← Book details Hayatul Mahayat Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 39 OF 41

Sashe 39

Hayatul Mahayat Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Baki d'auke da sallama suka shiga cikin parlour Amarya tsayawa su yaya Ahmad sukayi cikin mamaki yaya Ibrahim yace " lafiya naga kunja burki nan ? " murmushi yaya Abubakar yayi yace inamu ina shiga cikin bedroom kade akwai kaje kafitomana da ita musiyi baki muma amaran namu jiranmu sukeyi " dariya yaya Ibrahim yayi yace " ayfa se amare dariyar suma sukayi shiga cikin bedroom d'in yaya Ibrahim yayi cikin sauri Islam tarufe fuskarta murmushi yaya Ibrahim yayi yace " gaskiya wannan 'kawar taki ta kyautamin dahar tazauna tana jiran mushigo bata bar minke cikin kewaba " murmushi 'kawar tata tayi aje ledar hannunshi yayi yace kufito parlour 'yan uwana susiyi bakin amarya kinsan 'yan uwana sune abokaina " juyawa yayi yafita yanasakin murmushi cikin sanyin jiki Islma tasakko daga kan bed d'in jan mayafin tayi tarufe fuskarta 'kawar tata takama hannunta zuwa parlour

Bayan sunfito sun zauna yaya Ahmad yagabatar da addu'a sannan sukashiga yin abinda yakawosu babu jimawa suka mi'ke cikin sakin fuska yaya Abubakar yacema 'kawar Islam " muje nasa jafar yakaiki gida ko " tashi tayi tayima Islam sallama godiya tayimata shima yaya Ibrahim godiyar yayi mata suka fita rakiya yayi musu zuwa babban parlour bayan sunfita yakulle ko ina yakoma ciki nanma kullewa yayi ganin babu Islam a parlour yasa shi yin murmushi yanufi cikin bedroom zaune yasameta bakin bed babbar rigarshi yacire had'ida kwance agogon hannunshi kallonta yayi yace " tashi kiyo alwala muyi sallah ko "

Cikin sanyin jiki tami'ke tashiga toilet bayan tafito shima yashiga sosai Islam takejin fad'uwar gaba bayan yafito yajasu sallah suna idarwa yayi mata tambayoyi kamar yadda addini yatanada murmushi yaya Ibrahim yayi yami'ke yad'akko ledar dayashigo da'ita shida kanshi yad'akko fulet yajuye musu kazar had'ida tsiyaya musu lemon cikin cup sedayayi dagaske sannan Islam taci kad'an bayan sungama yami'ke yashiga toilet wanka yayi yafito d'aure da towel a 'kugun shi cikin jin kunya Islam takauda idanunta daga kanshi murmushi yayi yace " kishiga kiwatsa ruwa ko "

Sosai Islam takeji fad'uwar gaba wordrop tabud'e tad'akko doguwar riga sannan tanufi toilet tsayin lokaci sannan tafito sanye cikin doguwar rigar bacci tagefan ido take kallon shi kwance yake saman bed yana latsa wayarshi ganin tayi tsaye yasashiyin murmushi tashi yayi zaune yace " tahonan mana baby " sakejuyar dakanta tayi cikin jin kunya murmushi yaya Ibrahim yasakeyi yatashi isa yayi gareta d'aukarta yayi cak yad'aura saman bed saurin juyawa Islam tayi jawota yaya Ibrahim yayi yanasha'kar kamshin jikinta cikin sanyin murya yace

" kunyata kikeji baby ? haba ninefa Ibrahim angonki maiyasa kikejin kunyata " cikin sanyin murya Islam tace " yaya bazan iya hanakaina jin kunyarkaba sema jidanikeyi tana'karuwa " murmushi yayi yace " tobari nasauketa kunyar " jawota yayi jikinshi take yaji wani irin yanayi yashiga jikinshi ga kamshi namusamman dayake tashi cikin jikinta bataredajan lokaciba yashiga aykamata da sa'konni masu wurar bita tuni tsoro yakama Islma jikinta yad'auki rawa amma shi ina yayi nisa wajan sarrafata

Tsayin lokaci yana aykamata manyan sa'konni sosai yarud'e tashi yayi yarufamana baya yana niyyar shiga babban al'amari niko Npeedy kunyar yaya Ibrahim takamani nayi saurin fita inaji Islma nakuka tana ro'kon Yaya Ibrahim amma da'alama ya'ki sauraranta tofa Islam anshiga sahun manya bari nakoma naga yaya Amarya Rayhana take

