Sashe 2
Hamshakiyar Uwa Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Na gama tsifar kai na ce Jamila don Allah ki je gidansu Anty mai Saloon ki ce zan zo wankin kai, kuma ina son aja min gashi ance ɗari huɗu ne. Jamila ta kalli Umma ta ce Umma a tambayo? Umma tace dan Allah ku rabu da ni, ki ɗauka a cikin dubu ukunki da saurayin naki ya baki ta walima nace Umma zanyi girki walima da cincin tunda ga lemo. Jamila tace Meat pie ake yi fa ko dounot. Umma tace, duk abinda zata yi ma dai ga su can ta ɗauka, amma ki sani dai baza a yi girki ba, ana ta neman yadda za a yi a samu shi kafar a abinci biki za a haɗa a samu a fita kunya. Ga maganar kayan ɗaki Abbanku ya ƙi sam ya rubure ga maƙota sun saka ido suga nuni kunya a samu na yarda min magana. Nace Umma tunda Abba baya so kawai a haƙura da maganar Neman taimakon nan, tunda ai shi Yayan yace baya
da matsala dan ba a min kayan ɗaki ba. Umma tace, " Aike sam baki da hankali musamman yanzu tunda ki ka samu wannan saurayin tashe rashin kunyar ki ta bayyana damuwar ki a kai ki, za a kai ki ba dai namiji ba. Kuma ki kasa kunne ki jini sosai wannan zaƙuwar da kike nunawa in baƙi suka zo 'yan biki ki ka sake ki ka yimin wannan giggiwar sai na saɓa miki, kayan ɗaki kuma inma ba a yi ba koda naji haushi na banza ke za a yiwa gori. Nace to Umma kiyi haƙuri Allah ya bamu mafita. Jamila ta fita domin ta tambayo min gurin wankin kai. Matar nan daƙyar ta amshi ɗari biyar wai gashina yana da cika da tsawo. Na yi mamakin ganin gashina har gadon baya matar tace wai dan ba mai na sa ba da sai ya fi haka tsawo. Nace zanzo da bikina ta sa min. Naje gidansu Umman Amina ina tambayar inda zan samu wadda ta iya Meat pie. Tace Amina ta rakani gidan wata amarya tana yi. Nan dai mukaje tace saidai taimin kwaɓi inje gidanmu in murza in soya domin mijinta zai dawo yamma ta yi. Na siyo abubuwan da ta faɗa na kwaɓi ta kwaɓamin na ɗauka mukaje Amina da Zuhra da Jamila suka tayani, na kifi ne da kayan miya dan kuɗin bazai kai insai nama ba. Muka soye shi raƙayau wai domin kar ya lalace. Na basu su 'yan tayin aiki sukace ya yi daɗi sannan na kaiwa Umma nace gashi ta ɗiba ita da Abbanmu sai a ƙulla sauran. Tace to shi saurayin naki kin ɗibar masa? Nace anan za a ɗibar masa . Umma tace "To a bari sai da sassafe yanzu dai in je in rufe.
Na yi wanka na shiga ɗaki na kwanta ina ta tunanin banji muryar Mijina ba,kuma har yanzu bai ɗaga kirana ba,duk da ɗazu da safe yamin text ya ce fatan ina lafiya kuma in gaida su Umma. Na ce bari in sake kiranshi ko zai ɗaga. Jamila tace mayya sai ki yi tayi. Nace ai ko tara bata yi ba. Na danna kiran layin gabana yana faɗuwa tsabar son da nake masa ko sunan dana sa mishi a wayar na kalla sai inji tsigar jikina tana tashi. Muryata ta soma rawa lokacin da sautin muryarsa ta doki dodon kunnena. Baby Ya ku ke? Lafiya lau Yaya lafiya baka zo ba,kuma baka min waya ba, na shiga damuwa da banjika ba. Yace ayyuka na Baby suna da dama kiyi haƙuri zan zo ba na faɗa miki ba rannan nace bazan ke samun zuwa akan lokaci ba?" Nace Kasan dai alƙawari kaya ne ko? Yace "E." Na ce to ka san dai ka yi alkawarin zuwa filin saukar karatunmu domin kaga karatuna ko? Yace "Haka ne." Na ce to gobe ne da ƙarfe goma na safe za a fara, dan Allah kazo ka ga karatuna. "Wai dama gobe ne?" Ya tambaya da sauri. Nace e mana. "To kuwa gara da kika tuna min gobe Lahadi insha Allah zan samu in zo. Cikin Farin ciki nace to ka gaida Hajiya da su Anisa,kuma ina gaida su Anty su duka. Yace duk zan faɗa musu. Nace to sai da safe yace to mu kwana lafiya.
