← Book details Hamshakiyar Uwa Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 34

Sashe 8

Hamshakiyar Uwa Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da na shiga na sanar da Ummar na bata kuɗin, tace to ai sai kuje da Jamila ko? Na ce shima haka ya ce,nace to kuma wa zai taya ki aiki? Tace ba komai ai 'yan Kurna tun yau zasu zo kin haɗa kayan naki kin cire wanda zaki baiwa Jamilan da su Amina? Nace e nawa ai suna cikin bako Jamila ta kai kusa da akwatuna. Tace to in kunje dai ku kama kanku kar a sake ayi wata rashin kunya." Ƙarfe sha ɗaya ya kira ni yace gashi nan ta turo direba yanzu zai yi sallama da ni.
Muna aje waya É—an sako na shigowa muka yi sallama da umma muka fita.
🖊️🖊️🖊️
*HAMSHAƘIYAR UWA🧕🏻*

*NA*

*HALIMA ABDULLAHI K/ MASHI*

_PAID BOOK_
_Kuɗin karatu ₦600_
_Account number 0700549935 Halima Abdullahi Access Bank a turo shaidar biya ta wannan number 08140004302 ko katin Mtn_
_Phone 08140004302_

*DOKA*
_Ban amince wani ya É—ora littafin nan a wani Social media ba,ko a maida mini shi Audio ba tare da iznina ba yin haka daidai yake da fuskantar fushin hukuma. A kiyaye_

*Masu son a Tallata masu hajarsu suyi magana ta wannan number 09068032427*

*Page 16*

Rantsastsiyar mota ce mai numfashi muka shiga. Na dai san mun wuce gidan gwamna daga nan ban kuma gane ko ina muke ba, sai wani damfareren gida na ga mun shige. Muka bi bayansu zuwa wani falon. yace mu zauna tana zuwa ya fita.

Wata mai kama da Aliyu ta fito, cikin fara'a ta yi mana sannu da zuwa muka sakko muka durƙusa muka gaisheta.
Tace "Ku zauna kan kujera ai ke Antyna ce ta nuna Jamila. Jamila tace gata nan fa. Taɗan zaro ido cikin mamaki tace na zata kece. Jamila tace ni ƙanwarta ce. Na sunkuyar da kai ina mamaki yadda kowa ke ɗauka Jamila ce Yaya ta ko dan ta fini cika ido da 'yar ƙiba. Wata yarinya ta kawo mana kayan marmari da Lemon roba. Ni dai ruwan na sha. Ta kira ni cikin wani ɗaki tace kiyi haƙuri bana raina ki bane ɗauki waccan rigar ki saka ki yafa mayafinta ga shi can. Sai ki fito da takalmin can ki saka in zamu fita. Cikin mamaki nace to. Ta fita na saka doguwar baƙar riga tana ta ƙamshi, na yafa mayafin na riƙo takalman. Jamila ta zaro ido tana faɗin "Kinga yadda ki ka yi kyau kuwa?" Ta fito da makulin mota tace ku muje. A gaba tace na zauna muna tafe tana min 'yan tambayoyi har mukaje wani gida. Ƙamshi tun daga waje. Matar ta amshe mu sai naga ta y i mamaki da tace nice amaryar. Tace wai Maman Iman me yasa baku bata maganin gyara na murmurewar jiki ba? Tace "Nima ban ganta ba sai yau, kuma mun zo a makare, nan zan tafi in barta, ki yi mata komai duk abinda ya kama har ƙunshi dan Allah ki fito mana da ita saboda surutun mutane.

Matar tace baki da matsala sai dai kuma su kwana. Tace "To ba damuwa ko Antyna?" Ta kalle ni. Nace bari dai mu kira Ummanki sai ki faɗa mata. Tace to ku kira ta ɗin. Suka yi magana da Umma sannan ta bani wayar Umma tace a kula da kai sosai in kunga wani abu ba daidai ba ko baku gane ba ku min magana a waya." Nace "To" Na kalli Maman Iman na ce ƙanwata za ayi mata ƙunshinne? Tace "A yi mata mana itama duk abinda take so, amma karfa ta kai amaryarmu kyau. Cikin tsokana ta yi maganar mu kasa dariya.

Nasha azaba a gyaran jiki amma dana kalli fuskata sai da nace nice kuwa. Aka zuba min ƙunshi ƙamshi kuwa sai tashi yake duk inda na motsa. Jamila ma an mata ƙunshi, sai wasu abubuwa da take bani da madara ina sha. Washe gari ta kuma min hayar jiki. Sha biyu sai ga Maman Iman ta rungume ni tana faɗin amarya ta fito, yanzu sai tafiya gurin wankin kai. Tasha mamaki da ta ga gashin kai na da aka gyara har gadon baya.
Tace mu Fulani ne nace a a, amma an ce asalin Kakarmu ta gurin Uba Buzaye ne.
Daga can sai shagon kwalliya acan mukayi salla ta kawo mana abinci muka ci, sannan aka soma kwalliya, ban san cewa yamma ta yi ba, sai da Umma ta kira ni wai ina muke ga mutane sun soma cika gida 'yan zuwa party. Na bawa Maman Iman wayar nace kiji wai masu zuwa gun party sun zo sun cika gidanmu. Maman Iman tace bari in faÉ—awa Ango ya aiko da mota ita amarya daga nan gurin kwalliya zamu wuce. Umma tace shike nan. Ta kira Shamaki ina jin muryar shi yana cewa '"yar uwa wai ina yarinyar nan ne ko muryar ta kin ce bazan ji ba a tausaya min.
Tace "Ba za kaji ba sai kun haÉ—u anjima, ka aika motoci gidan su a kai mutane gurin party yanzu.