Momy dakanta takai Rayhana part d'in Muzaffar zaunar da'ita tayi kan cushion tafuskanceta sosai tace " Raihan nasan duk abinda nayimiki bazai ciremiki kewar mahaifiyarki ba amma inaso kid'auka mahaifiyar takice zatayimiki nasiha karki kalleni matsayin uwar miji kidubeni matsayin uwa agareki Raihan kiyima mijinki biyayya dan Aljannarki tana gareshi nasan ke maibiyayyace kuma mai ha'kuri to ki'kara idan muzaffar yayi miki wani abu karkiji sakkar sanar dani kema idan kinyimai ni zaisanar mawa banason yanke hukunci kai tsaye Raihan duk abinda kikeso kisanar dani zanyimiki shi muddin inada halinshi " su Farooq zasud'inga kwana gurina tunda naga basatashi cikin dare idanma suntashi se susha madarar su banaso sud'inga hanaki bacci "

Rungumai momy Rayhana tayi cikin kuka tace " banida bakin dazanyi godiya agareki Momy tabbas ked'in uwace babu ko sakka Allah yayi miki sakayya dagidan aljanna amma Momy kar su Haidar sutakuraki dakin barsu agurina " Murmushi Momy tayi tace " karki damuwa ba "kwacesu zanyiba iya darene kawai kuma kinga nasaba dajin motsinsu kinji kuyi ha'kuri "

Jinjina kai Rayhana tayi kama hannunta Momy tayi tanufi cikin bedroom d'in da'ita zaunar da'ita tayi bakin bed tasaki murmushi tace " Allah yabaku zaman lafiya daga haka tajuya zatafita cikin sauri Rayhana tataso rungume Momy tayi tabaya tasaki kuka sosai Rayhana takeyin kuka da'kyar Momy tasamu tayi shiru sannan tafita

Cikin 'kagara muzaffar yace kuzomuje mana mu'azzam nifa na'kosa naga pretty " murmushi mu'azzam yayi yace " to ay sekabari Momy tafito ko idan kuma zakashiga Momy naciki to gahanya nan mude munada sauran kunya " murmushi muzaffar yayi yace to ay ga Momyn can tafito itada hadiman ta " kallon inda Momy take sukayi muzanbil yace " gaskiya kaji dad'i muzaffar Momy tana masifar son matarka itadakanta takaima ita har d'aki gaskiya kaji dad'inka muz......"

Jan hannun shi muzaffar yayi suka nufi hanyar part d'inshi dankam shi yayi matu'kar matsuwa yaga matarshi suna shiga cikin parlour muzaffar yanufi hanyar bedroom bin bayanshi sukayi saurin tsayawa muzaffar yayi yace " ina zakushiga cikin bedroom d'ina ina ay tsayawa zakuyi nashiga mufito bedroom ay sirrin mata damijine "

Duka muzalbin yakawo mishi yayi saurin kaucewa yashige ciki yana shiga yayi saurin 'karasawa gareta sabida sasshekar kukanta dayaji aje ledar hannunshi yayi yajawota jikinshi yashiga tambayarta lafiya amma takasa cewa komi sefaman kuka datakeyi sosai hankalin muzaffar yatashi duk yadda zaiyi dan ganin tayi shiru amma abin yagagara cikin damuwa yami'ke yace

" bari nakira miki Momy inaga ita zakisanar da ita damuwarki juyawa yayi cikin Sauri tasha gabanshi share hawayenta tayi tace " dan Allah karka kirata nabar kukan ina tuna mama ne bansan halin datake jikiba yanzu " saurin kallonta yayi yace dama bata raye ? saurin girgiza kai tayi tace " a'a bahaka nike nufiba " ganin yadda tayi kamar batason maganar yasa yajawota jikinshi yace bari nasallamisu mu'azzam suna parlour "

Yana karashe fad'ar haka yafita cikin mamaki su mu'azzam suke kallon muzaffar murmushi yayi yace " nafagode da wannan babbar rakiyar taku Amaryar tawa bazatasamu fitowaba nima zankoma ciki sedasafenku " saurin tashi muzalbil yayi yajawoshi yace " Allah baka'isaba sekarakamu harabar gida dad'in abinma muma munada mata " janshi sukayi har waje suna dariya sedasukaje harabar gidan suka sakeshi suna dariya shima dariyar yakeyi yakoma ciki

