← Book details Hamshakiyar Uwa Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 34

Sashe 11

Hamshakiyar Uwa Part 2 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Kuma shi zan aura inyi rayuwa da shi cikin yanayin akwai ko babu. "Ya matso daf da ni. Yanzu ma dashi zaki rayu Baby ni yaron Alhaji Baita ne amma ba ɗan daya haifaba, ɗan jire kanti ne." Na juya muna fuskantar juna.ka tabbata? Yace "Na tabbata kuma zan tabbatar miki da zarar an gama bikin nan." Na sauke ajiyar zuciya tare da faɗin to duk kashe kuɗin nan da ake yi fa? Kuma a katin gayyata ka ɗora sunan Ali Baita. Ya ƙara ƙasa da murya. "Ba zan iya hana su kyautata min ba Baby, saboda mun zama ɗaya da su mutanen kirki ne hatta katin su suka buga sai ganin shi na yi. Kuma don Allah kar ki damu kanki kar ki saurari kowa abinda na faɗa miki kawai zakiji, ko mutane sun yi wata magana duk hasashe ne. abinda ni na faɗa miki shine kawai zaki y arda da shi kinji ko?" Na sunkuyar da kai nace To. Ya sauke ajiyar zuciya, "Yawwa amaryata, amma fa kin ɗaga min hankali da ace ni ɗan cikin Baita ne yanzu shike nan gobe sai a fasa aurenmu?" Na turo baki tare da faɗin e mana, haƙura zanyi. Ya yi ' yar dariya maimakon kiyi murna kin samu mai kuɗi." Nace taɓ aini bana ra'ayin auren mai kuɗi gara ma in muna tare kayi kuɗin, ance suna da wulaƙanci ga sakin mace ayi ta mata gori, arziki, kaga kaina ka rabu da matanka har kashi uku kaga kuwa dole in yi ta kaina. Haka iyayen ta ba a basu daraja dan suna talakawa. To da in aure ka ka sake ni Yaya gara ba muyi auren ba. Ya ɗan yi shiru. Can yace "Baby da aure da saki iri daya ne da mutuwa, nasan kina damuwa ne saboda na saki mata har uku, kar ki damu da wannan ke dai ki yi aure bautar Allah ,kuma Baby ni da ke alkawarin da zan miki duk juyi bazan sake ki ba, kema ina son ki yi min alƙawarin cewa duk wahala bazaki guje ni ba." Cikin sauri nace na yi maka. Yace to "Mun kashe wannan wutar gobe kamar haka kina gidana jiya Abba ya kira ni zancan kafi na kayan ɗakin ki. To jiyan ana fenti ne yau kuma mun tashi da perty , amma gobe bayan ɗaurin aure sai akai kayan ko?" Nayi murmushi Wannan maganar ku ce ta manya. Yace "Haka ne, to ga kaji nan a leda da madara da sauransu don Allah ki ci ki ƙoshi kinji?" Nace kai ka ci abinci? Yace "Hajiya a baki yau ta bani fura wai tun jiya banci komai ba kamar wani ɗan ƙaramin yaro ta ajiye Ni ta bani." Muka sa dariya. Nace kai ɗan gatan Hajiya ne. Yace "Ke 'yar gatana ce, zauna in baƙi a bakin kema." Nace'A'a. Yace "To shike nan ki koma ciki ki ci sosai don Allah Alhaji Shamsu ya kawo ni yana jirana dan ya koma gurin iyalinsa da wuri." Nace wai dama kana da Abokai? Yace "E mana duk zaki san su a hankali." Na ɗauki ledar na shiga ciki, shi kuma ya wace, na dawo ina leƙenshi ya tafi da sauri. Yanzu kam hankalina ya kwanta koda ƙarya ya yi min."
Jamila ta tare ni da faÉ—in "Me muka samu ne?" Nace Yaya da abinsa wai yasan banci abinci ba shine ya kawo min naman kaza. Nan fa suka É—auki sowa da guÉ—a suna faÉ—in wannan ango yana ji da ke. Kaji uku ne nace Jamila ta cire É—aya ta É—auki madarar ta haÉ—a ta kai wa su Umma, na É—auki nawa nace Amina ta raba musu. Muna gamawa sai ga mutane sun shigo da guÉ—a wai za ayi kamu, suka fesa min turare irin dai yadda ake yi a al'ada aka gama kowa ya watse sai mu 'yan kwana.
Cikin dare bacci ya ƙaurace min wai gobe zan zama matar aure, na ɗakko waya ta ina kallon hotunanmu da Shamaki, faɗin cewa na dace ma ƙauyanci ne, Allah ne kawai ya bani shi ba wayona ko wata dabarata ba a kyan fuska duk da yana namiji ya fi kuma ko da ina mace ban san a gaba ba, amma ni da kaina na san bani da wata ƙira mai ɗaukar hankalin maza ɗan gara ko daga sama. Wata zuciyar ta ce gobe kamar yanzu muna tare da shi. Gabana ya fadi ni ba ƙanƙanuwar yarinya bace na san meye aure duk da bansan shi a zahirance ba, dole inji fargaba ban sani ba ko ina da budurcin da ya tambaye ni ko babu.

