← Book details Hayatul Mahayat Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 41

Sashe 6

Hayatul Mahayat Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

" Ni Muzaffar nine mace tayima wannan mugun sharrin lalle badan d'an uwanaba da mahaifina wallahi dasena halakata nida 'kasar Bihar babu rana kuma babu lokaci

Wani 'kayatatcen gida akanufa dashi wato masaukin shi yana shiga yazauna kan cushion a parlour zuciyar shi duk babu dad'i sawa yayi aka kiramai doctor ya dubashi yabashi magani tunda yatafi bai bud'e wayar shi ba se yau tsayin 1 weeks kenan nan yaita ganin text d'in mahaifiyar shi da maimartaba da 'yan uwanshi babu text d'in daya bud'e sena mahaifiyar shi tambayar inda yashiga takeyi da halin dayake ciki amsa kawai yabata agajarce

" ina lafiya nakoma Pakistan anan zanciga dazama bazan dawo garekuba Momy nayi matu'kar mamaki dakuka yarda zan'iya aykata haka Momy wallahi banyima Arfat komiba kuma zmbanje daniyar aykata komiba shi Mu'azzam d'in yace inje akan naduba part d'in shi sabida Arfat tacemai tanajin motsi cikin part d'in shine ina zuwa tacemin a cikin bedroom d'in tane ina shiga tarufe 'kofar take sanar dani wai ni takeso tun farko ba Mu'azzam ba Momy kuyi bincike akan wannan abin nasanar dakene badan inajin shakka ko tsoran waniba a'a sedan kisan gaskiya tayadda zuciyar ki zatasamu natsuwa "

Tura text d'in yayi yatsurama wayar tashi ido tashi yayi yafita yabar wayar anan

Cikin tashin hankali Momy take karanta text d'in Muzaffar mi'kama yaya Ahmed wayar tayi shima yakaranta bama yaya Abubakar yayi shima yakaranta cikin damuwa Momy tace Abubakar jeka kiramin Mu'azzam tashi yayi yafita babu jimawa dafitar yaya Abubakar Zarah tashigo cikin kuka tafad'a jikin Momy

Hankali tashe Momy tashiga tambayar ta amma takasacewa komi tsa yaya Ahmad yadaka mata yace " idan bazaki sanar damu damuwar kiba tokiyi gaggawar rufe mana baki kibarmu muji da damuwar mu shiru Zahra tayi tare Abubakar yashigo shida Mu'azzam da Muzanbil basu text d'in Muzaffar akayi suka karanta bayan sun gama yaya Ahmad yace

" kai Mu'azzam hakane ? abinda Muzaffar yace "

Jinjina kai Mu'azzam yayi yasake bayyana musu duk yadda abin yakasance sannan yad'aura dacewa

" Momy nifadama inada shakka akan wannan lamarin nasan Muzaffar bazai aykata hakanba idan kuma ya aykata to babu shakka ba'a cikin hankalin shi yakeba amma kuyimin ha'kuri zuwa nanda safiya zan tabbatar da gaskiyar lamarin "

Rai 'bace yaya Abubakar yace " tayaya zaka tabbatar da gaskiya wadda baka tabbatar da'itaba tun lokacin da'abin yafaru se yanzu da abin yabaiyana cikin masarauta "

Ajiyar zuciya Mu'azzam yasauke yace " eh tahanya d'ayace zan tabbatar wadda bazan iya bintaba alokacin sabida ina cikin tashin hankali matu'ka tunda na auri Arfat banta'ba kusantar taba sabida ina ganin kamar hankalin ta ba akaina yakeba ta wannan hanyar zan tabbatar da gaskiya kuma inada tabbacin Arfat bata bibiyar maza "

Shiru kowa yayi sabida mamaki amma banda Muzanbil danshi baiyi mamakiba sabida shima hakan take cikin fad'a Momy tace

" lalle Mu'azzam har kake iya fad'in wannan maganar agabana to idanma Arfat tayi haka batadalefi kaine mai laifin sabida kakasa sauke mata ha'kkin ta tokam yanzu sede kabari mahaifin ku yatambayi malamai aji yaya makomar auranku 'yanzu "

Cikin sanyin rai Momy tace

" auta daure kisanar damu damuwar ki tunda akayi auran ki bakizo gidannan ba se yau amma gashi naganki cikin tashin hankali "

Kukan da Zahra take ri'kewa yakufce mata cikin kukan tasanar dasu komi mi'kewa Muzanbil yayi zaifita azuciye yaya Ahmad yayi saurin ri'ko hannun shi yace

" karkayi yunkurin komi se abinda maimartaba yace banason kowa yaji wannan lamarin "

