← Book details Hayatul Mahayat Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 36 OF 41

Sashe 36

Hayatul Mahayat Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kafin zahra tayi magana wayarta tad'auki ruri kallon momy tayi takashe kiran cikin tuhuma momy ta kalleta tace " zahra duk abinda zakiyi kisani akwai auran Aliyu akanki dukda bama tunanin komawarki wajan shi amma dole ki kiyaye tunda auranku yananan " cikin mamaki Zahra tace " Momy taya kikasan aurena da Aliyu yana nan ? "

Kallonta Momy tayi sosai tace " mahaifin shi yakira maimartaba akan cewa Aliyu yamayar dake kuma shima Aliyu yakira shi amma maimartaba yace " bazaki komaba garama ya sauwa'ke miki kawai to shine daganan basuzoba kuma basu sake kiraba muma bamu nemesuba dama munaso ki haihu ne tukun asan abinyi kicigaba da kallon kanki matsayin matar aure har zuwa lokacin dazamu yanke shawarar abinda yadace nima bangoyi bayan ki komaba sabida inda Aliyu yana sonki da yazo gidannan yafi a 'kirga amma babu shi babu alamar shi kuma ansanar ma iyayen shi haihuwar ki amma ko barka balle suzo gani jariri kinga kenan har yanzu suna nan akan bakarsu "

Daga haka momy tami'ke tabar parlour shigowar text cikin wayarta yasata maida dubanta kan wayar text d'in Aliyu ne kamar yadda tayi tsammani tamkar bazata dubaba kamar yadda tasaba sekuma tabud'e

_Assalama alaikum my dear ina fatan kin tashi lafiya dan Allah ina ro'konki kiyafemin zahra wallahi ina matu'kar sonki ina kuma farinciki da abinda kika haifamin dan nasan izuwa yanzun kin haihu amma dan Allah ina ro'kon ki kisanar dani abinda kika haifamin bana BIHAR ina Cameroon ayanzun tun washegarin danazo gurinki kuma kece silar tafiya na sabida bazan iya zama cikin 'kasar BIHAR batare da zahra ba ina matu'kar sonki daga mijin ki nahar abada Aliyu Yazeed_

Shiru Zahra tayi tana tunanin kalamanshi " kenan ma shi baisan maiye na haifaba danni yabar 'kasar shi da iyayen shi harma da aykin shi to ina matar shi ? "

Afusace Aunty Sumayya tashiga cikin parlour ta zaune tasamu yaya Ibrahim yana ayki cikin system tsaye tayi akanshi tace " Dadyn Amfal " dagowa yayi fuskarshi d'auke da murmushi yace " na am uwar gidan Ibrahim " zaro ido Aunty Sumayya tayi cikin girgiza da kalmar shi

Daga Al'kamin....🖊

NPEEDY A AJI 🌸🦚🌸

Comments and share please

Love u all sisters 🥰🤝🏻?🌸 *HAYATUL MAHAYAT* 🌸
🦚🦚🦚🦚
🦚🦚
🦚
Story and written
By
NPEEDY A AJI

Dedicated to
My Fatima Zahra yar amana

🌸NOORUL HAYAT🌸 WRITERS ASSOCIATIONS

🌹Expressions and heed Searching Sweet story Novels writer🌹
>>>>>>>>>>>>>>>>>>>
We are together all fans🤝🏻🥰
KAFA'DI ALKHAIRI KO KAYI SHIRU 🤫

