← Book details Hayatul Mahayat Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 41

Sashe 24

Hayatul Mahayat Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

wata irin tsawa maimartaba yadakama Aunty Sumayya " kinci gidanku ja'irar banza kawai idan mahaifiyarki kice zakiyi dariya ? to kar in sakeji kowa yawatse "

barin part d'in sukayi kowa yana kunshe dariya banda mom da mamy suda suka fara furgita tunda sunga box

cikin tashin hankali waziri yace

" wambai wallahi nifa nafara tsokana da wannan lamari karfa asirinmu yatonu mushiga uku? "

ajiyar Zuciya wambai yasauke yace

" hmmmm ayko idan bamuyi dagaske ba to wallahi gamucan cikin kurkuku dalla idan kurkuku ne ay dasu'ki idan ba'afille kanmuba "

saurin shfa kanshi wambai yayi

" to yanzu waziri maiye abunyi ? abinyi d'aya muzauna munemo mafita kawai "
Shigowa muzau Muzaffar yayi cikin parlour kaka yace

" ina kakar ? kice yau my Nabila takawo miki ziyara ? to yaushe zatadawo kutafi ? "

wani irin kallo maimartaba yayi mai yai shiru tashi zaune kaka tayi tace

" idan tadwo da kai zata tafi dama kai ne masoyin ta Murmushi Muzaffar yayi yace ashe har yanzu baki 'kaunar my Nabila to Nabila idan kina kusa kinji bayanin kaka "

" wayace kara jamin masifa wallahi ina matu'kar son ki mai Nabila haka sunan yakeko mugun soja ? to my Nabila kinji kaka tana zagar miki miji yaushe zakizo kutafi " saurin tashi zaune kaka tayi tashiga ro'kon Muzaffar 😂🤣

afusace maimartaba yami'ke yakora Muzaffar waje

cikin tashin hankali Ummi takalli mamy tace

" gaskiya fa akwai matsala idan har dagaske fatawar Mama tagani to babu shakka mun shiga uku gara musan abinyi tun wuri kingafa har cikin bedroom aka kaimin wannan ba'kin box d'in dankam ni ba'kine agurina tunda zejamin masifar "

ajiyar zuciya mamy tayi tace " tabbas muna cikin matsala gagaruma "

Cameroon

Aliyu kwance akan bed amma yakasayin bacci tunanin yadda zai billoma wannan al'amarin yakeyi amma yakasa duk tunanin shi yatsaya cak har gari yawaye amma yakasa runtsawa sannan yakasa iya dena kuka

cikin mamaki mama tashiga cikin bedroom d'in da Aliyu yake zama tayi tace

" haidar lafiya har yanzu baka fito kayi breakfast ba ? "

Murmushin 'karfin hali Aliyu yayi yace

" yanzu zan fito mama kwance nine ina tunanin Zarha ta " Murmushi mama tayi tace " to kade fito kayi breakfast sekacigaba dayi "

to gashinan fans nafanshe najiya dana shekaran jiya 👌🏻😊🤝🏻

daga Al'kalamin....🖊

NPEEDY A AJI 🌸🦚🌸

Comments And shine please

love u all sisters 🥰🌹🌸 *HAYATUL MAHAYAT* 🌸
🦚🦚🦚🦚
🦚🦚
🦚
Story and written
By
NPEEDY A AJI

Dedicated to
My Fatima Zahra yar amana

🌸NOORUL HAYAT🌸 WRITERS ASSOCIATIONS

🌹Expressions and heed Searching Sweet story Novels writer🌹
>>>>>>>>>>>>>>>>>>>
We are together all fans🤝🏻🥰
KAFA'DI ALKHAIRI KO KAYI SHIRU 🤫

My Novels
1-NAYI RAYUWA DAKE
2-SANADIN ACCIDENT
2019
3-SAKAYYAR CUTA
4-RUFAFFIYAR ZUCIYA

HAYATUL MAHAYAT
typing......✍🏻

Bismillahir Rahamanir Rahim

Assalama alaikum all fans ykk ina godiya agareku sosai Allah yabar zumunci kuyi hakuri naji sa'konnin ku kuma wasu dayawanku sun kirani akan rashin yin typing nagode amma ba'a son raina na'kiyiba har yanzu wutar bata zaunaba idan har kukaga banyi typing ba to akan dole ne nagode da nuna kulawar ku gareni ana mugun tare 🤝🏻😘

🅿 37 & 38

Cikin rashin kuzari Aliyu yafito zama yayi yafarayin break d'in badan yanajin dad'in abincin ba sedan kar mama tayi tunanin yanada wata damuwa

