← Book details Hayatul Mahayat Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 1 OF 41

Sashe 1

Hayatul Mahayat Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

[10/9, 9:28 PM] NPEEDY A AJI: 🌸HAYATUL MAHAYAT🌸
🦚🦚🦚🦚
🦚🦚
🦚

Story and written
By
NPEEDY A AJI

Dedicated to
My Yar Amana

🌸 NOORUL HAYAT 🌸
WRITERS ASSOCIATION

🌹Expressions and heed Searching Sweet Story Novels 🌹

<<<<<<<<<<<<<<<<<<<<<<
We are together all fans 🤝🏻🥰

KAFA'DI ALKHAIRI KO KAYI SHIRU 🤫

Alhamdulilah gashi Allah yasake had'amu a wani saban novel Allah yasa nafara a sa'a Allah kakareni da aykata ba dedeba a cikin wannan book d'in Allah kasa yadda nafara lafiya nagama lafiya Ameen

'Kir'kirarran labarine daga zuciyata taimakon Allah nikenema akan wannan labarin Allah karka barni da kaina dededa 'kiftawar ido bannemi shawarar kowaba dan Allah kar wanda yayimin shisshigi cikin labarina please banason hayaniya wanda yaga bai mishiba bance dole yakarantaba balle adinga 'kananun maganganu akai nagode sosai masoya

Ina matu'kar yinku 🤝🏻🌹♥🥰

🅿 1 & 2

BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM

Gudu sukeyi sosai cikin 'kumgurmin daji amma dukda haka hannuwan su nari'ke dana juna tayin lokaci suna gudu 'kara dattiyuwar matar tasaki had'ida fad'uwa cikin kuka yarinyar dake ri'ke da hannunta tadur'kusa tace

" mama dan Allah kitashi sun biyomufa ? "

Cikin wata irin murya matar tace

" Rayhana inamai umartarki da kibar gurinnan kafin su iso nikam daga nan bazan iya cigaba ba kalli 'kafata macijine yasareni kuma nasan izuwa yanzu dafinshi yagama shiga cikin jikina "

Kuka Rayhana tasaki sosai kicikicin d'agata tashigayi jin 'karar harbin bindiga yasa tadaka mata tsawa

" Rayhana idan baki tafiba amatsayina na mahaifiyar ki banyafe mikiba zakibari kashemu dukane kije aduk inda kike kinatare da Allah dakuma Addu'a ta kitafi nace "

Wani irin kuka Rayhana tasaki sumbatar hannun mahaifiyar tata tayi tace

" in sha Allah zamu sake haduwa Mama mama a ina danginki suke ? zan ..... "

" Nace kibarnan Rayhana tafi cikin kariyar Allah 'yata "

Juyawa Rayhana tayi aguje cikin duhun bishiyoyi tabuya amma tana iya hango mamanta wasu 'kattine majiya karfi ko wannen su hannun shi ri'ke da bindiga cak suka d'auki mahaifiyar ta suka juyada ita jin 'karar Harbin bindiga yasa Rayhana juyawa aguje cikin dokar jejin tsayin lokaci tana gudu dede wata 'katuwar bishiya tatsaya tana sauke numfashi

Hannuwanta 2 tad'aura saman kanta tasake saka wani irin iho jin sautin kukan jariri yasa Rayhana saurin waiwagawa cikin sauri tafara duddubawa tanabin sautin kuka cikin sa'a idanunta sukayimata arba da kyawawan jarire twins masu matu'kar kyau cikin kyawawan kayan sanyi

Cikin gigita tashiga waigewaige kozataga wani amma babu alamar kowa wani irin sauti taji

" keeee Rayhana kidauki wa'innan Twins d'in mugunta da makirci yasa anrabasu da iyayensu kituna kalmar mahaifiyar ki idan kika ceci wa'innan yaran to zamu saka idanu akan mahaifiyar ki kuma in sha Allah zaku gana wata rana

Mahaifin wa'innan yaran d'an babban gidane kuma tsayayyan namiji Rayhana kishiga duniya neman mahaifin su amma an kashe mahaifiyar su kuje tareda kariyar Allah sunayensu Faruq da Haydar kiduba abayan Faruq akwai wani ba'kin tabo tananne kad'e zaki iya banbance su sabida tsananin kamarsu nabarki lafiya "

Cikin rawarjiki Rayhana tadu'ka a gabansu cikin kuka tace

" wannan wace irin jaraftace yara har 2 kaddara tabani darana tsaka ina yar 19 years nashiga Uku "