Kwantar da kanta Momy tayi kan cushion tamakasa yin tunanin komi

Koda sarki yaji wannan lamarin na Zarah tashi yayi tsaye yafara kai komo cikin tashin hankali yace

" wai maiyake faruwane ? cikin masarutata daga wannan se wannan wallahi Aliyu 'karya yakeyi Zarah bazata ta'ba aykata zinaba in sha Allah se yayi nadamar dababu amfani akula dacikin jikin Zarah kar'abari wani abu yasamaishi shine zai zama silar saka Aliyu cikin matu'kar nadama "

Cikin mamaki wani mutun ke kallon Rayhana tana siyar da kayan lambu Cikin rumfa kallon yaran dake gabanta yayi nufar katin dake bayanta yayi sallama yayima mutumin bayan sun gaisa yace

" dan Allah bawan Allah wannan yarinyar kuma daga ina ? kashi hadda yara gata 'karamar yarinya "

Cikin had'a fuska mutumin yace

" kaga karufamin asiri wannan dakake gani narasa gane itad'in wane jinsice yau satin ta 6 anan gurin ranar danaganta anan nayi mamaki sabida se bayan magrip nabar shago har zuwa lokacin babu alamar mutun agurin amma washe gari danazo sena ganta kaga wannan rumfar datake ciki to sati d'aya baza'a iya gamayin taba amma naganta a kwana d'aya danaje nayi mata magana akan tatashi to ranar ko sisi banyiba hakama washegari

Danasake fitowa banyi mata magana ba segashi nayita ciniki kaga wancan mai kantin shi harda yun'kurin marinta kafin hannun yakaiga jikinta yama'kale haka yad'inga ihu seda yayi kwana 3 yana ro'konta sannan tashafa hannun yasa'be kuma kaga wannan kayan datake sedawa tunda nike nan banta'ba ganin wani yazo siyaba sabida kaf kasuwar nan tsoran ta akeji koda maganar arziki kayi mata to ranar haka zakatashi babu cinikin ko sisi amma ahaka sekaga tasiyar dakomi tana 'kirga kud'ad'anta "

Ajiyar zuciya mutumin yasauke yace

" nagode ma Allah dayasa banyi mata magana ba "

Kuyi ha'kuri banajin dad'i ne sosai kuma bazan samu yimuku typing ba gobe sabida ina wani uziri

Daga Al'kalamin.........✍🏻

NPEEDY A AJI 🌸🦚🌸

Comments and shine please

Love u all sisters 🥰🌹
[10/9, 9:32 PM] NPEEDY A AJI: 🌸 *HAYATUL MAHAYAT* 🌸
🦚🦚🦚🦚
🦚🦚
🦚
Story and written
By
NPEEDY A AJI

Dedicated to
My yar amana

🌸NOORUL HAYAT🌸 WRITERS ASSOCIATIONS

🌹Expressions and heed Searching Sweet story Novels writer🌹
>>>>>>>>>>>>>>>>>>>
We are together all fans🤝🏻🥰
KAFA'DI ALKHAIRI KO KAYI SHIRU 🤫

My Novels
1-NAYI RAYUWA DAKE
2-SANADIN ACCIDENT
2019
3-SAKAYYAR CUTA
4-RUFAFFIYAR ZUCIYA

HAYATUL MAHAYAT
typing......✍🏻

Bismillahir Rahamanir Rahim

🅿 11 & 12

Hawaye suka cika idanun Rayhana cikin zuciyar ta tace " ni Rayhana yau nazama tamkar mujiya acikin mutane wannan itace 'kaddara ta Allah kabani ikon cinyewa kallon yaran tayi tace Allah sarki tunkuna jarire an maidaku marayu sabida zalinci koson abin duniya Allah kasamufi karfin zuciyar mu in sha Allahu bazan barku kuyi kukan rashin mahaifiya ba "

Cikin girmamawa liman yakai gaisuwa gaban maimartaba

" Allah ya'karamaka lafiya kamar yadda kasani auran Mu'azzam da Arfat yananan babu abinda yawarwareshi sede idan shi Mu'azzam d'inne yace bazai iya zama da'ita ba amma kafin wata ma'amalar aure tasake shiga tsakanin shi da ita setayi istubura'i zuwa wannan lokaci idan babu 'kaddarar ciki shikenan idan kuma akwai har seta haihu amma babu abinda yashafi auran su sabida fayd'e ne bada yardarta hakan tafaruba "

Sallamar Liman maimartaba yayi zuciyar duk babu dad'i kiran Mu'azzam yayi yasanar dashi hakan sannan yad'aura dacewa

