← Book details Hayatul Mahayat Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 41

Sashe 14

Hayatul Mahayat Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Jinjina kai Muzaffar yayi shiko boka tuni yaji wani irin murd'awar ciki yasan idan har yabu'de to tabbas zaigamu damasifa cikin in ina da daburcewa yace

" maimartaba ay kunsan malamanma kalakalane nide banida sani akan addu'o'in bud'e sihiri musamman irin wannan mugun sihirin gaskiya sede anemi wani "

Cikin sauri kawu Yusuf yace " to ay babu damuwa semu nemi wani kawai kunsan shi ilimi kogine ? ta'inda wani yasha batanan wani yashaba muje kawai malam nasallameka " dasauri Muzaffar yace

" haba malam ay dole seka bud'e wannan sihirin kasan kai bakacika malamiba kazoyima mahaifina magani gaskiya ni banma yarda dakaiba dan haka kabud'e wannan kwalbar sihirin sannan mubaka damar tafiya idan kuma baka bud'eba to wallahi rufeka zanyi nayi bincike akanka amshi maza bud'e mug........."

Afad'ace kawu Yusuf yace " lalle muzaffar wato kaiga fitsararre kowa baiyi maganaba se kai dukga yayyanka basuce a'a ba se kai tunda yace bai iyaba ay bai zamadole seya iyaba dan hak........... "

Dakatar dashi kaka tayi dafad'in " ay abinda muzaffar yace yayi dede dan haka dole yabud'e idan har ba munafiki bane " wani irin fitsari boka yaji yafara zubomai shiko kawu Yusuf wani irin bugu zuciyar shi keyi waziri kuwa sharar zufa kawai yakeyi cikin azama boka yajuya yafita aguje cikin sauri mu'azzam da muzalbil da yaya Abubakar sukabi bayan shi shima Muzaffar juyawa yayi zaibi bayansu Momy tace " dagata Muzaffar barsu sukamoshi yana fita 'kofar parlour dogarawan dake tsaran gurin sukayi saurin ri'keshi sha'ko wuyan shi muzalbil yayi yafara dukanshi cikin sauri Sarkin gida yarugo yace

" Allah ya taimakeka Yarima kabada izinin dukan shi karka wahalar da kanka " afusace muzalbil yace " kai Sarkin gida wannan huruminmu ne banakuba dan haka dakanmu mukeson nayimai mugun duka " cigaba da jibgarshi sukayi idan wannan yaduka wannan yajibga aguje kawu Yusuf da waziri suka fito nufar wajan sukayi sunayi musu tsawa ki'ro hannun mu'azzam kawu Yusuf yayi wani irin naushi muzalbil yasaukema kawu Yusuf abaki wanda yasa ha'korin shi fita lokaci d'aya hantsilawa yayi yafad'i yana waiyo Allah cikin sauri muzalbil yayi kanshi yana fad'in ya Allah dan Allah kawu kayi ha'kuri nazata wannan malamin 'karyarnne nakawoma naushi "

Kasa magana kawu Yusuf yayi kamashi mu'azzam yayi yanufi parlour shi dashi dan bashi gajin gaggawa sedasu muzalbil sukaga boka yayi lilis sannan suka rabu dashi sawa sukayi aka kulleshi awaje mafi tsaro tsayin lokaci suna cikin parlour maimartaba suna cigaba dayin farincikin samun lafiyar shi fitowa maimartaba yayi parlour bayan yayi wanka yashirya tsaf bayajin komi ajikin shi se rashin kuzari zama maimartaba yayi cikin soyayya ya kalli su Sudees yace

" har sunyi bacci kenan ? masha Allah addu'a " maimartaba yayi sannan yafarayin jawabi Alhamdulillah a yau ina matu'kar farinciki da Allah yakawo 'karshen wannan kalular tawa wanda jikokina suka zama silar warkewata kai Muzaffar mahaifiyar ka tasanar dani komi akan wannan matar taka dakuma yaranka Alhamdulillah nayi matu'kar farinciki haka kuma inayi muku fatan alkairi a cikin zamanku

Kowa yasheda nayima wa'innan jikokin nawa kyautar wannan babban gidan nawa dake wajan masarautar HAYAT da kimanin kud'i nera million 20 kowa 10 million sannan kowa yasheda bazanyi sassauci ba gaduk wanda yayi 'ko'karin cutar dasu dan haka kowa yakiyaye inaso ashirya walimar dawowar muzaffar dazuwan matar shi dakuma babban farinciki wato samun Sudees da Shureem kowa yasan irin yadda akeyin bikin murna vaduk wacce tahaihu to su Shureem basusamu hakanba sabida basa taredamu dan haka yanzu za'ayi musu shgalin murnar zuwansu duniya harna tsayin sati 2 inaso acibada datsare wannan malamin har zuwa bayan kammala wannan bikin murnar da'alama yanada masaniyar wani abu gameda wannan kwalbar sihirin sabida naji yana fad'in zaifad'i komi kowa yatashi yaje ya kwanta "

