Sashe 20
Hamshakiyar Uwa Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Masu hotuna da bidiyo ana ta ɗauka gaskiya ni tsarin ya yi min, wata zuciyar tace tunda kin tsallake Hajiya ta ci kyace abin ya birge ki mana. Haka dai aka ci aka sha sannan aka gama. Aka kai wa Hajiya abin magana zata yi jawabin godiya amma kafin haka sai ƙawarta Hajiya Zulaiha ta amsa ta isar da saƙon Hajiya game da abincin da amarya ta ciyar da su, tace "Zan yi ɗan bayani kaɗan kafin Hajiya ta yi godiya, gaskiya amarya girki ba laifi amma a ƙara gyara hannu sosai, ta ɗan taɓa baki, ya yi daɗi sai dai ɗan gyara guda biyu dazan miki, na farko ɗanwake mai da yaji ne sai kika bamu da miya. Na biyu kin mana ɗan zubi a dambu sai ki ƙara sakin hannu kaɗan saboda rowa bata da wani amfani kuma bata cikin sunnar gidan nan. Na sunkuyar da kai, ina mamaki amma duk da haka ni ce da godiya tunda ƙorafin ya tsaya a haka,,Hajiya ta ci abinci Allah ya soni ni.
Hajiya ta amshi abin magana tayi godiya ga kowa tare da fatan duk za su koma gidajen su lafiya.Sannan ta sa albarka tare min fatan zama jarumtar mace musamman gurin yi wa miji biyayya. Aka abin maganar wai ince wani abu bani wai nima in yi godiya. Gabana yana faɗuwa na amsa. Nace Mun gode Allah ya maida kowa gida lafiya, kuma insha Allahu zan yi amfani duk shawarwarin da aka bani zan kiyaye. Haka taro ya tashi kowa na san Barka. Ana tashi aka kira la'asar. Hajiya ta kirani inyi sallama da baƙinta. A lokaci ne wannan mai cewa ina da rowar same ta tana cewa "Hajiya Zeena duk matan da ke Kano amma Shamaki ya rasa wadda zai ɗauka sai wannan cokokuwar ko cikin 'ya 'yanmu ya kasa zuwa ya duba. Na kalli Hajiya lokacin da takecewa
"Bar ɗan yau da abinda ya ke so Hajiya Zaliha. Wani mugun so ya ke yiwa yarinyar nan ba domin na samu tabbacin ba asiri suka yi masa ba da a haka zan kalli abin. Gaggawa fa ya yi aka je aka nemo masa auren ta. Ni kuma kinsan matsala ta, ina son ɗana da yawa kuma ya rayu akan samun duk abinda ya ke so, in ba ɗana abinda ya ke so matsawar yin hakan ba saɓon Allah bane." Nace su sauka gida lafiya na juya raina ba daɗi, na soma jin takaicin kushe min halitta da ake yi. Gefena tanƙam da 'yan uwa da 'yan unguwa sai kallo na suke suna min murna. Na zauna bakin gado Jamila ta zo ta ce "Abinci ya yi daɗi Yaya Baby kuma ke ki ka dafa?" Na ce e mana. Wayata ta soma ringin ta miƙo min. Na amsa Mijina ne Hajiya ta hana ni faɗa masa Yaya To bansan wane suna zan saka masa ba. Na ɗaga, yace " Yaya Baby gaske ne ke kika dafa abincin nan?" Cikin shagwaɓa na ce wai don Allah nice Yaya? Yace "Ina son yadda su Jamila suke faɗa ne." Abicin bai yi daɗi bane ko? Na tambaye shi. Yace "Inji wa, ai in faɗa miki abincin Hajiya ne kaɗai ya fi naki daɗi." Na yi murmushi a zuciya ta nace ai ita Hajiya komai nata ya fi na kowa. "Sannu soyayyata ,kin yi ƙoƙari sosai.
.....
Yace "Yawwa Baby amma Hajiya ta ci abincin kuwa?" Nace ta ci mana har ƙawayenta duk sunci. Ya ce to Alhamdulillah! Allah ya yi miki albarka me ki ke so in zo miki da shi?" Na yi ƙasa da murya kai kawai nake son ka dawo lafiya bana son komai.
Sai kurum na ji sumba a kunne na tare da faɗin ina sonki da yawa zan faɗa miki wani abu amma don Allah kar hakan ya sa ki canza min." Nace ka faɗa min Allah bazan taɓa canzawa ba. Yace "Baby idan yadda nake ji a game da ke shine soyayya, to a baya ba soyayya na yi ba, duk bugun numfashi sai na tuno ki,na samu kaina da hirar ki da kowa harma da waɗanda ba su kamata inyi hirar da su ba. Don Allah Baby kina jin makamancin abinda nake ji?"
Na sauke ajiyar zuciya, zanfi son in faÉ—a maka idona yana kallon na ka, in ka dawo wannan hirar za muyi. Ya kuma sumbatar wayar ba tare da ya kuma cewa komai ba ya katse wayar.