Babu jimawa dazaman shi Alhaji Tanimu yafito kallon inda Aliyu yake yayi yace

" ya gajiyar tafiya ? " Murmushin 'karfin hali Aliyu yayi yace " babu gajiya " jinjina kai yayi yasakai yafita cikin ba'kin ciki Aliyu yami'ke komawa cikin bedroom yayi wanka yashiga daniyyar fita cikin garin

BIHAR
komawa Muzaffar yayi part d'in su shiga cikin bedroom d'in shi yayi wata irin ajiyar Zuciya yasauke ganin Rayhana kwance itada yara ga duk kan alamu tad'ad'e dayin bacci wasu irin kayan bacci ne jikinta duk sun bayyana surar jikinta idanu yazubamata yana kallon surar jikinta ahankali yad'aga lab'ban shi yace

" komi nata yayi surar jikinta abin jan hankali tamkar ba 'karamar yarinya ba tabbas dabaki kasance yarinya 'karamaba dana....... "

Saurin rufe bakin shi yayi yanufi toilet wanka yayi yafito yayi shirin bacci kwanciya yayi raya suna tsa'kiyar su idanunshi yazuba mata yana kallon fuskar ta jin iskar tasowar hadari yasa Muzaffar tashi sauke labulayen yashigayi wata irin wal'kiya akayi dede lokacin Rayhana tabud'e idanunta saurin rumtse su tayi sabida ganin wannan wal'kiyar sosai ruwa yatsuge tamkar da bakin 'kwarya gyarama yara kwanciya yayi yaja musu blanket har ita Rayhana baisan idanunta biyu ba hannu yasa ya gyara mata gashin daya sakkon saman fuskarta tsayawa yayi yana 'karemata kallo jiyayi kamar karya d'auke idanunshi akanta

Komawa yayi ya kwanta amma idanunshi na kanta yana kallon kyakkyawar fuskar ta dede lokacin akayi wata irin tsawa afurgice Rayhana tatashi zaune 'kan'kame jikinta tayi shiko Muzaffar lumshe idanunshi yayi kamar mai bacci amma yana kallon ta

Wata tsawar akasakeyi tuni jikinta yad'auki rawa ware idanunshi Muzaffar yayi yana kallon yadda 'kirjinta yakeyi sama yana 'kasa tashi yayi zaune yace

" meyene? " ajiyar zuciya tasauke tace " tsoro nikeji " d'an tamke fuska yayi yace " wane irin tsoro? bayan gani " wata tsawar aka sake saki afurgice Rayhana tajuya tama'kalema banga kallon bayanta yayi cikin dakewar murya yace " taso kidawo nan " tamkar dama jira tajeyi sauka tayi daga bed d'in gyarama yara kwanciya yayi ganin anyi wata wal'kiyar yasata saurin hayewa saman bed d'in cusa kanta tayi cikin 'kirjin shi ta rungumoshi sosai

Sake rungumota yayi sosai yanaji wani irin yanayi yana shigar shi bacci yayi gabada Rayhana amma shikam Muzaffar yakasa runtsawa ahaka har aka kira salla ahankali Rayhana take bud'e idanunta saurin rufe idanun shi Muzaffar yayi zame jikinta tayi tatashi tazauna ahankali takai bakinta dede kunnanshi tahuramai iska ahankali wani irin yaeerr Muzaffar yaji hannu yasa yajawota jikin shi tafad'o kallon ta yayi yatamke fuska yace

" wai yaushe nazama abokin wasanki ? " saurin girgiza kai tayi saka idan shi yayi cikin nata saurin rumtse idanunta tayi sabida yadda taga idanunshi sunyi 'ko'karin janye jikinta tayi daga nashi sake matseta yayi cikin 'kirjin shi kukan Shureem yasashi sakinta

Komawa tayi ta kwanta kusada Shureem tana ririgashi amma ya'kiyin shiru rigarta tad'aga tana shirin bashi nono saurin tashi Muzaffar tayi yace

" mai zakibashi ? " amsa tabashi da nono mana " tamke fuska yayi yace " wai dama kina nufin akwai ruwan nono anan gurin ? shiru Rayhana tayi tami'kama Shureem nono ganin yadda yaro yayi shiru yana shan nonon yashashi jinjina kai sauka yayi daga bed amma cikin mamaki yaji mararshi tayi wani irin 'kullewa sosai yayi 'ko'karin mi'kewa amma yakasa cikin dabara yake tafiya dan kar Rayhana talura shiga cikin toilet yayi cikin tashin hankali Muzaffar yace

