Sashe 6
Hamshakiyar Uwa Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Take fuskata ta canza zuwa murmushi, na shiga kalle-kallen ko zan iya hango shi Mijina. Sai dai har na sakko Jamila ta zo da gudu ta amshi kyautukan ban hango shi ba. Daga nan sai malamai suka gabatar da asusun makaranta domin neman taimako. Kabbara da naji an ɗauka ita ce tasa na ɗago kai na dubi ta kusa da ni nace menene? Tace "Babban baƙon da aka gayyato ne ya ke jawabi cewa ya bada Miliyan uku ayi gyaran makaranta." Sai na sa hankalina a gurin ina faɗin gaskiya ya taimaka. Sai naji yana faɗin "Wannan yarinyar mai albarka Allah ya yi mata albarka tare da iyayen ta wadda ta zo ta ɗaya ga sheda da ta samu ta ladabi haƙiƙa ta zama abar alfahari ce." Sannan ya ci gaba da fadin "ina yarinyar tazo nan. " Malam ya zo da sauri ya tasani. Kyakyawan Basarake ne yana zaune cikin shigarsu ta sarakuna yasha gilashi baƙi. Na durƙusa a gabansa. Yace yarinya zaki ci gaba da karatu ne? Na zuba masa ido kenan abin nawa ya kai duk wanda ya yi magana sai inji muryar sa irin ta masoyi na. Malam yace "Aure za ayi mata ranka ya daɗe kunya ta ke ji shi yasa ta yi shiru." Ya ce "To Allah ya albarkaci auran mun zaci zakici gaba da karatu ne mu faɗa miki zamu ɗauki nauyin karatun. Amma tunda ance aure za a miki to in mahaifanki suna wannan guri muna saanar da su cewa zamu sai miki kayan ɗaki da kayan da duk wata gara. Allah miki albarka Ya sa ki yi amfani da abinda ki ka karanta, kuma muna yi miki nasiha da ki bi mijin shima ya shede ki kamar yadda ki ka samu sheda daga Malaman ki . Su kuma sauran yaran da suka ci jarabawa zamu basu dubu ɗari ɗari. Ragowar yaran da suka yi sauka kuma za su rabauta da naira dubu ashirin ashirin. Ta ke aka soma kabbara. Daɗi ya rufe ni addu'a na ke Allah ya sa ba mafarki na ke yi ba. Allah mun gode maka ya kawo mana mafita ni da iyayena. Babban baƙon shine ya miƙa mana allunanmu aka ɗauke mu hotuna. Lokacin da zai bani nawa sai na ji ya ce abar alfahari kin na tabbar mijin ki in yana nan to yana cike da farin ciki da godiya ga Allah. Na zubawa fuskarshi ido muryar Aliyu na ce. Malam ya min tsawa wai in wuce, Sannan ya basu kuɗaɗensu a Envelope ni kuma ya ce a bashi lambar wayar mahaifina. Malam ya sa lasifika ya ce in Mahaifin Rabi'atu Abubakar yana gurinan ya iso nan ana son ganin shi. Abba yazo cikin murna suka gaisa da babban baƙo yana ta godiya sannan Abba ya yi godiya ya bada lambar waya inda wani da ke tsaye da wayoyin babban baƙon ya amshi lambar ya saka a ɗaya daga cikin wayoyin. Suka tafi malamai suka raka su gurin wasu manyan motoci.
Haka dai sauka ta tashi ana ta farin ciki da murna a gurin . Su Umma abin ba a magana. Ni kam tun kafin mu ƙarasa gida na amshi wayar a hannun Jamila na soma kiran layin Yaya. Na kira ya fi sau goma amma ɗan tahalikin nan bai ɗauka ba. Na ja tsaki na miƙawa Jamila wayar. Tace "Wai ke duk wannan alkhairi da ya same ki a yau amma har yanzu kina ƙunci." Nace dole in yi ƙunci baizo ba fa. Jamila tace "Ya zo mana." Cikin sauri nace kun haɗa ido? Tace "A'a amma ga kyauta ya bayar?" Nace zai iya aikowa. Nima zan fara gwada mishi nawa rashin kulawar tunda haka ya zaɓa. Jamila tace "Kamar zata iya." Nace zaki gani kuwa.
Labari fa ya watsu a unguwa sai murna ake zuwa taya Ummanmu. Da dare ina jin Abba yana cewa Umma kinga dai abin Allah ko? Tace "Wallahi Ubangiji ya share mana hawaye, wannan lamari Allah muna godiya a gare ka." Muka shiga ɗakinmu. Jamila tace ki buɗe mana kyautar ango mugani mana. Na tura mata kwalin ke ki buɗe, domin ni ita kanta kyautar haushi take bani. Wani kyakkyawan siririn agogo ne mai kyau ruwan gwal, sai wani zobe kamar na azurfa yana da jan dutse shi mai kyau. Ga ƙaramin ƙur'ani mai girma izu sittin, ga kuma wani kyakkyawan carbi mai ruwan gwal. Take na ruɗe ina ɗaga kayan cikin farin ciki. Jamila ta sa dariya tare da faɗin "Kin daina jin haushin kenan?" Nace ai ba haka bane, ƙur'ani mai girma fa ya bani ya bazanyi murna ba. Haka dai har muka kwanta ban samu wani kira ko saƙo daga mijin da zan aura ba.
