Sashe 23
Hamshakiyar Uwa Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Na rakota zuwa falon Hajiya ta yi wa Hajiya sallama Hajiya tace "Har zata wuce to kin bata ruwa ta sha kuwa?" Nace na shafa'a sauri take daga asibiti ta ke. Jamila na fita zan juya Hajiya tace "To me tazo yi kenan haka?" Nace saƙo na bata. Tace "Amma banga komai a hannun ta ba?" Har zan ɓoye sai na tuna da maganar Juma da ta Shamaki, game da faɗan gaskiya, sai nace kuɗi ne na bata zata kai wa .Abbanmu asibiti. "Ina kika same su?" Ta jeho min tambaya da sauri. Nace abokan shi suka bani ranar da aka kawo ni. Tace "Kin ce abokan shi, shi wa?" Na fara gajiya da tambayoyin ga halin da nake ciki sai na soma hawaye cikin rawar murya nace Shamaki. Ɗa gyaɗa kai tare da faɗin "To na gane, shi kuma kukan na menene?" Na share hawaye tare da girgiza kai nace ba komai. Ta maida kallon ta ga TV na wuce ciki zuciyata fal da takaici.
Haka azahar da la'asar suka riske ni a gurin ba wani labari a halin na faɗawa Jamila zan ke kira ina samun labarin halin da Umma take ciki amma kona kira bata ɗagawa. Shima Abba shiru, shikuwa mijina fushi ma nayi ban ƙara gwada wa ba. Addu'o'in dai ba irin wadda bana yi.
Sautin wayata ya sa na tashi da gudu na nufi ɗalkota ina dubawa Shamaki ne, na zauna a ƙasa ina kallon wayar harta yanke, ya sake kira har lokacin ban ɗaga ba. Gani nake babu wani amfani ko na ɗaga. Karan da wayar ta addabe ni da shi ya ci gaba da kirai shi ya sa dole na ɗaga amma ban iya magana ba na kara a kunne Yace "Baby Ina meeting a Abuja lokacin da ki ka kirani yanzu ina filin jirgi nan da minti talatin ina Kano me ya faru?" Na saki sabon kuka, cikin muryar da na yi kuka na gaji nace Umma ta mutu ina ta kiranka baka ɗaga ba ƙilama yanzu an kaita. Yace "Wace Umma?" Nace Ummanmu na kashe wayar na ɗora sabon kuka.Ni na gama yanke wa tunda suka ƙi ɗaga wayata bashakka Umma ta mutu na rasa ta har abada.
Shamaki ya yi tsam a filin jirgi ya É—aga waya ya kira Number Abba. Abba ya É—aga Shamaki ya gaida shi cikin girmamawa, sannan yace "Yarinyar nan ce ta kira ni tana min kuka
"Wai da gaske ne Allah ya yi wa Umma Rasuwa?" Abba yace Baby akwai ruɗaɗɗiyar yarinya, shiyasa ban so Jamila ta faɗa mata ba. Kuma shine dalilin da ya sa nace karsu ɗaga kiranta.Ummansu addu'a take buƙata, bata rasu ba yanzu dai sun ce mu tafi asibitin Malam Aminu Kano. Aiki ne za'ayi mata. Shamaki yace Abba ina ganin ku tafi asibitin Zeena Hospital zan sanar da likitan kafin kuje ya ɓuɗe mata fayal.
Abba yace alhamdulillah na gode Aliyu Allah ya sa a mizani. Yace ba komai sai munzo asibitin.
Ban kuma ji daga kowa ba har magariba.In
Kwance inda nayi salla. Juma ta shigo da abinci ta ga na rana yana nan. Tace "yannan ki daure ki ɗan taɓa mana." Nace Baba Juma karki aje haɗa duka bazan iya ci ba. Tace "Banga laifin ki ba yarnan Uwa ta wuce wasa. Kuyi addu'a Allah ya fisshe ta. Nace Ameen. Yau ce ranar farko da na ganshi ya shigo a irin wannan lokacin.
Ban Ko É—ago ba bare in dune shi. Ya tsugunna a gaba ya sa hannu ya É—ago ni fuska ta ta yi suntum yace "Subhanallah Baby kinga fuskar ki kuwa? Na soma sabon kuka ya rungume ni ki samu natsuwa, ki shirya muje Asibitin mu duba ta. Nace bata mutu ba?
Yace ta samu sauƙi muje
ki tabbatar Na tashi da sauri na shiga ciki na wanko fuska na saka Hijabi yace "A' a ki canza shiga mai kyau, sannan ki ci wani abu naji tace haka ki ka yini.
Nace zan canza shigar amma abinci kam ka min afwa sai na ga jikin.
A falon Hajiya mun rusuna ya sanar da ita cewa mun fito. Tace Juma ta haÉ—a abincin da za'a kai asibitin.
Muka fita tana cewa mu yi mata sannu.
Muna baya Bala direba ya na jan mota muna baya ya sarƙe
hannuwanshi cikin nawa har muka kai Zeena Hospital. Nace
ba Murtala aka ce ba ? Yace "Ƙila daga can aka turo su nan." Muka shiga ni dai da kyar nake cire ƙafa, ban damu da gaisuwar girmamawar da Nurse ɗin ke yiwa Shamaki in mun haɗu da su jifa jifa ba. Ya kira yaawar wani yana tambayar sa da turanci lambar ɗakin. Ya faɗa masa har mun ɗan wuce sai muka dawo baya. Abba na zaune bakin gadon da Umma ke bacci ya riƙe mata hannu da ake yi mata ƙarin jini.Kan tabarma kuma Jamila ce da Umman su Amina.