Sai dai ina da tabbacin ban taɓa zina ba. Ni dai har kiran sallar farko idona biyu ina ta saƙe saƙe daga binasi bacci ya ɗauke ni. Da safe na yi wanka cikin shadda Maman Iman ta kirani ta ce ta turo direba zai kaini gidan kwalliya. Na sanar da Umma tace to muje da Jamila amma karmu jima kafin ɗaura aure mu dawo.
Yau ɗin ma dai kamar jiya, tsara min kwalliya tamkar wata 'yar tsana. Ta bani wasu kayan tace inyi canji cikin wani ƙaramin akwati sai wata leda mai ɗauke da sarƙoƙi a jikin ledar an rubuta DIJANGALA ENTERPRISE. Kenan acan suka sai min. Ta sa direba ya ɗakko mu. Layin mu cike da mutane da motoci ya tsaya nesa kaɗan da lungunmu dan ba gurin fakin, muka sauka mukayi masa godiya muka nufi lungunmu. Jamila ta ce "Yaya Baby kalli ƙofar gidan Abbansu Zuhra ki ga motoci kuwa.?" Nace kinsan ɗan kasuwa in yana da mu'amala da mutane za su zo masa. Tace "kin dai ƙi yarda." Nace wai bana faɗa miki yadda muka yi da shi ba a jiya, amma kina ta musu, ki barsu in an kaini sun ga gidansa sai su samuwa kan su lafiya. Mutane sai kallona suke masu min Allah ya sanya alkhairi suna yi har muka shiga gida. Ya cika ɗajim da mutane sai kallo ya dawo kaina.

Ƙawayen dolena suka shigo duk sun sha wanka, sai ga mai hoto da me ɗaukar bidiyo aka shiga ɗaukar hotuna. Can Jamila ta miƙo min wayata "Kina da saƙo daga ango." Na duba da sauri, "Alhamdulillah! Alhamdulillah!! Alhamdulillah!!! Na zama mijinki Baby." Na ɗago a sanyaye na kalli Jamila, idanuna suka cika da hawaye, ta ce "menene"? Sallamar Abba ce ta sa na maida kallona gareshi, yana faɗin "Alhamdulillahi an ɗaura Allah ya basu zaman haƙuri. Sai hawayen suka kwaranyo bazan iya fassara ko kukan menene ba. Jamila ta ce "Kingani zaki ɓata kwaliyarki ke da ki ke ta zumuɗin zaki auri Yaya meye na kuka?" Nan abokan wasa suka taso ni a gaba. Jamila ta dubi Abba zai fita ga mai hoto ana ta ɗauka. Tace Abba don Allah zo a mana hoto." Sai akace a kira Umma. A nan kam ban jure ba sai da na zubar da hawaye sosai hoton har su Jafar da Baba Habu ƙaramin mu ga cikin Ummanmu.
Jamila ta jani ɗakin Umma na canza kaya ta ɗan goge min inda hawaye ya min jirwaye a fuska. Muna fitowa sai tankani ake yi dan kyau. Atamfa ce mai adon zaiba, ta ɗauki ɗinki. Lokacin aka ce ga angwaye za su shigo su yi gaisuwa a yi hotuna. Nan naga munafircin mata. kowacce ta maido hankalinta ƙofar shigowa.

Yaya da Abokansa ƙamshin su ne ya fara shigowa kafin su shigo, ya yi kyau cikin shadda mai ruwan siminti tsananin kyan shaddar shine ya bayyana tsadar ta.
Chapter 11 · 0% Book details