← Book details Hayatul Mahayat Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 41

Sashe 27

Hayatul Mahayat Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

" lafiya Muzaffar ? kaje ka kwanta kayi ha'kuri addu'a zakayi ma Nabila kuma kagodema Allah daya bayyana gaskiya Allah yadawo maka da Farooq da haidar cikin 'koshin lafiya gaskiya kayima Raihan godiya akan wannan jahadin datayi maka zanbama Raihan kulawa tamkar nice na haifeta Allah yanunamin auran ta zanyi mata gata wadda ko Zarha banyi mawaba "

zama Muzaffar yayi dankam shi yayi matu'kar mamakin furucin Rayhana na nuna babu aure a tsakanin su tuna lokacin datake bama Shureem nono yayi cikin zuciyar shi yace " dukda ba itace mahaifiyar suba amma ta'iya shayer dasu ashe bata ta'bayin aure ba ? amma ta'iya jure munanan kalamaina akan haka yaya zanyi kenan ? "

Mi'kewa yayi yace " Momy tana ina zamuje mu kwanta ne " cikin mamaki Momy tace hakan bazai yiyuba Muzaffar kwana cikin bedroom d'aya ya haramta kai da Raihan tunda ba matar kabace wanda yafaru abaya dan banida msaniyar hakan ne shiyasa daga yau Raihan tana nan tare dani itada yaran ka "

Cikin takaici Muzaffar yace " Momy duk abinda Raihan tafad'a gaskiya ne amma banda abu d'aya Raihan matata ce bawai 'kanwaba kamar yadda tafad'a tun damuka shigo cikin masarautar mu akwai aurena akanta sannan nima se yau nasan Farooq da haidar sune Shureem da Sudees Momy kitasota muje mu kwanta dare yanayi kumani bazan iya kwanciya babu su Farooq ba "

Jinjina kai Momy tayi tace " lalle ma Muzaffar idan son Raihan kakeyi to kasanar dani amma bazan yarda da wannan maganar takaba inada tabbacin Raihan bazatayimin 'karyaba maiyasa bakafad'i hakanba cikin taron jama'a kowa yaji se yanzu kasanar dani sonta kakeyi senaji ra'ayinta idan ta amince da kai shikenan amma seka jira ta kammala karatu "
girgiza kai Muzaffar yayi yace " har yanzu banajin son Raihan amma ina bu'katar zama tareda ita sabida su Farooq nine yadace tazauna dani Momy bawaniba kodan yarana sabida ayanzu ita suke kallo matsayin uwa kuma banaso susan ba itad'in bace dan karsu d'andani zafin maraici nine yadace Momy Allah Raihan matatace "

Wani irin kallo Momy tayi mai tace " kafita idona Muzaffar banyarda da zancan kaba se idan Raihan ce tasanar dani haka koda hakane to babu shakka senaji nakuma yarda cewa tana sonka kuma kaima kana sonta bazan bayar da Raihan ga wanda bayason taba ko ita bata son shiba dan haka kar in sakejin kace Raihan matar kace karka hana masusonta zuwa kaji nagayamaka zaka iya shiga ka gansu dan darajar yaranka suna bedroom d'in Zarah kafin zuwa gobe agyra mata wancan bedroom d'in na Sumayya dukda baiyi komiba amma andad'e babu wanda yashiga yakamata a gyara shi 10 minutes nabaka sabida zan kwanta "

Daga haka Momy tabar parlour cikin bedroom tashiga cikin takaici Muzaffar yanufi bedroom d'in rai 'bace yana shiga yasameta zaune tanabama Shureem nono wani irin tsaki yaja yace

" kitashi muje kisanar da Momy cewa akwai aure na akanki muje mu kwanta inajin bacci " kallon shi Rayhana tayi cikin rashin nuna tsoro tace " ayni jira nakeyi kabani ta'kardar saki sabida nasan kai baka 'karya al'kawari kuma dama yarjejeniyar tamu zata 'karene daga angane gaskiya dan haka bazan iya cigaba dazama da wanda babu kowa cikin zuciyar shi se wadda bata raye zan cigaba da shayar maka da yaranka sabida darajar Momy harsu isa yaye nikuma bayan nagama karatu naza'bi miji dede da ra'ayina kai kuma kanemi babbar mace kabar yarinya 'karama "