Na zurawa wayar ido ina farin ciki.
Zuwa biyar duk aka watse sai su Jamila suka ƙara gyara min ko ina fes ita da Amina na ɗauki kuɗin da abokansa suka bani na ba Jamila nace ta kaiwa Umma duka dubu Ashirin ne. Tace "Ki aje goma a hannun ki a kai mata goma saboda ko za kiyi baƙi zaki iya ba su kuɗin mota." Nace to haka ne. Na basu turare da janbaki daga cikin kayan lefena ita da Amina, su Jafar ma. turare na basu suka min sallama suka tafi.
Na yi wanka nayi sallar magariba na saka wani farin leshi mai ratsin gwal na sha turaruka ina jiran mijina. Sai dai har nayi sallar Isha'i aka kawo min abincin dare amma babu labarin angona na ɗan dai ci farfesun kajin da farar shinkafa kaɗan domin naji yunwa, da rana ban iya cin abinci ba. Na sake gyara fuskata na zuba ɗaurin ɗan kwali na zauna ina kallon TV, na aje turare a gefe na da zummar in ya ƙwanƙwasa ƙofa infeshe jikina da shi kafin in buɗe.
Can cikin bacci naji bugun ƙofa Lokacin ina mafarki ina gida gamu tare da su Umma. Na tashi firgigit ɗankwalina ya faɗi na ganni a ɗaki na naje na buɗe ƙofa shine tsaye ga jakarsa a rataye. Na zuga hamma sannan nace masa sai yanzu ka dawo sannu da zuwa, Na miƙa hannu zan amshi jakar hannunsa Yace a a barta zomuje ɗakina." Nace bari in yi shirin kwanciya. Yace 'a 'a muje haka." Na juya na ɗakko ɗankwalina ya kulle ƙofar da makulli. Da ƙyar na ke tafiya na gaji liƙis saboda aikin da muka sha ɗazu kuma ni ina da wata ɗabi'a in na fara bacci aka tashe ni raina ɓaci ya ke ga ciwon kai. A Ɗakin nashi na kalli agogon bango ɗaya da minti biyu. Na zauna bakin gado ya shiga banɗaki, a zuciya ta nace haka zai ta zama a gurin Hajiya Kullum har irin wannan lokacin? Taɓ da sake na furta a zuciyata. Na kwanta a kan gadon inajin futowarsa ya yi wanka ya gama feshe feshen turaren sa, na yi laf ni a dole bacci ya kwashe ni.Ya zo ya shafa gefen kumatuna ya na faɗin "Baby." Na sake jan bargo . Ya min magana a kunne wai Baby ki tashi ki saka kayan bacci. Sai na yi kamar zan tashi sai in kuma ɓingirewa, ina jin sa yace Baby kinsha gajiyar aiki ne bari dai in haƙura nima yau. Ya jani jikinsa,. hardai , baccin gaske ya ɗauke ni.
Yauma kamar jiya zai tafi masallaci ya tashe ni, haka nan shiru bai shigo ba bisa dukkan alamu yauma sai zai tafi kasuwa, to kenan bani da wani lokaci da zamu zauna da mijina muyi hira wannan babban ƙalubale ne a tare da ni ya zama dole in nemo wa kaina mafita, sannan ya kamata in kula sosai gurin nemo mafita kar in nemo wadda zata fiddani daga gida. Yau ya kamata in fara bugar cikin Juma domin insan ina nasa gaba a gidan.
Na gyara ko ina a sashen sa sannan na dawo na gyara nawa, na karya na yi wanka sannan naje gaida Hajiya. tace "Ya baƙunta?" Nace Hajiya ai na zama 'yar gida. Ta "'A 'a har yanzu ke baƙuwa ce tunda baki gano lokacin da ya kamata ki gaisa da mutanen gida ba sai rana ta hudo ki ke iya fitowa Ina fatan dai ba sai yanzu shima Ubangiji aka gaida shi ba?" Na matsa kusa da ita na sunkuyar da kai ina ɗan murmushi, ba yanzun bane, tunda zai fita ya tashe ni, nan ɗinne dai Allah bai sa na zo akan lokaci ba, ina neman afuwa akan hakan. Ta ɗan taɓa baki tace "Ko kusa ba kiyi laifi ba gidan aurenki ne nan dole ki huta in sautin ki ka zaɓa." Na sunkuyar da kai Nace, akwai abinda za ayi muku ne? Tace a a babu komai,.kije ki sallami mijinki mana." Na sunkuyar da kai ina zaton yana shirya wa ne domin tafiya kasuwa. Tace "In ya gama ai dole zaku yi sallama ko?'" Na miƙe tare da faɗin To Hajiya.
Ina sane na yi musu haka sai da ya shiga na zo gaisheta dole nima in nemi mafita ta akan wannan lamarin, amma ina da buƙatar sanin wasu abubuwa.