My Novels
1-NAYI RAYUWA DAKE
2-SANADIN ACCIDENT
2019
3-SAKAYYAR CUTA
4-RUFAFFIYAR ZUCIYA

HAYATUL MAHAYAT
typing......✍🏻
And
🙆🏻💘 Mugun sartse!!!!! 💘🙆🏻

Coming soon after hayatul mahayat in sha Allah
Bismillahir Rahamanir Rahim

🅿 55 & 56

" Wannan Kalmar taka tanunamin cewa dagaske aure zakayi ? " Sosai ran yaya Ibrahim ya'baci yace " amma gaskiya sumayya wani lokacin hankalin ki yana tafiya yawo ko kina nufin momy zatayi miki wasane " to gaskiya ne zanyi aure kuma babu fashi dan haka kigayamin duk abinda kike bu'kata zanyi tafiya zuwa wani ayki amma se bayan zuwan amarya dan senafi samun natsuwa idan nad'anci angonci kafin natafi idan kuma naga zaki takurama 'kanwar taki to senatafi da'ita kawai dan babu mai shiga cikin farincikina "
Cikin fusata Aunty sumayya tace " dadyn Amfal kishiya ni !!!! wacece wannan mai ganganci da rayuwarta ? " murmushi yaya Ibrahim yayi yace " koda nagayamiki bazaki fahimtaba zakifi ganewa idan kika ganta alokacin da matsayin ku yazama d'aya ina nufin idan tasan waye Ibrahim nima nasan wacece ita 'kilama idan Allah yasa nabuga ball a seti yakasance akwai 'kaninsu Amfal wato new baby woooow Allah kanunamin wannan ranar akwai kwasar shaku shaku 🕺🏻😜

Daga haka yaya Ibrahim yami'ke had'ida rufe system d'in shi yabar parlour fad'awa Aunty sumayya tayi kan cushion tadafe kai tanajin zafi cikin zuciyar ta afili tace " lalle koma wacece zatayi kuskuran auran mijina to wallahi zansa tayi nadama mafi muni cikin rayuwarta "

Cikin harabar skul d'insu yayi parking jawota jikinshi yayi sosai yarungumeta yanasha'kar kamshin jikinta kamo fuskarta yayi bakinshi yahad'e danata yashiga yimata kiss dandanan yafara shiga wani layi cikin dabara Rayhana tajanye jikinta danashi cikin muryar lallashi tace

" My Noor kayi ha'kuri nakusa makara kaji " cikin sanyin jiki yamaida hannun shi kan mararshi yace " pretty kingani ko amma shikenan please idan kindawo kicema Momy zakikoma gurin mijin ki " zaro ido Rayhana tayi tace " karufamin asiri Allah bazan iyaba kai kasanar da'ita " murmushi muzaffar yayi yace " naji amma idan nasanar da'ita idan har ta tambayeki kina bu'katar hakan zakice eh ? zaro ido Rayhana tayi ta girgiza kai had'ida cewa " dan Allah kabarni nashiga lecture " ajiyar zuciya Muzaffar yasauke yace idan kinfito kikirani zanzo nad'aukeki dan banaso driver yana zuwa d'aukarki dan kinsan mijin naki akwai kishi "

Fita Rayhana tayi tanasakin murmushi binta yayi da kallo har tashiga ciki tada mota yayi yatafi yanajin zuciyar shi tayi sanyi wata hidimar yatafi ba gida yanufaba cikin dan damuwa mahaifiyar Islam tace

" gaskiya badan maimartaba ne yanemi auran Islam dakanshiba kuma mahaifin ku ya'amince da gaskiya bazan yarda da auran ba sabida Sumayya zataga kamar munci amanar tace "

Ta'be baki Aunty Zaliha tayi wato 'kawar Aunty Sumayya tace " wane cin amana kuma umma shifa Ibrahim shine yace yanasonta dakanshi bamune muka tura Islam akan tasa yasotaba hasalima ita Sumayya ita tanemi Islam akan taje tazauna gurin ta kuma ita dakanta tace duk namijin dayasami Islam matsayi mata gaskiya yamore to kinga zataso mijinta yamore ko umma " harararta Umma tayi tace " rufemin baki angayamiki idan za'ayima mace kishiya tana duba dangantakane ayko da cikin zuri'ar sune tofa sekinga tayi kishi kodan ke bakida ita shine zakice haka tobari mugani idan Isma'il yace zaiyi aure zakice yamore dan haka kitanadi irin amsar dazakibama Sumayya aranar dataga Islma matsayin matar mijinta "

Murmushi Aunty Zaliha tayi tace " Umma in sha Allah ni baza'ayimin kishiyaba kuma inada masoshi masu yawa wa'inda zanbama Sumayya kude kawai mucigaba da hidimar biki kuma kar wanda yabari Sumayya tasan maganar auran nan har se ranar da Islma tashiga matsayin mata "

Girgiza kai umma tayi tana tunanin wannan lamarin zaune Samha take a parlour hannunta ri'ke da Apply sefaman zuyashi takeyi takasaci cikin mamaki muzalbil yake kallonta 'karasowa yayi yazauna kusada ita hannu yasa yashafi cikinta sannan yazauna rungumota yayi cikin tattausar murya yace