Mi'kewa kowa yayi amma wasu cikin rashin kuzari suka mi'ke bayan fitar kowa kilishi kawai akabari cikin part d'in sabida itakeda girki tashi tayi tanufi kan cushion d'in da maimartaba yake zaune zama tayi cikin farin ciki tace

" Nayima Allah godiya dabaka lafiya maimartaba Allah ya'kara tona asirin ma'kiyanka "

Ameen maimartaba yace hira sukacigaba dayi irinta mata da miji kallon Zarah Muzaffar yayi yace

" waike mai kikeyi ne har yanzu cikin gidan nan baki tafi gidan mijin kiba ? "

Tuni zuciyar Zarah takarye cikin damuwa tace " yaya tun bayan tafiyarka da kwanaki 3 Aliyu yasakeni k....... " dakatar da'ita yayi dafad'in " saki shi Aliyu ? lalle yayi kuskure jeki kwanta zuwa safe zamuyi magana "

Rai'bace Muzaffar yawuce itako Rayhana binshi kawai takeyi ga yaro saman kafad'ar yayi bacci part d'in shi suka nufa har cikin bedroom d'in shi yashiga da Sudees kwantar dashi yayi saman bed d'in shi waigowa yayi ganin babu Rayhana yasashi nufar hanyar parlour rai 'bace kiranta yayi bayan tashigo ya amshi Shureem ya kwantar dashi saman bed jawota yayi da'karfin tsiya tafad'o jikin shi saurin janye jikin shi yayi daga nata kunnanta yakama yamatseshi da'karfi yace

" kinwani tsaya daga parlour bana gaya miki anan zaki d'inga kwanaba ? tun daga yau kinaso kinunamin bakyajin magana ko ? to wallahi kibini ahankali kawai kayan baccin Nabila cikin wardrobe d'ina ga toilet cen kije kiyi wanka kibud'e kid'auki d'aya daga ciki kisa idan kinsa ki kwanta kusada Sudees sune zasu zama mana katanga tsakanina dake da nayi 'kud'in a'kasa zaki dinga kwanciya amma darajar yaranki yasa najanye haka dan sun taimakeni sunzama silar warkewar dad "

Juyawa yayi yafita parlour System d'in shi yad'akko yabud'e komawa yayi cikin bedroom d'in yazauna saman sofa

Cikin sanyin jiki take d'aga kayan duk babu wadda zata iya sawa sabida duk masu bayyana surar jikine da'kyar tasamu wata doguwa mai kauri amma tanada tsagu daga 'kasa zuwa 'kugu shiga tayi da'ita cikin toilet d'in shiko bai masan tanayiba dan gaba d'aya hankalin shi yana kan system

Tsayin lokaci sannan Rayhana tafito hannu tasa ta'ri'ke wajan tsagun nufar wajan bed tayi cikin tsaurin murya yace " zonan " fad'uwar gaba taji sosai amma kuma yaya zatayi dole tanufo inda yake kallon ta yayi yahad'a rai yace

" wai mai kike rufewa lalle yarinya nikam mai zangani ajikinki kina 'kwala to dama kindena boye wannan jikin naki dako kallo bai isheniba balle ta'bashi fita parlour zakiyi inaso nashiga wanka sabida bakiyi girmanda zaki'iya kallon koda sumar 'kafataba kuma duk ranar dakika sake kikaga koda kafad'atace to wallahi senayi miki hukunci a wannan ranar fita "

Sosai Rayhana taji zafin wannan kalaman nashi dan har seda sukasata 'kwalla shiko ko'ajikin shima har seda bacci yafara d'aukar Rayhana sannan Muzaffar yafito afurgice tatashi zaune sabida jin kiran tadayi asaman kanta gaba yatasata suka shiga cikin bedroom d'in hawa yayi saman bed yakwanta had'ida rungumo Shureem yaja blanket sabida akwai sanyi sanyi ga tafkatafkan windows d'inshi abud'e masu 'bakin glass daga amma daga ciki farine ana iya hango komi daga ciki amma daga waje ba'a iya ganin kowa zuwa tayi taja labulayen jikin windows d'in sabida itakam tsoro takeji idan tahangi wajan a cikin daran nan dukda cewa akwai hadahadar mutane musamman dogarawa da Security cikin tsawa yace mata " maza kimayar dashi yadda yake kizo ki kwanta ke nifa banason takura da damuwafa dan haka bibini ahankali kinji nagaya miki "