Cikin matsanancin 'bacin rai yace " idan kuma na'ki sakin nakifa zakiyi aure da aurena akankine ? kuma kibar shayar dasu Shureem haka sabida bana bu'katar breast d'inki su canza daga na budurwa ayanzu zasu iya rayuwa da madara sabida sun kusayin shekara ki shirya sanar da Momy gaskiya zuwa gobe dasafe "

Kwantar da Shureem tayi tace " ba dai maganar auran muba karabudani cikin sirri kamar yadda muka shirya komi cikin sirri na auri wanda raina yakeso nagode ma Allah dayasa babu abinda yashiga tsakanina da kai balle nazauna da kai dole kum......... "

Kanta yayi cikin zafin rai yace " to bari wani abin yashiga senaga dame zakiyi tun'kaho hawa yayi saman bed d'in yajawota jikin shi cikin sauri ya kwantar da ita yarufamata baya yana shirin rabata da kayanta jin maganar Momy yasashi saurin sauka daga bed d'in shigowa Momy tayi wani irin kallo tayimai tace fita zan kulle part d'ina seda safe 10 minutes nace amma gashi har kusan 20 "

rai 'bace Muzaffar yafita yana isa cikin part d'in shi ya iske Mu'azzam tasowa Mu'azzam yayi yarungume shi yace

" natayaka murna d'an uwana sannan nazo neman alfarmar ka kasan ance bari yahuce shike kawo raban wani inaso kayimin jagora wajan auran Raihan nasan zatafijin maganar ka sabida kai tafi sani kaji dan....... "

Turashi Muzaffar yayi cikin zafin rai yanunashi yace " wallahi idan kasake zuwamin da irin wannan maganar senayima abinda zakace anya kuwa ni d'an uwan kane ? fitamin daga part "

'Daga 'kafad'a Mu'azzam yayi yace " ok kabarshi zannemi soyayyar ta batare da taimakon kaba " daga haka yasakai yafita cikin 'bacin rai Muzaffar yashiga yin watsi dakayan cikin parlour cikin wani irin yanayi yashiga cikin bedroom toilet yanufa ruwa yasakar ma kanshi cikin zuciyar shi yace

" zanyi maganin ki Raihan idan baki fad'i gaskiya ba hmmmmm har kinja anfara kawo miki hari lalle zanyi maganin duk wanda ya ra'beki "

Daga Al'kalamin.....🖊

NPEEDY A AJI🌸🦚🌸

Comments and shine please

Love u all sisters 🥰🌹🤝🏻?🌸🤝🏻🌸 *HAYATUL MAHAYAT* 🌸
🦚🦚🦚🦚
🦚🦚
🦚
Story and written
By
NPEEDY A AJI

Dedicated to
My Fatima Zahra yar amana

🌸NOORUL HAYAT🌸 WRITERS ASSOCIATIONS

🌹Expressions and heed Searching Sweet story Novels writer🌹
>>>>>>>>>>>>>>>>>>>
We are together all fans🤝🏻🥰
KAFA'DI ALKHAIRI KO KAYI SHIRU 🤫

My Novels
1-NAYI RAYUWA DAKE
2-SANADIN ACCIDENT
2019
3-SAKAYYAR CUTA
4-RUFAFFIYAR ZUCIYA

HAYATUL MAHAYAT
typing......✍🏻
Assalama alaikum kuyi ha'kuri najina shiru kunsan jiki da jini se ahankali jikin babu dad'i ga rashin wutar nefa ina mi'ko sa'kon gaisuwa da jinjinar bangirma agareku ina godiya sosai Allah yabar zumunci tabbas naga masoya masu tarin yawa yawanku yakai yadda bazan iya lissafokuba sede nayi jam'i godiya nike jiki Alhamdulilh yayi sau'ki sosai Allah yabar 'kauna ana tare all masoya 🤝🏻😘🌹
🥰😊

Bismillahir Rahamanir Rahim

🅿 41 & 42

Tsayin lokaci Muzaffar yana cikin toilet sannan yafito d'aure da towel dawani a hannu yana goge kanshi bayan yatsane jikin shi jallabiya kawai yazura yazauna bakin bed juyawa yayi yazurama bed d'in ido dede inda Rayhana take kwanciya da yara tashi yayi tsaye yatana kai komo yakasa kwanciya wayar shi yad'auka dukda yasan bashida number ta amma yashiga dubawa tsaki yaja layin Zarha yakira har kusan sau 3 amma bata d'agaba sakekira yayi seda takusa katsewa sannan tad'aga cikin muryar bacci tace

