← Book details Hayatul Mahayat Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 41

Sashe 18

Hayatul Mahayat Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Turata yayi saura kad'an tafad'i tabaya wucewar shi yayi cikin sanyin jiki Arfat tajuyo idanunta sunciga tab da hawaye ganin Mu'azzam agabanta yasata zaro ido Murmushin takaici Mu'azzam yayi yace

Alhamdulillah dama Zuciyata takasa amincewa d'an uwana zai aykatamin haka yau gashi naji aynahin gaskiya da kunnuwana tabbas Muzaffar baiyi 'karyaba Arfat ina tsananin sonki amma ayanzu natsaneki bazanyi saurin sakinkiba yanzu sena d'an d'ana miki irin ba'kin ciki da damuwar dakika sani kikasa d'an uwana aciki sannan kiyi gaggawar sanar dani wannan cikin najikinki nawaye Arfat tabbas kin cutar dani nami'ka miki daukkan soyayyya ta ke kuma kinci amanata cin amanarma hadda cikin shege dukdan kulla makirci to wallahi bazan ta'ba yarda da wannan cikinba sanin kan kine kinsan ban ta'ba kusantarkiba na yarda dashine sabida ina zaton na d'an uwanane to yau naji tabbacin bashida ala'ka dashi kamar yadda banida shi "

Ya'karashe maganar cikin rawar murya yajuya saurin ri'ke rigarshi Arfat tayi tace

" Doctor wallahi wannan cikin nakane bashida wani uba se kai ka saura r......... "

Juyowa yayi afusace yasauke mata mari idanunta cike da hawaye tad'ago ta kalleshi ganin hawaye saman fuskarshi gawani irin red da idanunshi sukayi sabida tsananin 'bacin rai saurin rumtse idanunta tayi afili tace

" Doctor yau kaine nike ganin hawaye saman fuskar ka ? Nashiga uku ni Arfat "

Barin gurin Mu'azzam yayi cikin sauri itako dur 'kushewa tayi saman gyuwoyinta Muzaffar yana shiga cikin fada maimartaba yafad'a Murmushin shi su wajiri kuwa wata irin fad'uwar gaba sukaji kasancewar kayu Yusuf baya gurin yasa waimbai jin kamar yasaki fitsari gaisuwa Muzaffar yakai gurun mahaifin shi sannan yazauna gaisheshi aka shigayi saurin dakatar dasu yayi fuskantar mahaifin shi yayi yace

" Allah ya'karamaka lafiya mahaifina nazomaka da wata magana amma batana nufin shiga cikin hukuncin kabane inaso kabani damar tuhumar wancan azzalumin mutumin dasuke kirada malami dan nalura akwai lauje cikin nad'in akan zuwanshi wajan yima magani "

Jin jina kai maimartaba yayi yasauke ajiyar Zuciya yace

" karka damu Yarima Muzaffar zanbaka damar haka amma kabari zuwa gobe idan munyi magana da hajiya kaji "

Jin jina kai Muzaffar yayi yami'ke sallama yayima mai martaba yafito daga fada dafe setin zuciyar shi waziri yayi dan ji yake kamar zata fito sabida tsananin bugawa datakeyi Part d'in Momy Muzaffar yanufa

Cikin sanyin jiki Muzanbil yashiga cikin parlour zaune yasamu Samha tanashan fruit sallamar shi kawai ta amsa tacigaba dashan fruit d'inta kallonta yayi yai saurin kauda kanshi sabida irin shigar datake jikinta ji yayi tsigar jikinshi tatashi cikin bedroom d'in shi yanufa cikin zuciyar shi yace

" lallema yarinyar nan wato yau ko bag d'in bazata amsaba wanka yayi yashirya yafito dining yanufa zama yayi yanajiran tazo tazubamai amma shiru shikuma girman kai yahana yayi mata magana 'kwafa yayi yazuba abincin Spoon d'aya yayi yai saurin furzar da abincin yami'ke afusace yanufi gurinta cikin fad'a yace

" waine irin abincine wannan ? Sekace za'abama dabba " mi'kewa Samha tayi tace " daga cikin gida yake wanda hadimai sukayine dama bani yadace nadingayin abinciba kaima Kasan haka inayimakane sabida kyautatawa to nalura baka bu'katar haka shine nabari idan katashi bu'katar haka sekayimin magana idan naga zan iya " tana 'karashe fad'ar haka tanufi hanyar fita daga parlour cikin mamaki Muzanbil yabita dakallo dan yakasacewa komi