'Daukar yaran tayi tana d'aukarsu sukayi shiru goya d'aya tayi tasa'ba d'aya wani 'karamin box tagani daga gefan inda suke d'auka tayi batare data bud'eba tacigaba datafiya sosai tagaji gashi har yanzu takasa hango titi babu motsin d'an Adam ko kad'an

Duhu taga yamamaye garin d'aga kanta sama tayi wani irin hadarine yahad'u gagarumi tuni jikin Rayhana yafara rawa sabida ita Allah yayi mata tsoran hadari waige waige tafarayi wata bukka tahango d'an nesa da'ita cikin sauri tanufi gurin addu'a tatsaya tayi sannan tashiga katifar rimice a cikin bukkar se 'kwaryar nono rufe da faifai dawata fitila sagale daga sama bakin bukkar da asabari kwantar da Faruq tayi sannan ta kwance Haidar shima ta kwantar dashi wata irin wal'kiya akayi cikin sauri tasauke asabarin takunna fitilar komawa tayi tazauna kan katifar rimin tazubama yaran ido

Wata irin matsananciyar soyayyar su taji cikin zuciyar ta Afili tace

" ikon Allah yauga Rayhana dayara batare datasan ina tadosaba amma wannan yaran dagani iyayen su ba 'yan wannan 'kasar tamuta ta Cameroon bace sunfi kama da 'yan yankin Southerly Asia Allah kasadani da iyayen wa'innan yaran nahuta Waiyo mama Allah yakareki daga sharrin mugun mahaifina "

Wasu irin hawayen ba'kinciki sukashiga gangarowa daga cikin idanun ta bud'e wannan box d'in tayi wani ring tagani mai matu'kar kyau dagani zaiyi tsada se wasu d'aurin kud'i amma ba irin na 'kasar Cameroon d'in bane maidasu tayi cikin box d'in tarufe tagumi tayi zuwacan tace

" dole nayi binciken wa'innan kud'in nawace 'kasane dole zai zama anan mahaifin farooq da haydar yake zanje kowace 'kasace dan neman shi nikam daga yau Farooq da Haydar aguna sun koma Sudees da Sureem "

Wata irin tsawa da'akasaki yasa Rayhana saurin saka kanta cikin cinyoyinta tuni jikinta yad'auki rawa addu'a tashigayi akan Allah yasa wannan ruwan yad'auke cikin sauri

" Banayin farinciki idan bangankaba Sojana banajin dad'in kalma idanba takaba babu wanda ya'iya furta haruffan sunana naji babu gyara se kai Sojana "

Waige waige yafarayi yana neman inda zaiganta amma babu alamun ganinta sede murya komawa yayi yazauna yadafe kanshi idanun shi nafitarda siraran hawaye sakejin muryarta yayi

" mai nike gani nafita daga idanun Sojana ? a'a karka bari rashina yasa kazama mai raunin zuciya tsayayyar zuciya gareka karta raunana dan rashin Nabila hawayenka masu matu'kar tsadane ba'kinciki ciki yayi 'kad'an yasamesu sede farinciki Sojana ka kalli Farooq da Haydar inada tabbacin zasu wankemaka rad'ad'in rashina dan nikam bazan dawoba ba'kiya sundatse igiyar dake tsakanina da kai Sojana sun datse rayuwar Nabilar ka n....... "

Mi'kewa yayi cikin sauri cikin dakakkiyar murya yace

" My Nabila 'karya sukeyi bazamu ta'ba rabuwaba sekin dawo gareni konazo na riskeki babu amfanin rayuwata idan babu Nabila sun rabani dake sun rabani da Twins d'ina taya zan'iya rayuwa My Nabila kizo mukoma gida kina......... "

Amatu'kar furgice yatashi gawata irin zufa data wanke fuskar shi wani irin mugun kallo yawatsama wanda yatasheshi daga baccin tashi yayi zaune yajingina da fuskar bed d'in yana sauke ajiyar zuciya ruwa mai sanyi yami'ka mishi babu musu ya'amsa yasha duka yashanye ruwan shiru na tsayin lokaci sannan yace

" haba Muzaffar yakamata karage wannan damuwar kayarda Nabila tamutu bakuma zata dawoba wanda yafika sonta shine yad'auki abunshi taya zakakasayin tawakkali ? katashi maimartaba yanason ganin mu a babban parlour "

Tsaki Muzaffar yaja sannan yasauka daga bed d'in hanyar toilet yanufa seda yakusa kaiwa yatsaya juyowa yayi yace

" Mu'azzam kasani Nabila bata mutuba dan har abada tananan araye cikin zuciya ta "

Idasa shiga cikin toilet d'in yayi binshi da kallo Mu'azzam yayi ya girgiza kai tashi yayi yafita yana jinjina girman soyayyar da Muzaffar yakema Nabila kai tsaye babban parlour yakoma d'aukacin iyalan masarutar HAYAT suna cikin babban parlour

