Sashe 32
Hamshakiyar Uwa Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Washe gari ya bani zannuwa biyu da dubu goma ya ce inje barka shi baya son zuwa suna É—in nan. Nace to. Na sanar da Hajiya tace to in shirya baya azahar.
Mace mai fara'a maman Haidar wai takwara aka yi wa Shamaki, nace a lallai ki ce ni aka yi wa haihuwar amma bai faɗa min ba. Tace ai bai faɗa masa ba sai ranar zaiji. Nace to ki ce in zuge baki na. Tace gaskiya kam. Da tare zamu zo sai kuma yana da uzri. Tace "Ko kuma Hajiya ta hana ba." Nace Ya zata hana mu fita tare, cikin mamakin yadda aka yi ta san maganar na yi tambayar. Tace "Ba gulma ba amma ko zuwanki na sha mamaki, duk matan Shamaki sai dai su saci hanya su ziyarci mutane, bata son su yi hulɗa da kowa, shiyasa ki ka ga ko gurinki ban zo ba." Na gyara zama domin jin kanun labarai. Nace to ko domin ni ban jima bane shiyasa bata fara min ba? Tace "Ƙila dai ɗan ke yarinya ce ƙarama shiyasa bakya ganewa. Shekara ɗaya na cika ta ke sa shi ya saki mace tace wai bata ci jarabawa ba,ko uban me ta ke jarabtawa oho mata." Nace ce duk bansan wannan ba,ke ya 'aka yi kika sani? Tace "Tsoro na ke kar magana ta fito." Nace sai dai in ke ki ka faɗa amma ni bana haka kamar kin haƙa rami kin saka.
Tace "Ai Kinsan Maman Anisa ƙawata ce munyi makaranta a gurin bikina suka haɗu da Shamaki suka yi aure, kar ki ga irin son da suke yi wa juna amma shekara na cika ta sa ya sake ta. Har yanzu suna son juna kuma tace min kuma zasu iya maida auren su." Gabana ya faɗi amma sai na saki murmushi nace ya faɗa min ai baya ɓoye min komai, ta ce "Haba dai." Nace ƙwarai kuwa. Tace Kenan har irin zaman su da maman Mubina da Meema?" Nace kina shakka ne? Tace "A 'a Naga ita Maman Anisa bai taɓa faɗa mata komai game da su ba." Nace Kinsan so kala kala ne ni komai na shi na sani. Tace ni Uwar gidana sun saba da Maman Meema sun zama ƙawaye tunda matan abokai ne,to ita ke ba uwargidana labarin zaman su shine ta ke bani." Nace dama ku biyu ne? Tace e uwargidana anjima nan zaki ganta tunda muna zama lafiya. " Nace yafi muku sauƙi yaushe zaka tsaya fitina akan namiji? Tace ashe kin gane ga mazan nan namu masu neman matan tsiya kuna nan kuna faɗa wasu na can na faranta musu. Na ce ai kuwa Allah dai ya shirye su. Ta sake kallo na da taji bance komai ba. "Ashe kinsan suna neman mata?" Nayi "yar dariya akwai wani da zaka sheda ne yanzu a maza? Ta taɓa baki tace babu. Amma ya faɗa miki har yanzu suna fita da maman Anisa?" Na yi shiru da alamu matar nan so take ta hasala ni kuma kamar aike. Nace duk na sani, nifa da kika ganni duk wadda ta zubda kanta ta bashi ya bi ya tsallake ruwanta. Ta buɗe baki cikin mamaki, tace "Kin ɗaure mishi gindi kenan? Nace To Maman Haidar ina son mijina ya yi abinda ya ke so. Tace "Yanzu na gane abinda ya sa Hajiya bata nuna muku mugun halinta ba. Ita ke ɗaure mishi gindi yake bin mata." Nace To shi Mijinki wa ya ɗaure mishi nashi gindin? Ta saki dariya gaskiya kullum muna ƙorafi muna masa addu'a. Nace to ya bari? Tace ya dai rage da har a gabanmu yake waya da 'yan matan shi, sai da muka tada balli. Shine yake yi a ɗakin shi .
Sallamar wasu mata muka ji ta amsa ta leƙo sai naji tana faɗin a kamar haɗin baki ga Maman Anisa da Maman Meema. Gabana ya yanke ya yi wata muguwar faɗuwa.
🖊ï¸ðŸ–Šï¸ðŸ–Š
ï¸Na dake domin na gane duk yadda aka yi kiran su ta yi a waya,ko ta tura musu message tun da na lura wayar ta tana hannun ta tunda na zo, amma dai banga ta yi waya ba. Muka bi juna da kallo ni da su, lokacin da suka zauna, na gane Naman Anisa domin suna da kamanni, na kalli. Wadda nake zaton ita ce uwargidan maijego ta ce "Amarsu ce aka zo mana Barka?" Na bi ta da kallo ban amsa ba. Wadda na ke zaton Maman Meema ce tace "Amaryar ma?" Wai a zuwan bata sani ba. Mai jego ta amshe da sauri ta ce "Amaryar Shamaki mana." Maman Anisa ta zaro ido, Tare Da faÉ—in Shamak dai "Dama ke ce Amaryar Allah sarki, har kin bani tausayi ta yatsina baki, gata yarinya wannan tafi sha biyar ma, kai Allah sarki ya zaman É—aki? Har yanzu kwanciya bata gundire ki ba.? Kin lura dai gidan Zeena akwai na'ura ki bi a hankali. Ta ci gaba.
