← Book details Hamshakiyar Uwa Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 34

Sashe 9

Hamshakiyar Uwa Part 2 Complete Hausa Novel · about 4 min read

To haka dai aka ci gaba da shagali, abinda ya ɗaure min kai kalaman da MC ke faɗa in zai ambaci ango ko danginsa, sai ya ce Shamaki Aliyu Ali Baita shugaban rukunin kamfanonin ZEENA. Ɗaya cikin Antys ɗin shi ta zo gurinmu sai ya ce Hajiya A'isha Ali Baita kenan uwar marayu da marasa ƙarfi shugabar ZEENA Foundation. Tofa! kaina ya soma kullewa duk yadda aka yi akwai abinda Yaya ya ɓoye min. Haka da aka zo matakin rawa, sunyi watsi da sabbin 'yan dubu dubu har abin tsoro ya bani. Kuma ga masu kirari suna ta yi wa Yaya Shamaki Ali Baita. Suna faɗin shaharar ɗan kasuwar nan mai kuɗi da ake labari ko kwatance dashi. To haka dai aka kawo wani cake mai mugun girma inda muka yanka ni da Yaya, abin dai zallar al ajabi. Da aka tashi suka shigar dani wani ɗaki aka kawo min abinci, nace na ƙoshi ni dai buƙata ta in je gida inga Ummana tun jiya ban ganta ba. Sukace ai daga goben zaki jima baki ganta ba. Daƙyar dai na ci ɗan cake na sha ɗan lemo. Yaya ya zo yace in zo ya maida ni gida Abbanmu ya kira shi yanzu. Haka dai muka firfito kowa ya kama hanya. A baya na zauna shima haka abokinsa kuwa ne ke kanmu. Ya zura min ido ni kuma na ƙi kallon sa, hardai na kasa jurewa na sa hanuwana na rufe fuskata ina dariya. Yace "Baby ji nake kamar in wuce da ke gidana gobe in an ɗaura shike nan." Na saci kallon sa, dama ana yin hakan? Abokinsa da ke jan motar ya sako baki da faɗin "Za a fara yau." Na dafe bakina cikin kunya. Yaya yace Alhaji Shamsu me ya kawo kunnen ka. Shima ya sa dariya tare da faɗin "Ba da ku nake ba Ango da Amarya." Yaya ya matso daf da ni, ya kwantar da kan shi a bayan kujera yadda har ina jin iskar numfashinsa, a gurin kumatuna, ya ce, "Baby in ɗan taɓa hannunki ƙunshin nan ya min kyau sosai. Na waiwaya na masa wani irin kallo, ya hure ida nuna, na lumshe su gaba na yana wata irin faɗuwa. A cikin kunne na naji kalmar ina son ki Babyna. Na naɗe hannuwa na a ƙirji, domin tsigar jikina naji ta yi wani yarr tamkar zazzaɓi zai rufe ni. Alhaji Shamsu yace zumuɗi. Duk muka sa dariya. Haka muka iso bakin lungun mu.
🖊️🖊️🖊️
*HAMSHAƘIYAR UWA🧕🏻*

*NA*

*HALIMA ABDULLAHI K/ MASHI*

_PAID BOOK_
_Kuɗin karatu ₦600_
_Account number 0700549935 Halima Abdullahi Access Bank a turo shaidar biya ta wannan number 08140004302 ko katin Mtn_
_Phone 08140004302_

*DOKA*
_Ban amince wani ya É—ora littafin nan a wani Social media ba,ko a maida mini shi Audio ba tare da iznina ba yin haka daidai yake da fuskantar fushin hukuma. A kiyaye_

*Masu son a Tallata masu hajarsu suyi magana ta wannan number 09068032427*

*Page 17*

Yace tsaya nan direba mai sa ido. Muka fito shine ya riƙe min rigata ta baya na tsallaka kwata, muka isa ƙofar gidanmu yace shiga ciki zan kira ki anjima. Na shige cike da ɗokin ganin Ummana. Gidan ya cika da Jama a, 'yan ƙauye da na birni. Innarmu ƙanwar Ummanmu ta rugo da gudu ta rungume ni tana cewa ga amarya. Na samu su Umma da su Umman Amina a ɗaki suna ta tattaunawa. Umman Amina ta ce ke 'yan nan dama ɗan gida Ali baita ne mijin naki. Na yi sukuti ina ta sauraron su, suna ta murna. Ni kuma zuciyata bata murna, kuma na kasa gane me yakamata inji farin ciki ko takaicin Aliyu ya min ƙarya. Ina son insan gaskiyar abinda ake faɗi. Na canza kayan jikina Umma tace inje gidan Umman Amina can zamu kwana da su Jamila domin gidan ya cika. Nace to sai inyi salla acan. Umman Amina tace zata aiko mana da tuwo in an kaɗa miya. Nace ina su Amina tace in yi gaba sunje ɗakko markaɗen kunun safe ita da Jamila da Zuhra. Naje Dakalin ƙofar gidanmu na zauna jiran su domin dai abikin nan sune ƙawaye. Sai ga Fati mai Awara, tace "Jamila ina amarsu." Nace ba Jamila bace. Ta zauna "Ashe kece da kanki, haba gaskiya naji ƙamshi duk ya buɗe ko ina, amarya mai maganar zuma, kaga matan manya. Ai munje perty ke kuwa ina kika zaƙulo ɗan gidan Alhaji Baita? mamakin da kowa ke yi kenan Baby." Nace ina ya zaƙulo ni dai, wannan amsar kuma shine zai bada ita ɗan gidan Ali Baitan. Tayi dariya tare da faɗin "Koma dai menene kin dangwalo, yanzu ina zaki." Nace gidan Umman Amina can zamu kwana. Tace "Bari in faɗawa Umman mu sai inzo mu kwana ai duk mune ƙawayen Maimuna ma tun ɗazu ta ke zuwa nemanki." Cikin mamaki nace to sai kunzo. Na bita da kallo ina mamaki wai harda Maimuna yarinyar da ko magana bata min saboda Babanta yafi Kowane uba sukuni a lokonmu. Muryar Jamila ta sa na waiwayo ina kallon su sun taho da bokitai a kansu na markaɗe Jamila tana ta ba su labarin gidan Maman Iman da kuma guraren data kaimu, wai ita tun daga nan ta san dangi arziƙi ne.
Chapter 9 · 0% Book details