyan kaya 'kwalama Rayhana kira yashigayi cikin sairi tafito itama shirye take cikin wata atamfa mai matukar kyau da tsada sosai d'inkin yayi mata kyau tamke fuska yayi yace
Chapter 11 · 0% Book details