" ya Allah " rumtse idan shi yayi sabida yadda yakeyin fitsari cikin wahala ga mugun d'aurewar da marar shi tayi ga ciwo tsayin lokaci sannan yafito adu'ke ganin babu Rayhana da yara yasashi sauke ajiyar zuciya yace " gara dakika bar bedroom d'in nan "

A daddafe yayi salla ganin ciwon gaba yakeyi yasashi kiran wayar Mu'azzam babu jimawa Mu'azzam yashigo kwance yasameshi saman bed dukya takure jikin shi dubashi yashigayi cikin mamaki Mu'azzam yace

" mai kenan Muzaffar ? kanada mata fa amma kazauna ka kashe kanka akan bu'katar ka gaskiya hakan beyiba ayadda nalura babu wata matsala a tsakanin kada Raihan to amma yaya haka "

tamke fuska Muzaffar yayi yace

" eh babu matsalar komi amma bakaganin 'kananan yaran dake tare da ita ay bai kamata natakurataba ko ? "

Girgiza kai Mu'azzam yayi yace " wannan ba hujja bace Muzaffar yaro baya hana miji kusantar matar shi koda ciki ne sede idan cikin yazoda matsala dan haka ka'aje wannan tunanin naka kayi abinda yadace "

Tamke fuskar Muzaffar yayi sosai yace " kai malam karubutamin magani idan zaka iya idan kuma baka iyawa to zanje wani waje "

Jinjina kai Mu'azzam yayi yace " ok zan rubuta maka amma fa bawani dad'ewa zaiyi yanayima aykiba idan har ba abinda yadace kayiba to akwai lokacin dako kasha bazaiyi aykiba "

Rubuta mai Mu'azzam yayi yabashi sannan yace bari yakawo mai wani yasha yasamu sau'ki cikin mamaki Rayhana takalli agogon parlour har 11:20 amma Muzaffar bai fitoba shiga cikin bedroom d'in tayi tsaye taganshi alamar yanzu yagama shiryawa rungume shi tayi tabaya tace

" My Noor lafiya har yanzu bakafito kayi break ba ? " hannun shi yasa yacire hannuwanta daga rungumar datayimai hanyar fita yanufa batare dayace mata komiba kan dining d'in yaje yazauna cikin sauri Rayhana taje 'ko'karin zubamai abincin tayi fuska babu walwala yace

" barshi zansa dakaina d'auki yara kuje part d'in kaka nizan fita sena dawo " yanayin maganar ne batare daya kalletaba ganin yanayin shi yasa Rayhana barin gurin cikin sanyin jiki ahankali yajuya yana kallon bayanta cikin sauri yakawar da idan shi kamar wanda yatuna wani abu

Baki d'auke da sallama Rayhana tashiga part d'in kaka cikin sauri kaka tace " maraba da Rayhana kawomin yaran nan mi'ka matasu tayi sannan ta gaidata fuska sake ta'amsa hadda samata albarka mamaki sosai Rayhana tayi cikin 'kasada murya Zarha tace

" lalle kaka anga mutuwa andena nunamakowa 'kiyayya " nufar inda zahra take tayi tazauna suka gaisa amsar yaron tayi tace

" to wani suna zamukira shi dashi Zarha ? " ta'be baki Zarha tayi tace " Yazeed mana ay babu mutuncin dake tsakanina dame sunan balle na'boye " girgiza kai Rayhana tayi tace

a'a Zarha hakan bai kamataba karki duba abinda sukayi miki martabar masarautar ku zakijawo idan kika sakaya sunan duk ranar dasukaji zasusan lalle akwai tarbiyya da karamci cikin masarautar HAYAT sabida sunsan sunyi miki abinda yakai ki ambaci maisunan dawani muguwar kalmar amma sabida tarbiyya bakiyi hakanba kuma kinga kodan shi yaron bai san komiba kuma duk kanku babu wanda zai'ki ke ko mahaifin shi danginki ko dangin shi dan haka kiyi ha'kuri ki sakaya wannan sunan amma koni banbaki damar ki sassauta ma Aliyu anan kusaba kisa yasan darajarki kafin ku dedeta "

ajiyar zuciya Zarha tayi tace " tabbas hakane Aunty Raihan kuma nad'auki sawarar amma bana tunanin zan iya komawa gidan Aliyu " Murmushi Rayhana tayi tace " Zarha kisani har yanzu akwai igiyar auran Aliyu akanki tunda yamayer dake tun tuni "
Chapter 24 · 0% Book details