" Mu'azzam abindayafaru yariga yafaru karka bari mace tashiga tsakanin ka da d'an uwanka karka sake wani yaji cewar baka ta'ba kusantar Arfat ba kaga idan wannan abinyafita to babu shakka wata matsalar ce idan har Allah yakawo cikin 'kaddara tasanadin haka to banason kafurta cewa banaka bane sabida rufuwar asirin d'an uwanka Mu'azzam zuciyata takasa yarda cewa Muzaffar zai aykata haka cikin hankalin shi amma bashida mafita karka daku baza'abar bincike ba kuma bazan baryin addu'a akan Allah yabaiyana gaskiya "

Kuka sosai Mu'azzam yakeyi yarasa yadda zai kwatanta yadda yakejin zuciyar shi tabbas yana matu'kar son Arfat amma bazai iya fifitataba akan d'an uwan shi tashi yayi yama maimartaba godiya yafita

Shiko Muzanbil tunda wannan abin yafaru ya'kajin tsanar mace cikin ranshi dan kam shi yayi imanin inde Muzaffar yayima Arfat fayd'e to ita tashirya komi dan yasan halin Muzaffar sosai zaman da Samha tayi kusadashi yasashi 'kara tamke fuska cikin sanyin murya tace

" haba mijina maiyasa har yanzu kakasa gane irin son danikeyimaka ? Yarima wallahi zuciya ta tanagaf da bugawa akan sonka dan Allah kabani koda gurin dazan tsuguna ne acikin zuciyar ka koda bansamu gurin zaman ba "

Mi'kewa Muzanbil yayi zaibar gurin sabida jiyake duk ta isheshi saurin kamo hannun shi tayi cikin zafin rai yajuyo a tsora tayi saurin rungume shi cusa kanta tayi cikin 'kirjin shi tana jin wata irin bugun zuciya jin shiru yasata d'ago kanta ahankali fararan idanunta tasauke kan kyakkyawar fuskar shi ganin idanun shi tayi alumshe murmushi tayi sannan tasakeshi bedroom d'in ta tanufa tana sakin murmushi cikin 'bacin rai yabita da kallo cikin zuciyar shi yace

" lalle Samha kinfara rainani amma zanyi maganinki sabida naga kinfara shiga hurumin daba nakiba "

Misalin 9 Hamdiyya tashiga part d'in Kilishi itada kuyangun ta 2 zaune tasamu Kilishi a parlour anayimata tausar kafa gefanta Zahra tana kishingid'e idanun ta alumshe hannun ta ri'ke da Apple tunanin irin mugun wula'kancin da Aliyu yayi mata takeyi jin shigowar Hamdiyya yasata bud'e idanunta cikin girmamawa tace

" Ummi barka dashigowa " kamar dagaske Hamdiyya tace " ayni bazan amsaba tun yaushe kikazo amma bakije kin gaidaniba se danazo ? waima mai yakawoki kikabaro gidan mijin ki ? "

Kafin Zahra tace komi Kilishi tayi saurin cewa " mijin natane yayi tafiya kuma zai jima kafin yadawo kasancewar Allah ya azurtata dasamun ciki kuma yana d'an bata wahala shine taro'keshi akan yabarta tadawo gida har zuwa lokacin dazai dawo to kinji dalilin zamanta "

Yatsina fuskar Hamdiyya tayi dan ita bahaka tasojiba sallama tayima Kilishi tafita zuciya babu dad'i bayan fitar Hamdiyya da d'an wani lokaci Kilishi tasallami hadimanta tashi tayi tanufi bedroom had'ida kiran Zarah cikin bedroom d'in bayan tazauna Kilishi tadubaita tace

" Zarah inaso kiri'ke wannan sirrin karkisake wani cikin masarutar nan yasan cewa Aliyu yasakeki sabida akwai masujiran haka dayawa bayan 'yan uwanki banason kowa yasakejin haka "

Jinjina kai Zarah tayi sabida yadda idanunta suka cika tab dahawaye tashi tayi tafita bedroom d'in ta tashiga kan bed tafad'a tasaki wani irin kuka mai tsuma zuciya Hamdiyya tana fita part din Hajiya Ayna tashiga wato kaka zaune tasameta tanacin tuwon acca da miyar ku'baiwa wadda tasa manshanu daga ciki kuma hadiman tane ketayimata hidama sabida part d'in kaka baya rabuwa da ba'ki

Gaisuwa Hamdiyya tami'ka sannan tazauna seda tajira kaka takammala cin abincin sannan tace
Chapter 6 · 0% Book details