Yace "To" suka yi sallama. Ta dube tace "Ni na hana angon ki ya kira ki."

Azuciyata nace na gode Allah da yasa nima ban kira shi ba. Na sunkuyar da kai ina murmushi. Tace nafi son lokacin da zai ganki sai yaga kin canza gaba ɗaya har muryarki ko bata baki wani haɗi ba ne? Jamila Itama aka mata kwalliya ta kawo mana kaya Jamila ma wani leshin Maman Iman ta bata tace kici albarkacin amarya ko za su yi miki kayan cikin nata ne gashi kin fita ƙiba. Azuciyata nace ko da yaushe tasa akayi min ɗinkin ko gwada ni tela baiyi ba. Kamar ta san na saƙa hakan a zuciya tace da kayan ki da kika cire akayi gwaji.

Nace Allah ya saka da alkhairi. Jamila ta saka cif.
Suka shirya ni cikin wata doguwar riga bayanta yana jan ƙasa gashi ta ɗame ni da suka gama komai aka kaini gaban madubi. Maman Iman ta kaini ta ce "Kalle ki." Cikin mamaki nace ni ce haka! Suka sa dariya. Nace ko Umma uwar da ta haifeni baza ta gane ni ba. Suka yi ta ɗaukana a hoto. Nan dai muka nufi mota don ana ta matsawa da kira. Ina bayan mota Jamila a gaba Maman Iman ita ke tuƙi. A harabar gurin motoci na alfarma iya .ganin mutum ta ce da Jamila ta fita ta duba mutanan unguwarmu ko sun samu shiga. In taga waɗan da ba su da pass ta yi mata magana zata sa abarsu su shiga.
Ta dube ni "Amarya ki zauna bari naje mu fara shirya shigarku. Na kuma tsakiyar kujerun bayan tafiyar su ina sake kallon kaina a madubi gaskiya ni kyakkyawar ce a she ko dai don an canza min kamanni ne. Naji a ƙwanƙwasa gilashi Jamila ce ta buɗe tace kinga kuwa 'yan unguwa maza da mata a wajen gate wasu. ma ni dai ina ganinsu ko magana bata taɓa haɗa mu da su ba. Nace kije ki faɗawa Anty Maman Iman in sun shigo arziki ne.
Tana tafiya Yaya na zuwa ya ci wata shadda kalar sararin samaniya, ya yi mugun kyau a zuciya ta nace ashe dai akwai mijin Nobel da gaske. Ya shigo ya zauna kallona ya ke ya kasa magana. Nayi ɗan murmushi, Yaya ka yi kyau sosai. Yace "Baby baki lura na kasa magana ba, gaskiya ne ina son gayu sosai zaki na gyara min jikin ki haka ko?" Na ɗaga kai alamun e. Ya ciro waya ɗan matso muyi hoto. Gabana ya fadi Allah ya sa ba taɓani zai yi ba. Na ayyana a zuciyata. Hularsa da ɗankwalina ne kawai suka haɗu ina jin sautin numfashin sa. Na lumshe ido domin wani yanayi na samu kai na. Cikin murya ƙasa ƙasa yace "Buɗe ido Amaryata ki kalli camara. Na kalleni a cikin wayar munyi mugun kyau. Ƙwankwasa motar ya tsaida ɗaukar hotunan da ya ke yi. Abokansa ne da su Anty. Maman Iman tace "Wai waya ce kazo ne? " Yace Na ga shigowar ki fa, nasan amaryata ta na wurin ki. Nan dai muka fito aka nufi shiga Hall. Yaransu ne aka jera a gaba sun sha wata farar riga bulawus su kuma mazan sun sha shadda mai kalar ƙasa. Sai su Antys da Jamila da Zuhra da Amina suma dai an sako su saboda Maman Iman tace ina ƙawaye na tace gasu nan. Leshi dai suka sa daidai ƙarfinsu amma fa kowacce da kalar nata. Sai abokan Yaya ni yau nataɓa ganinsu.
Hawaye naji yana bin kumatuna lokacin da na kalli gurin da jama ar dake gurin a domin ni, a zuciya ta faÉ—i na ke, Allah na gode maka. Allah ka sa in masa biyayya. Da muka zauna yace kalle ni sai yaga hawaye. take ya rikice ya sunkuyo gurin kunne na yace. "Baby me akayi ba daidai ba? Kukan me ki ke yi ne amaryata."

Na motsa baki zanyi magana sai muryata ta soma rawa, yace "To karki yi maganar, ya kai hannu ya ciri hankici a aljihunsa fari tas yasa hannu ya dafa ɗankwali na ta baya yana tsane hawayen fuskata cikin lallashi yana faɗin haba soyayyata zaki ɓata gayunki mana." Na ware idanu ina kallon fuskar shi a zuciya ta ina godiya ga Allah daya min baiwar miji irin wannan. Ya ɗakko ZEENA table water ya tsiyaya a kofi ya bani. Yana faɗin "Sha masoyiya." Sanyinsa ya ratsa maƙogwarona dai dai lokacin da MC yace " Kai Don Allah ku tafawa Ango da Amarya haƙiƙa zai iya kula da amaryar nan tasa da kyau. Sai mukaji tafi da sowa sam na manta akwai mutane a gurin duk zatona mu biyu ne sai sautin dake tashi, na manta da akwai dubunan jama'a da ke gurin.
Chapter 8 · 0% Book details