" Hello yaya lafiya kuwa ? tsawa yadaka mata yace " itace takawo haka maza kituro min number Raihan " baijira mai zataceba yakashe wayar bin wayar Zarha tayi da kallo tana mamakin yadda bashida number Raihan kuma yake nemanta cikin daran nan tura mishi tayi takashe wayar sabida gudin masifar shi dan bata bu'katar yasake kiran ta musamman yadda tajishi cikin fad'a

Jin 'karar shigowar text yasa Muzaffar saurin duba wayar shi ajiyar Zuciya yasauke tamkar Raihan d'in yagani kiran wayar yashigayi amma ba'a d'agawa yakuma kasa ha'kura dakiran cikin mamaki yace

" yau ni Muzaffar niketa kiran number har sau babu adadi amma babu piking " harya cire rai dazata d'aga babu zato yaji muryar ta cikin bacci " Assalama alaikum " shiru Muzaffar yayi sabida yarasa mai zece nemo natsuwar shi yayi yace " mijin kine Muzaffar ina bu'katar Lipton yanzu " kallon agogon d'akin tayi 02:26 cikin muryar bacci tace

" haba dadyn Haidar kayi ha'kuri dare yayi sosai kabari zuwa safe kaji " shiru natsayin lokaci sannan yace " bazan iyayin hakan ba ajiyar Zuciya Raihan tayi tasake cewa to tayaya zanfito yanzu kasanfa Momy bazata barniba amma in sha Allah zuwa safe dawuri zan had'a maka kaji dadyn Farooq " a hassale Muzaffar yace banason wannan sunan idan muna magana tsakanina dake kibari se gaban su Momy kifad'i wannan cikin d'an mamaki tace to se wanne ? ajiyar Zuciya Muzaffar yayi yace se wanda kikaga damar sawa kuma kiyi gaggawar fad'ar gaskiya idan kuma kika'ki zakija abubuwa dayawa kinji nagaya miki " kashe wayar yayi yawurgata saman bed yanasakin huci kamar wanda yayi dambe

Bin wayarta Rayhana tayi da kallo tana mamakin 'karfin hali irin na Muzaffar shida yace bayasonta kuma bazai iya rayuwar aure da 'karamar yarinyaba to tayaya yadamu akan seta bayyana makowa shi mijin tane ' gaskiya bazan iyaba bazan zauna da wanda bayasona ba " kashe wayar tayi takoma ta kwanta amma takasa komawa bacci cikin 'bacin rai Muzaffar yahau saman bed cikin muryar fushi yace " tayaya kikayimin tsaye cikin zuciya Raihan maiyasa nikeson cigaba dazama dake? ok nagane sabida su Farooq kinacan kina bacci amma ni inanan nakasa hmmm "

Kwanciya yayi yaja blanket amma kokusa yakasa runtsawa cikin farinciki Mu'azzam yashiga cikin parlour shi zama yayi yana Murmushi cikin mamaki Arfat take kallon shi kasa jurewa tayi tataso tazo kusadashi tazauna cikin d'an sakku tace

" doctor wane abune yasaka cikin farin ciki haka ? rabandanaga Murmushin fuskarka harna manta " sakeyin Murmushi Mu'azzam yayi yace " dole nayi Murmushi sabida nasamu wadda nikeso yarinya mai tarbiyya ga hankali da natsuwa ga sirrin kyau kay gaskiya nayi matu'kar sa'a "

Wani irin ba'kin ciki Arfat taji amma setayi saurin dannewa tace " natayaka murna sosai Doctor wacece wannan mai matu'kar sa'a haka ? " Murmushi Mu'azzam yayi sannan yami'ke taku d'aya biyu yayi yace " Raihan ce tunda babu aure tsakaninta da Muzaffar ay nikam tagyarumin kishirya idan har ta'amince kizauna a d'akinki to babu matsala idan kuma tace bazata zauna da kishiyaba tofa zakiyi waje "

Yana gama fad'in haka yanufi cikin bedroom wani irin 'bakin ciki da razana Arfat taji cikin sauri tabi bayan shi amma kafin ta'karasa haryasama 'kofar key dur'kushewa tayi agurin tana kuka mai tsuma zuciya yanajinta dukda cewa yanajin kukan nata cikin ranshi amma yadake tsayin lokaci yanajin kukan nata har yadenaji
Chapter 27 · 0% Book details