Sosai muzaffar yanunama Rayhana tsananin soyayya a wannan daran wanda suduka seda sukaji kamar babu kowa cikin duniyar masoya sesu

Misalin 10: 30 Aunty Sumayya tafito daga bedroom d'inta cikin shirin fita tsaki taja tasake kiran wayar yaya Ibrahim akaro nakusan 6 amma bai d'agaba cikin fusata tanufi 'bangaran Islma tanafad'i tun wajan 10 nasofita na'kosa najenaga gidan 'kanwata Islam amma ya'kifitowa shimai amarya ko sallama babu tashiga dede lokacin yaya Ibrahim yafito daga bedroom d'auke da Islam zaikaita dining cikin razana Aunty Sumayya tayadda bag d'in hannunta tadafe 'kirjinta tace " Islam kece ko idanunane ? " murmushi Islam tayi tace " nice Aunty " cikin fusata Aunty Sumayya tayi kansu

Daga Al'kalamin....🖊

NPEEDY A AJI 🌸🦚🌸

Comments and shire please

Love u all sister 🥰😘🌸 *HAYATUL MAHAYAT* 🌸
🦚🦚🦚🦚
🦚🦚
🦚
Story and written
By
NPEEDY A AJI

Dedicated to
My Fatima Zahra yar amana

🌸NOORUL HAYAT🌸 WRITERS ASSOCIATIONS

🌹Expressions and heed Searching Sweet story Novels writer🌹
>>>>>>>>>>>>>>>>>>>
We are together all fans🤝🏻🥰
KAFA'DI ALKHAIRI KO KAYI SHIRU 🤫

My Novels
1-NAYI RAYUWA DAKE
2-SANADIN ACCIDENT
2019
3-SAKAYYAR CUTA
4-RUFAFFIYAR ZUCIYA

HAYATUL MAHAYAT
typing......✍🏻
And
🙆🏻💘 Mugun sartse!!!!! 💘🙆🏻

Coming soon after hayatul mahayat in sha Allah
Bismillahir Rahamanir Rahim

🅿 63 & 64

Hannu yaya Ibrahim yasa yadakatar da'ita dole Aunty Sumayya tadakata sabida yadda taga fuskar shi zaunar da Islam yayi kan kujerar dining sannan yadawo gurinta babu zato taji yasureta tsakiyar parlour yanufa da'ita zaunar da'ita yayi kan cushion shima yazauna rungumota yayi cikin sanyin murya yace

" Haba Honey duk wannan fushi kuma akaina zakisaukeshi ninefa Ibrahim naki tabbas nasan nayi lefi agareki amma kisani duk kece kikaja komi banyi niyyar 'kara Aure ba amma kikasa nayi ra'ayin haka gaskiya inajin ciwon yadda kike takura Muzaffar akan dole seya auri Islam hakan yasa kika tsani Nabila tsana mafi girma har tabar duniya da ba'kin cikin ki amma koda tarasu baisa kinyi nadamaba kika koma kan Raihan dukda irin taimakon datayima d'an uwanki haba Sumayya wallahi idan kikayima Raihan wula'kanci inajin zafi har cikin Raina fiyeda yadda nikejin zafi idan kika wula'kanta Nabila narasagane dalilin haka amma inajin Raihan tamkar jinina

Sumayya kece kikace bazakiyi kishi da Islam ba ashe abin bahakabane to amma meyasa kikeso ayima wasu kishi ke kuma bakiso yaya haka Islam fa 'kanwarkice tayaya zakibari zuciya tasa ki aykata abinda zaisa girmanki yazube ? Sumayya inasonki fiyeda tunaninki kuma babu sama dake cikin zuciyata da idanuna amma kisani ada na auri Islam ne dan kikoyi darasi badan inasontaba amma maganar gaskiya ayanzu ina son Islam sosai Honey ni Ibrahim inamebama matata ha'kuri dan Allah kuzauna lafiya zantafi zuwa jibi idan akwai abinda kuke bu'kata keda yara kisanar dani "

Kuka sosai Aunty Sumayya takeyi tanayin nadamar yarda datayi dasu Islam tabbas batayi tunanin su zaliha zasuci amanarta hakaba mi'kewa tayi tanajin wani'iri jiri yanad'ibarta bata kalleshiba tace
Chapter 39 · 0% Book details