Da sauri naje na riƙe mata hannu Abba ya ce ai bata farka ba ,bayan anyi aikin. Na dubi Abba da sauri nace wai dama aiki aka mata. Ya ce "aiki aka yi mata 'yan ta wahala kukan ta ɗaya da aka ciro ta ta koma ga Allah." Allahu akbar, ina take Abba. Yace "An rufe ta ɗazu nan kafin magriba ita kuma sai mu yi fata Allah ya bata lafiya." Muka amsa Shamaki suka gaida da Abba ya masa ya maijiki daga nan yace zaije ya duba wani ya dawo,ya fita .
Abba ya ce ki bi mijinki sau da ƙafa dubi abinda ya yi mana banda shi da sai dai Ummanku ta mutu domin bani da kuɗin da za a yi mata aiki. Na dubi Abba shine ya biya? Abba yace komai da komai. Bala direba ya shigo da kayan abinci Jamila ta amsa ta na yi masa sannu, suka gaida da Abba ya tambayi mai jiki sannan ya fita. Shamaki suka shigo da likitan na gaida shi. Likitan ya yi bayanin cewa saura minti arba'in ta farka anyi aikin cikin nasara kuma zata tashi lafiya lau. Sai yanzu na haɗiye wani tarin abu da ya maƙale min a wuya. A fili na furta Alhamdulillah yace da ta farka kar su bata komai su sanar da shi.
Shamaki yace zamu tafi sai kuma gobe zamu sake zuwa. Nace ya barni in kwana,wata tsawa da Abba ya buga min bansan lokacin da a nayi waje da sauri ba.
Muna zuwa gurin mota Sahamaki ya ba Malam Bala kuÉ—i yace ya hau mashin ya wuce gida bari shi ya ja motar zamu biya unguwa ne.
Na koma gaba ya ja muka tafi. Kawai gari muka yi ta zaga wa muna hira yana É—an Min wasanni, mushiga wannan Supar market yace in É—auki abinda nake so har goman dare sannan muka nufi gida lokacin zuciyata ta yi sanyi ta cika da nishaÉ—i.
Muna shigowa Azima tana shafawa Hajiya maganin ƙafa duk suka bimu da kallo, na ajewa Hajiya ledar hannu na domin naga tana kallon ledar. Tace Menene? Shamaki ya ce turarene mun biya na sayi nawa ne shine na sai muku,ta sa albarka ta tambayi yana yi jiki muka ce da sauƙi. Nan da na barsu na tafi ɗakina. Na yi salloli sannan na shiga wanka na shirya na nufi ɗakin mijina.
Washe gari da safe da ya shigo daga gurin Hajiya zai yi shirin kasuwa nace zaka sa a kai ni asibiti ne ko in zaka kasuwa ne zaku sauke ni?
Yace jirana ake yi bazanbi ta can ba,amma game da naki zuwa ki tambayi Hajiya inta ce ki je zata sa a kai ki. Na yi sororo ina kallon sa kamar in ce Hajiya nake aure?Sai kuma na fasa na fita zuwa gurin Hajiyar irin tambaya tun yana gidan.
Na rusuna na sake yi mata sannu da hutawa, sannan nace Shamaki ne ya ce in tambaya ko zani asibiti? Jin shiru ya sa na ɗago na dube ta itama ni take kallo a zuciyata ta nace kema dai Uwa ce kinsan zafinta. Ga mamaki na sai baki tace ki je ki buga musu yawa kiji lafiyar ta, babu buƙatar zuwanki. Na rusunar da ƙwayar idanuna sannan na miƙe tare da furta to. Ɗakina na koma na zauna a kan gado na ɗora sabon kuka. Ina jin shigowar shi ban ko ɗago na kalleshi ba , ya zauna kusa da ni yana tambayar abinda ke faruwa. Nace ba komai. Yace "Hajiya ce ?" Nace 'A 'a . Ya miƙe tare da faɗin shike nan ni zan tafi kasuwa, na miƙe ina share hawaye na amshi jakar kamar kullum domin yi masa rakiya.
......
Na raka shi har falon ƙarshe ya amshi jakar ya ɗago fuskanta ki daina kuka ya kawo bakin shi kunne na ya raɗa min cewa zanbi ta asibitin zan kira ki in faɗa miki yadda jikin yake kinji?" Nace To kace cewa Umma don Allah ina son zuwa ban samu dama bane ina son in ganta kuma ina yi mata addu'a .
Wasu hawayen suka biyo kumatuna, ya sa hannu ya share yace "zan haÉ—aku da ita a waya. Nace to. Yace "Share hawayen ki" Nasa hannu na share sannan ya fita ni kuma na dawo, zan wuce nace cewa Hajiya sannu da hutawa. Ta amsa da "Yawwa."
Haka na koma ciki naci gaba da 'yan ayyuka na. Na gama na koma na kwanta . Gurin ƙarfe goma sai ga kiran shi na ɗaga. Yace gani a Asibiti jikin Umma ya yi kyau sosai ki je video call zan kira ku gaisa. Da rawar jiki na shiga video saiga Umma zaune tana min magana cikin murna na gaishe ta, nace ya jiki? Tace "Jikin da sauƙi Alhamdulillahi ya naki jiki?" Nace na samu sauƙi. Tace "Ki daina kuka akan sai kinzo tunda ba daɗin jikinki ki ke ji ba, sannan ki yi godiya gurin Hajiya surukarki muna ganin aiken abincin safe da yamma Allah ya ƙara ɗaukaka." Nace to zan faɗa mata, yanzu dai babu inda ya ke miki ciwo? Ta ce. " Babu inda ke min ciwo Baby ki kwantar da hankali ki, ki ƙaraiwa mijinki godiya ya taimaki rayuwata sosai." Nace To Umma. Muka yi sallama.