MASARAUTAR HAYAT KENAN wadda ke cikin 'kasar BIHAR

Sarkin masarautar Sarki Abdurrahaman sarkine adali mai tausayin talakawanshi yanada mata 2

Sarauniya kilishi itace uwar gida tanada yara 7 Ahmad Abubakar Sumayya se yan 3 Muzaffar Mu'azzam muzanbil se auta Zahra

Se Amarya Hamdiyya yaranta 3 Aminu samir maimunatu

Se 'kannnashi su 2 Yusuf da Idris matar Yusuf tanada yara 4 kabir jamil Arfat Jidda

Matar Idris tanada yara 5 jafar Samha Nuraddin Zainab jamila

Mahaifin su yarasu tun bayan wasu shekaru se mahaifiyar su Ayna masifaffiyar tsohuwa kenan magana d'aya idan tayi babu canji dole abi takafamusu dokar 'kin auran bare se 'yan gida komin isarka baka isaba Muzaffar shine yafara karya dokar kakarsu shiyasa basa shiri har yanzu

Lokacin da Muzaffar yaje wani ayki Egypt yahad'u da Nabila Allah yad'ura mishi mutuwar son ta bai koma Bihar ba seda Nabila matsayin matar shi lokacin da Muzaffar yazoda Nabila matsayin matar shi babu wanda baiyi mamakiba sabida shi bashida ra'ayin mace cikin rayuwar shi Arfat kuwa tasha kuka kamar ranta zaifita sabida tsananin son datakeyima Muzaffar

Ganin irin son da Muzaffar yakema Nabila yasa kowa yatsaneta cikin 'yan'uwan shi mahaifiyar shi Sarauniya Kilishi ita kad'e takeson Nabila se maimartaba amma baya nuna hakan sabida mahaifiyar shi duk tafi kowa tsanar Nabila

ganin Muzaffar yayi gaban kanshi yasa aka shirya auran sauran 'yan uwan nashi an had'a Mu'azzam da Arfat Mu'azzam yana matu'kar son Arfat amma ita ina hankalinta yana kan Muzaffar har izuwa yanzu tsawon 3 years kenan dayin auran su amma har yanzu babu abinda yashiga tsakaninta da Mu'azzam shi ya'ki tunkararta sabida miskilancin shi ita kuma ta'ki sakin jiki dashi

Shi kuma muzanbil Samha aka bashi wadda tana matu'kar son shi amma shi bata cikin tsarinshi ko kallo bata isheshiba balle wata ma'amala

Sauran yayyan nasu suma haka aka musu amma suna zaune lafiya cikin soyayyar juna

Muzaffar yakasance Soja mai babban matsayi miskili kuma mai zafin zuciya bajin shakkar kowa

Mu'azzam doctor miskili amma mai sanyin hali ga tausayi

Muzanbil Lawyer mai masifar jan aji ga mugun wula'kanci yafifita aykinshi akan komi narayuwar shi

Tunda aka kashe Nabila aka kuma sace yaran data haifa bayan 1 months da haihuwar su Muzaffar yadena shiga harkar kowa dama ya kasance mararson magana yasake zama maizafi akan kowa

Zahra autarsu an auradda ita ga Aliyu yaron ma'kwafciyar masarautar su wato masarautar Yazeed bisa umarnin kaka wanda har yanzu babu wanda yasan dalilin yin haka

Akwai kishi mai zafi tsakain Kilishi da hamdiyya duk abinda jakadiya tagani agurin Kilishi setakaima hamdiyya gulma Hamdiyya tanajin mugun haushin 'yan 3 Sarki watosu Muzaffar sabida yadda sarki yake mugun sonsu duk cikin yaranshi Yusuf yana matu'kar hassada akan sarautar sarki danshi bai'ki yamutubama shi yahau saman kujerar dan acewar shi baiga yaron daya isa yahau saman kujerarba bayan mutuwar sarki ba seshi

Shiko Idris matar shi ita ke zugashi amma dan tashi babu ruwan shi da shi'anin mulki yana d'aukar shawararta sabida yana tsananin sonta

Akwai mugayen munafukai a fada musamman wazirin sarki da wambai

Masarutar Yazeed masarutace mai cike dazalinci izgili da rashin sanin darajar d'an adam 3 dayin auran Zahra ba'kar wahala takesha cikin wannan masarutar babu mai 'kaunarta har shi Aliyu mugun wula'kanci yakemata 'kanwar shi kad'ai take tausayin ta amma ba'a bari ta taimaketa
Chapter 1 · 0% Book details