" haba baby har yanzu kinkasa cire wannan damuwar ? kina zaune har lokacin fita aykinki yakusa wucewa amma kina zaune " ajiyar zuciya Samha tasauke sannan tace " inaga zan ajiye ayki tunda bakaso " sosai yafuskanceta yace " haba baby na kibar wannan maganar duk komi yawuce na amince da aykin ki sabida nasan banida shakka akanki dan haka tashi kishirya mufita idan ka saukeki nise driver ya'karasa dani Office "

Murmushi Samha tayi tami'ke cikin zuciyar ta tace ayanzu nagamsu barrister yana sonan nima yakamata nabashi kulawa

Kayane aketashigowa dasu part d'in momy set d'in akwatina 4 masu matu'kar tsada sosai Momy take mamakin irin wannan kaya cikin sanyin jiki aunty sumayya tashiga parlour zaro ido tayi sannan takalli momy kafin tace komi muzaffar yashigo parlour kallon momy yayi ya'karasa gurinta cikin farin ciki yace

" Momy kinga wannan kayan set 3 na akwatinan daduk kayan ciki na Raihan ne 1 kuma gudummawata ga yaya Ibrahim kinga seya kawo nashi ahad'a akai gidan amarya dan na'kosa Raihan tasamu Aunty mai 'kaunar ta kuma momy anjima za'a shigoda set 2 nakoma na d'aki daya naki Momyna seki za'bi irin color dakike so d'aya na Raihan inaso acanza komi na part d'inmu nakima haka Momy se asa hadimai sufito dakomi nacikin part d'in bana bu'katar komi duk na kwashe abubuwana masu mihimmanci sauran bana bu'katar su masu saka kayan musamman suke dasu za'a kawo kayan kafin suzo se'a kwashe komi "

Farin ciki momy tayi sosai kanshi tadafa tace " Allah yayi maka albarka Muzaffar " Ameen yace cikin farinciki yafita yanufi part d'in kaka cikin damuwa aunty sumayya tace

" Momy gaskiya muzaffar bayasona wato hadda had'a lefe wai gudummawa hmmm wato kishiyar tawa zaiyima set d'in akwati ciki dakayan lefe lalle " zama tayi rai 'bace

Murmushi Momy tayi tace " Sumayya ay kece kika nemi 'kiyayya gurin muzaffar amma badan hakaba ay duk cikin 'kannan naki muzaffar yafi jidake amma kika takura rayuwar shi har kikasa yatsaneki kinga kuwa kece kika nemi 'kiyayya dakanki amma ko yanzu zaki'iya dawo da darajarki gareshi musamman idan kikaso Raihan "

'Kara had'a fuska Aunty sumayya tayi jin momy ta ambaci Raihan itako momy ko lurama batayiba sema kiran hadimai datayi akan suje susanar dasu ummi umma mamy dayaran suzo ganin lefan Raihan

Babu jimawa kowa yahad'u cikin parlour momy bud'e akwaitinan akashigayi sosai kowa yayi mamakin irin kayan da muzaffar yazubama Rayhana ciki hadda keys d'in manyan motoci guda 2 da kyautar ma'kudan kudi zuwa saban Account d'in dayabu'de mata kowa yana mamakin irin wannan dukiya da muzaffar yakashe akan Rayhana akaf tarihin masarautar HAYAT babu wadda akata'bayima lefe irin na Rayhana cikin zuciyar Arfat tace " tabbas muzaffar mallakin Raihan ne Allah kabani zaman lafiya nida mijina "

Kafin wani lokaci tuni anshiga had'a part d'in momy dana muzaffar da kaya masu matu'kar kyau da tsada kallon wayarta Zahra takeyi se faman ruri takeyi amma takasa d'agawa akaro na 4 sannan tad'aga dagacan 'bangaran Aliyu yasauke ajiyar zuciya yace

" haba Zahra kiji tausayina mana wallahi ina sonki har cikin raina banida burin dayawuce naganmu atare akodayaushe nayimiki al'kawarin ajeki cikin saban gidan dana gina ba cikin masarautar muba dan Allah zahra kiceci rayuwata "

Ajiyar zuciya zahra tasauke tace " zanyi tunani " sosai Aliyu yaji dad'in kalmarta yasake cewa mai kika haifamin kuma yaya sunan shi ? " seda tayi Jim sannan tace " namiji kamar yadda kabu'kata sunan mahaifin kane ina kiranshi da Sayyid " nata gama fad'ar haka takashe kiran kallo Aliyu yabi wayar dashi wani irin sassanyan murmushi yasaki yanaji kamar yabud'e ido yaganshi gaban Zahra da Sayyid d'inshi "
Chapter 36 · 0% Book details