Fuska tamke Muzaffar yazauna saman cushion d'in dake kusada Momy gaidata yayi ko kallon inda Aunty Sumayya take baiyiba itama shigowarta kenan yanzu tashi Rayhana tayi tanufi freezer lemon ta d'akko had'ida yanka nau'ikan fruit acikin fulet tanufo gurin Muzaffar ganin haka yasa Momy tashi barin part d'in tayi tanufi part d'in kaka dede lokacin islam tashigo gurin Aunty Sumayya tanufa

Zama Rayhana tayi kusada Muzaffar d'aukar yankan watermelon tayi tanufi bakinshi dashi tagefan idanunshi ya kalli Aunty Sumayya ganin shi take kallo yasa shi bud'e bakin tasame cikin wata irin murya Rayhana tace

" woow Sojana kayi kyau sosai dole nasiya wannan wankan " wata irin fad'uwar gaba Muzaffar yaji cikin zuciyar shi yace kajimin yar duniyar yarinya tayaya tasan wannan kalmar hmmmm senaci uban Zarah nasan itace zata sanar mata " saurin 'ka'kalo Murmushi yayi tunawa dayayi su Aunty Sumayya suna gurin yace

" haba wane biya zakiyi bacin danke nayi kemafa kinyin kyau sosai shiyasa nasake biyoki nan dan nasake ganinki " Murmushi Rayhana tayi tasake samai fruit abaki abin watermelon d'in yazubar mai ajiki tayi saurin yun 'kurawa zata goge mishi akayi rashin sa'a tafad'a saman jikin shi saurin rungumoshi tayi sabida jidatayi zata fad'i d'ankwalin dake kanta yazame kamshin irin mayamayan gyaran kan Nabila yadaki hancinshi ga kamshin turaranta wani irin tashin hankali Muzaffar yaji saurin cije lip's d'inshi yayi cikin zuciyar shi yace

" wannan yarinyarfa idan nayi wasa kasheni zatayi amma senayi mugun sata tashiga cikin hankalinta tuni idanunshi suka canza launi itako sake 'kan'kameshi tayi tsakaninta da Allah ita tsoro yasatayin hakan badawani daliliba afusace Islam tami'ke tafita daga part d'in itako Aunty Sumayya zuciya tagama kasheta

Kuyi ha'kura najina shiru jiya batare dana sanar mukuba wani uziri yatsareni ina yinku fans ana mugun tare ina godiya da irin 'kaunar dakuke nunamin Allah yabar zumunci 👌🏻😘

Daga Al'kalamin....🖊

NPEEDY A AJI 🌸🦚🌸

Comments and share please

Love u all sisters 🥰🌸👍🌸 *HAYATUL MAHAYAT* 🌸
🦚🦚🦚🦚
🦚🦚
🦚
Story and written
By
NPEEDY A AJI

Dedicated to
My Fatima Zahra yar amana

🌸NOORUL HAYAT🌸 WRITERS ASSOCIATIONS

🌹Expressions and heed Searching Sweet story Novels writer🌹
>>>>>>>>>>>>>>>>>>>
We are together all fans🤝🏻🥰
KAFA'DI ALKHAIRI KO KAYI SHIRU 🤫

My Novels
1-NAYI RAYUWA DAKE
2-SANADIN ACCIDENT
2019
3-SAKAYYAR CUTA
4-RUFAFFIYAR ZUCIYA

HAYATUL MAHAYAT
typing......✍🏻

Bismillahir Rahamanir Rahim

Jinjina da d'inbin godiya gareku fans tabbas naji 'korafinku akan na'kara yawan typing to kunason typing amma bakwason yin comment iyakar ku thanks eh ha'kika inason godiyar dakuma addu'ar ku amma yin Comment yana sahun gaba wajan zummar yin typing sabida tananne zansan mai kuka d'auki sa'kon nawa to idan kunason na'kara yawan typing nadinga ganin ruwan Comment da muhawara akan Novel d'in 👌🏻

Sannan dan Allah masu bina ta pc akan natura musu daga farko dan Allah kudinga tambaya a group sabida abin yanayimin yawa please 👏🏻 Ana tare all sisters 🤝🏻😘

🅿 31 & 32

Mi'kewa tayi rai 'bace tace

" gaskiya Muzaffar kabani kunya wannan yar 'karamar yarinyar kakeyima irin wannan hmmm "

Fita tayi afusace tana fita Muzaffar yasauke wata irin ajiyar Zuciya rai 'bace yace " se yaushe zaki saukamin daga jiki ? " fuskar shi tanuna 'bacin rai amma muryarshi takasa fita da karfi kamar yadda Rayhana tazata jiki a sanyaye tami'ke saurin fita daga part d'in tayi sabida tsoran abinda zai biyo baya kai tsaye part d'insu tanufa su Sudees suna gurin Momy a can wajan kaka