Hajiya ta fito daga cikin ɗakinta ƙarfe uku na rana taɗan matse bacci kafin la'asar. Idanunta suka sauka akan yaranta sun baje a falonta suna ta hira, ga alamu sun gama cin abinci domin Juma tana ta gyaran gurin. Duk suka miƙe suna yi mata sannu da fitowa. Ta amsa musu bayan ta zauna, tace "Ashe kun jima kuna jirana, yau wani bacci na ji tun da nayi azahar na shiga ciki. Maman Nana tace Ai kuna shiga ciki na iso, Juma ke faɗa min sai kuma ga su suma. Hajiya ta kaɗa kai cikin isa Tace "Marabanku da zuwa suka amsa. Ta kalli wasu lesuka dake zube kan kujera, tace muga kayan can na waye?" Maman Iman tace nawa ne siya na yi zan baiwa Ango shine aka ce tuni an kai lefen. Shine zan ɗinke kayana. Hajiya ta ciro daga leda ta taɓa jikin leshin. "Ina kika samu wannan leshin kayan London ne ko har can ki kayi Oder?" Maman Iman Tace 'a'a akwai DIJANGALA ENTERPRISE sune suke shigo da su, kayan su suna da kyau kuma Hajiya ga ta da farashi Hajiya tace "Mace ce mai kamfanin?" Hajiya ta tambaya tana ƙara taɓa jikin leshin. Maman Umar tace E, mace ce. Hajiya ta gyaɗa kai tare da faɗin Allah ya dafa mata. Ina son inga mata suna dagewa da kasuwanci, ki duba min lafaya irin waɗanda kika san ina so kamar kala goma sai ki turomin. Maman Umar tace bamu da su a kasuwa ne?" Hajiya tace "Karfafa mata gwiwa zanyi ga kayan suna da kyau." Maman Nana tace Ni dai sarƙoƙin zaki turomin in duba.
Suka gama tattaunawa tare da yaba kayan DIJANGALA ENTERPRISE. Hajiya tace "Lafiya na ganku kamar kun haɗa baki ku duka?" Maman Umar Wadda tun fitowar Hajiya ta ke saƙa da warwar kan tunanin ta inda zata fara magana saboda Shatima ya kirata ya sanar da ita komai. Tace Hajiya mun zone a tattauna akan bikin nan. Hajiya ta bita da kallo wanda sai da ta sunkuyar da kai haka ya sa kowacce ta shiga taitayin ta. Duk sukayi tsit saboda irin kallon da Hajiyan ta yi wa babbar su. Hajiya ta soma magana cikin isa. "Sanin kanku ne bana son a yimin ƙarya ko da kuwa yin haka shine zai ceci rayuwata ko? In ba zaku faɗa min abinda ya kawo ku ba kuna iya tashi ku tafi gidajen mazajenku. Na san komai game da abinda kuka tattauna, haka zalika nasan Shamaki ya sanar da ku cewa na sani. To menene abin wani ɓoye ɓoye, bakwamin adalci fa, ban yi muku tarbiyya akan rashin gaskiya ba fa."
Duk suka durƙusa a gaban ta suna neman afwarta. Tace "In har maganganun da yazo min da su na al'adar da nake gabatarwa ce to in baku son ranku ya ɓaci ku rufe zancan, sannan ku ɓace min a nan, haka nake ra'ayin tsarin gidana ku bari in na mutu sai ku canza ku yi duk irin yadda ku ke buƙata.
🖊ï¸ðŸ–Šï¸ðŸ–Šï¸
*HAMSHAƘIYAR UWA🧕ðŸ»*
*NA*
*HALIMA ABDULLAHI K/ MASHI*
_PAID BOOK_
_Kuɗin karatu ₦600_
_Account number 0700549935 Halima Abdullahi Access Bank a turo shaidar biya ta wannan number 08140004302 ko katin Mtn_
_Phone 08140004302_
*DOKA*
_Ban amince wani ya É—ora littafin nan a wani Social media ba,ko a maida mini shi Audio ba tare da iznina ba yin haka daidai yake da fuskantar fushin hukuma. A kiyaye_
*Masu son a Tallata masu hajarsu suyi magana ta wannan number 09068032427*
*Page 15*
Su ka yi ta ba Hajiya haƙuri,
ƙarshe dai ta haƙura amma fa ba"a tado da zance ba. Sai dai suka ɓige da tunanin yadda za a gudanar da taron bikin. A'isha ta ce gaskiya ayi Dinner su shirya koma i iyaka su ɗakko amarya kawai, Maman Iman tace haka za'ayi dan ya ɓoye mata ai kuma ranar wanka ba sauran wani ɓoyo cibiya tunda nan gidan za'a kawo ta zai ci gaba da ɓoye mata ne? Maman Umar tace kwarai kuwa domin duk abinda ya ke son ya samu ko ya sani nasan dai zuwa yanzu ya sani. Haka dai suka kira manajan ZEENA Event center suka sanar da shi suna da Dinner ranar asabar in sun karɓi kuɗin wasu to su mayar masu.
Suna gama shirya komai Hajiya tana jin su. Suka kira Shamaki suka faÉ—a masa yace "Duk yadda kuka ce haka za ayi, amma da kun bari sai an kawo ta É—akin ta sai a yi Dinner É—in.
Maman Umar tace a a ayi Dinner ranar Asabar ,Lahadi a ɗaura aure, Monday taron Hajiya. Yace shike nan sai ku buga mata katin da zata baiwa ƙawayenta da na shiga gurin Dinner ɗin." Ba matsala wannan ta katse wayar bayan ta faɗa masa hakan. Hajiya tace sai ku ɗinka wa amaryar kayan da zata saka a shagalin." Maman Iman tace kubar komai na shirya amarya a hannuna. Suka ce mun bar miki dama kece 'yar gayu. Ta ɗaga waya ta kira DIJANGALA ENTERPRISE ta faɗa mata cewa zata turo mata hotuna wasu lessis cikin 'yan Swizaland ɗinnan ta turo mata su zata saka kudin yanzu.
To haka dai suka yini har kusan magriba sanan suka watse.