"Yawwa ki lura da su Juma 'yan leƙen asirin Hajiya ne. Kin gane ai?" Murmushi na yi,
Kasu dai kamar wayayyu kuma dai kyawawa ne dan na yarda sun fini a kyau,amma abin takaici babu iji ba iya magana bare tauna kalma.
Na maida kallo na ga Maman Meema wadda take faɗin "Ko bata iya magana ne?" Na yi ɗan murmushi sannan nace ina yininku?" "Ai ashe bamu gaisa ba." Inji Naman Anisa. Sai kuma suka amsa lafiya lau." Maman Anisa sai yatsina take yi tana hare harare ta miƙe tana danna waya,can ta kara a kunne sai tana faɗin Dadyn Anisa wannan karon kuma a haka aka ƙare? Duk mu ukun da ka rabu damu muna da kyau da diri bana kuma muciya da zani aka ɗakko." Mai jego ta tashi da sauri hankaɗa ta ciki tana faɗin shiga kiyi a ciki uwar neman jaraba. Na yi ɗan murmushi, ko kusa ban ji wani haushi ba,domin dai ko ma me zata faɗa yanzu dai ni ke da miji to wane kula su zanyi? Maman Meema tace "Nima dai sai kallon ta nake ina mamaki wai ace kamar Shamaki ya auri wannan yarinyar, koda yake tausayi ma ni take bani wallahi, watan ta nawa yanzu?" Kishiyar maijego tace ƙila zata yi wata biyu ko uku.
Ta kalle ni " Ki fara ƙirga lokacin barinki gidan. Allah ya sa dai kema kina da ciki, duk rintsi randa gado ya taso dole sai kin shigo ciki." Hajiya dai baƙin ciki take yi kar a zauna da ɗanta a samu gado, da ace zai yiwu ta bawa ɗanta abinda matan shi zasu bashi wallahi bazata taɓa barin shi ya yi aure ba.
Na lalle ta nace, da farko banyi niyyar cewa komai ba, domin bani da magana da ku duk kun girme ni, kuma banga laifin ku a cin zarafin da kuka yi min ba, laifi nane da nazo barka har maijego ta kira ku domin ku taru ku ci zarafi na, da sirika ta da kuma mijina.
Na miƙe tsaye na turawa mai jegon ledar gashi nan Allah ya raya. Na ciro waya ta na soma kiran layin Hajiya. Ta ɗaga nace Hajiya barka da yamma tace "Yawwa Rabi'atu." Nace direban ya taho ne? Tace yanzu ya kawo min saƙo da nace ya bari sai ya yi la'asar sai ya zo ya ɗakko ki. " Nace in babu damuwa ya zo kawai yanzu. tace to bari insa a sanar da shi.
Ina kashe wayar mai jego tana riƙe hannu na haba amarya wallahi ban yi dan in wulaƙanta ki ba, kuma ba wadda na kira kawai dai arashi aka samu. Dan Allah ki zauna mana kafin direban ya zo."
Na kwace hannu na nace zan jira shi a waje. Tace "Ki rufa min asiri. Kishiyar ta kuwa sai dariya ta ke yi.
Sai kira ya shigo, na duba naga Shamaki ne a zuciya ta nace sun gama waya da Naman Anisa ta gama ci min zarafi na shine ni kuma zai kira ni me zai faÉ—a min.
Amma sai na ɗaga inji me zai ce,. Sai naji yace "Shugabar ɗalibai kina gidan jegon ko kin koma gida?" Wani lokacin yakan faɗa min haka tun da na sa mishi babban baƙo. Take na gane cewa wayar ƙarya ta yi. Nace babban baƙo gani yanzu zan wuce, danma tsofaffin matanka sun zo ana ta labari. Yace "Su waye suka zo!? Nace kaji ni fa. Cikin shagwaɓa na yi maganar. Sai naji ya kashe wayar. Maman Meema tace "Lallai yarinya mune tsaffin?" Kishiyar maijego tace ita ma kwana nawa ne wai maye ya yi amarya. Maman Anisa ta fito ta na fadin wai me take cewa! Ƙaran wayar maijego ya tsai da ita, mijin maijego ne ya kira ta. Ban san me yake faɗa ba, naji dai tana faɗin nifa ba wanda na kira, to ance maka za 'ayi faɗa ne." Sai ga Shamaki ya sake kirana,"Ina fata dai ba wadda ta zage ki?" Nace , To ko an zage ni babban baƙo ai na kai ne. Zan jira direba a waje ko ka yarda in hau adaidaita sahu? Yace "Na yarda ki ɗauki drop ki bar gidan." Nace yanzu insha Allahu. Ina kashe wayar naga duk suna kallo na. Mama Meema tace Abin tausayi kya gama kicifin ki fice ki bar gidan ba dai Hajiya Zeena da Shamaki ba." Na yi mata kallo sama da ƙasa sannan nace, in banci Jarabawa ba ke nan, kinsan wani abu? Ko a makaranta ban taɓa faɗuwa Jarabawa ba,bare ta gidan Hajiya Zeena mai sauƙi, ku rungumi ƙaddara a kwai zafi ka kasa cin Jarabawa musamman ta shiga ajin gaba.
Na Kalli Maman Anisa nace daƙiƙi shine ya ke maimaita aji, Allah ya sa dai kin fahimta. Na dubi maijego nace Dole Hajiya ta hana zuwa gidan ire Iran naki domin hakan yafi alkhairi. Allah ya raya miki ɗanki. Na rataya jakata na fice, ina ji suna banza a banza kawai.