Jiki a sanyaye tamayar dashi yadda yake sannan taje tahau ssaman bed d'in rungume Sudees tayi tarumtse idanunta kamar maiyin bacci amma takayin hakan sabida cikin matu'kar tsoro take

Washe gari tun misalin 7 aka gama shirya komi ko'ina kabi cikin masarautar HAYAT abin shi'awa sabida an 'kawata gurin da 'kyalekyale da abubuwan ban shi'awa cikin sauri abokin Aliyu yashiga cikin parlour shi cikin sa'a kuwa yasame shi azaune zama yayi ko gaisawa basuyiba yace

" Yarima nazoma dawani mihimmin labari yau anayi wata gagarumar walima cikin masarautar HAYAT nasan kowa yana cikin farinciki babu wani 'bacin rai kaga kasamu hanyar ganin Zarah cikin sau'ki sekace gayyatarka akayi tunda masarauta ce basedole anji waye yagayyacekaba "

Mi'kewa Aliyu yayi yana jinjina kai murmushi yasaki yace

" tabbas nasamu dama abokina lalle kakawomin gud news kaje kashirya tare zamu bari nashiga wanka "

Mi'kewa yayi cikin zuciyar shi yana fad'in " yau senaji d'umin jikinki da laushin jikinki danayi mugun kewarshi tsayin watanni "

To Aliyu barimugani ko hakan zai yiwu

Cikin tashin hankali waziri yace " Allah yabaka nasara sarkin gobe munacikin tashin hankali fa wallahi idan boka yafad'i gaskiya tofa kashinmu yabushe dan natabbatar kashemu za'ayi "

Mi'kewa kawu Yusuf yayi cikin rashin sonyin magana sabida kumburin dabakin shi yayi ga'azabar ciwo yace

" ay se idan yana raye sannan zaifad'a ko ? Waziri kasan duk yadda zakayi akashe boka cikin wannan shgalin nasan hankalin kowa zai d'auku wajan hidimar babu wanda zai ankara "

Jinjina kai waziri yayi alamar gamsuwa

Cikin damuwa Ummi tace " tur'kashi gawani saban aykin kuma gagarumi "

A'bangaran Aunty Sumayya kuwa cikin fad'a tace

" kwantar da hankalin ki Islam inde Muzaffar ne sekin aure itakuma waccen shegiyar Rayhana senasan yadda nayi tabar cikin masarautar nan tareda samun mugun wula'kanci daga Muzaffar "

Tofa Rikici kenan

Daga Al'kalamin.....🖊

NPEEDY A AJI 🌸🦚🌸

Comments and shire please

Love u all sisters 😘🥰🌹🌸 *HAYATUL MAHAYAT* 🌸
🦚🦚🦚🦚
🦚🦚
🦚
Story and written
By
NPEEDY A AJI

Dedicated to
My Fatima Zahra yar amana

🌸NOORUL HAYAT🌸 WRITERS ASSOCIATIONS

🌹Expressions and heed Searching Sweet story Novels writer🌹
>>>>>>>>>>>>>>>>>>>
We are together all fans🤝🏻🥰
KAFA'DI ALKHAIRI KO KAYI SHIRU 🤫

My Novels
1-NAYI RAYUWA DAKE
2-SANADIN ACCIDENT
2019
3-SAKAYYAR CUTA
4-RUFAFFIYAR ZUCIYA

HAYATUL MAHAYAT
typing......✍🏻

Bismillahir Rahamanir Rahim

🅿 25 & 26

Sosai cikin masarautar HAYAT tacika da d'inbin jama'a kamar anyi watanni ana gayyatar mutane wajan wannan walimar cikin d'an damuwa Momy take kallon hanyar part d'in Muzaffar sabida har yanzu basu fitoba gashi har malaman sun gama hallara kowa suyake jira

Acikin part d'in kuwa Muzaffar zaune yake kan cushion d'in parlour fuskar nan tashi a matu'kar tamke cikin matsanancin tsoro Rayhana take kallon shi tsayin lokaci sannan cikin tsawa yace

" ke zonan " jiki yana rawa ta'iso gurin shi tunkafin tadu'ka yasauke mata mari mai zafi agigice tayi zaman 'yan bori a'kasa hannu yasa yasha'ko wuyanta cikin fad'a yace

" wato ke harkin samu guri ko ? mai yakai hannunki kan kayana ? " wasu irin hawaye suka fara sauka saman kumatunta murya a sanyaye tace
Chapter 14 · 0% Book details