Kwanciya Muzaffar yayi kan cushion d'in jikin shi duk babu 'karfi wani irin takaici yakeji cikin zuciyar shi yace
" wato ni wannan yarinyar zata nunawa futsara kodayake tasan waye namiji tundaga shedanan Sudees da Shureem tun tana yar ficiciyarta toni bazan d'auki wannan fitsararba zanyi maganinta "

Itako Rayhana tana shiga tayi saurin d'aukar wannan box d'in cire zoban ciki tayi ta'adanashi sannan tad'auki wata abaya tasaka tafita tanayi tana waige cikin tsoro da fargaba tashiga cikin part d'in saurin sauke ajiyar Zuciya tayi ganin babu kowa cikin parlour rumtse idanunta tayi tanufi cikin bedroom d'in dake kallon hanyar waje wani irin bugawa zuciyarta keyi tana shiga tabud'e idanunta jin 'karar saukar ruwa cikin toilet yasata dafe 'kirji saurin aje box d'in tayi kan bed tajuya tafita cikin sauri

Part d'insu takoma tana shiga tanufi freezer robar ruwa tad'akko ko tsayawa neman cup batayiba tabud'e takafa kai seda tasha yakai rabi sannan ta'aje tashiga cikin bedroom kullewa tayi sannan tazauna kan bed tana sauke ajiyar Zuciya duk tagama furgicewa tsayin lokaci sannan tami'ke tanufi toilet

Ummi nafitowa daga toilet idanunta suka sauka kan wannan box d'in cikin tashin hankali ta'karasa wajan bud'e box d'in tayi zaro ido tayi ganin kud'in amma babu zoban saurin rufewa tayi tami'ke fita parlour tayi hadimai tashiga 'kwalama kira cikin tsoro suka shigo zubewa sukayi suna kwasar gaisuwa tsawa tadaka musu tace

" waye yashigo cikin part d'in nan kuma har cikin bedroom d'ina ? " cikin tsoro suke sanar da ita babu kowa mari tawatsama takusa da ita tasake cewa " kamarya bakuga kowaba shashanci kenan lalle idan kuwa hakane bakuda amfani kuma wallahi kuyi gaggawar nemomin wanda yashigo yanzu ko nayi muku hukunci mafi girma "

Juyawa tayi takoma cikin bedroom ko Shiryawa takasayi sabida tashin hankali afusace tami'ke tasa kaya cikin tashin hankali take fad'in

" tabbas akwai wanda yasan komi akan 'batan Twins d'in Muzaffar gashi ni za'a farasawa cikin matsala bayan bani 'kad'ai na aykata hakan ba ana ganin wannan box d'in agurina za'a zata har kisan Nabila inadasa hannu aciki dana shiga uku dole nasan abinyi kuma dole nanemi wadda yakawo wannan box d'in "

Cikin sanyin jiki Muzaffar yafito daga part d'in Momy cikin mamaki yake hangen harabar ajiye motoci yadda manyan motoci keshigowa cikin sauri aka bud'e Motar dake tsakiya fuska naga Muzaffar yasaki had'ida yin Murmushi yanufi gurin dogarawa suka shiga kirari Muzaffar yana isa yarungume shi yana fad'in

" oyoyo yaya Ibrahim se yanzu kake dawowa agaskiya nayi fushi " Murmushi Yaya Ibrahim yayi had'ida kama kunnanshi yace " ayi ha'kuri aboki " bata rai Muzaffar yayi yace " haba yaya Ibrahim nacefa kadena cemin aboki koda baka auri Aunty Sumayya ba aykai babban yayane " sakeyin Murmushi yaya Ibrahim yace " ammafa lokacin dakake yaro konace yaya sekace a'a aboki dan haka wannan kalmar bazata mutu ba "

" kayi maza kasanar da 'kanwata Nabila nadawo kaga wannan bag d'in duk tsarabar tace hadda wani saban turare kasan aduk lokacin dana dawo take canja saban turare gakuma tsarabar Twins gaskiya naso nazo wajan hidimar sunan su ayki yatsareni Allah yasa 'kanwata batayi fushi daniba ? " ganin yadda fuskar Muzaffar tacanza yasa yaya Ibrahim yin shiru amma cikin zuciyar shi cewa yayi Allah yasade lafiya cewa yayi sunufi part d'in maimartaba dan shi yakeson fara gani kafin kowa

Suna isa maimartaba yafad'ad'a Murmushi shi rungume yaya Ibrahim yayi yace " masha Allah yau ga d'ana yadawo zama yaya Ibrahim yayi sukad'an ta'ba hira sannan suka mi'ke zuwa part d'in Momy
Chapter 18 · 0% Book details