Jamila ta lalle ni bayan na gama waya tace wai ke Yaya Baby har wani canza murya ki ke yi ba in zakiyi waya da Ya'yan nan, sanan wannan wayar taki ba a saka mata kati ne? Tunda aka baki ban taɓa jin kice a siyo miki kati ba, kuma rannan har Baabar Kurna ki ka kirawa Umma, sun jima suna magana. Sai lokacin na kula da haka na ce taɓ tun katin da ya kawo a kwalin wayar kuma ai katin ɗari biyar ne. Jamila tace duba Balance ɗinki mu gani, na tsurawa lambobin ido baya na danna bangane adadin kuɗin ba. Na furta ina kallon Jamila. Tace, mu gani tace kamar ɗari takwas ko dubu takwas. Nace ko dai naira takwas ba. Muka sa dariya. Nace duk tsiyarsu ko nawa ne dai sai sun ƙare domin kirana zantayi ƙila kuma ina cikin wani tsari ne wanda suke bada bananza. Jamila Tace 'hakane ma. Na sauke ajiyar zuciya na ce Allah na gode maka Ubangiji kamin komai.
Jamila tace Yaya Baby kina bani mamaki har cikin dare ina jinki kina yiwa Allah irin wannan godiyar, wallahi ba su Umma ba ko ni ina jin haushin yadda kika koma mara kunya lokaci guda. Na tausasa Murya yanzu wannan rashin kunya ce Jamila yi wa Allah godiya? Tace "Ai ba iyaka godiyar zaki tsaya ba, da banyi magana ba cewa zakiyi da ya baƙi miji kamar Yaya Aliyu a dai-dai wannan lokacin." Nace to Jamila meye laifin hakan kar ki manta a da fa ko kare bai ce yana sona ba har tsegumina ake a layi yanzu kuwa an dawo masu zaginma sai shige min suke yi. Jamila tace to ai shigewar ta munafirci ce, in kin yarda, ɗazu da Umma tace in amshi rariyar da Umman su Nabila suka ara a gidan na samu Umman su Fati mai awwara,tun daga soro naji suna cewa wai ba'a san asalin Yaya Aliyu ba,babu bincike daga zuwa an ɗau yarinya za a bashi. Wai ƙilama ba ɗan ƙasa bane ƙarshe sai kin tara 'ya'ya ya gudu ya barki. Umman Fati ce da wannan dogon jawabin. Umman Nabila kuwa tace su suka sani dubi uban kayan lefe gashi sun saka aure da gaggawa kamar suna da wata tsiya ma ji ma gani dai mu 'yan rakiya ne har gidan ango muga abinda zasu kai mata." Nace Muna fukai ina son mijina haka, ko daga sama ya faɗo, kinsa Allah da nice naje sai na zage su, nifa Jamila akan Aliyu iyayena ne kawai suka fimin shi sai ku ƙanne na. Jamila tace shiga nayi da sallama sai suka hau borin kunya na amso na dawo ko Umma ban faɗa mata ba. Nace Yawwa gara kar ki faɗa mata dama, cikin damuwa take. Ai basu kaɗaiba ko gidansu Zuhra da suke 'yan uwanmu ai suna nuna baƙin cikin su. Kuma suma suna munafircin Yaya Aliyu na maganar bincike shiyasa ban so aka ƙara sati ɗayan nan ba wallahi. Domin gani nake wani zai iya zuga su Umma su ce sun fasa bashi ni. Jamila ta ja tsaki ta kwanta tare da faɗin ni fatana Allah ya sa yana miki irin son da ki ke masa." Nace yanzu har Kinji haushi kenan? Ta ce "Zakewar taki ce tana yawa, kuma kisan Allah Umma da Abba abin yana basu takaici kyazo kija wa kanki suce sun fasa mugani ko zaki bishi ba aure. Na ɗora kaina a gadon bayanta ina faɗin bazan bishi ba Jamila, amma na tabbatar zan mutu. Dakin yayi tsit Jamila haushi ya hana ta bani amsa. Ni kuma na faɗa tunani wai ace an fasa. Da sauri naga Jamila ta tashi zaune tasa hannu biyu ta tallafi fuskata wai ashe hawayena ne suke sauka a gefen cikinta. Tace Kuka ki ke Yaya Baby, me akayi na kuka?" Na sauke ajiyar zuciya cikin rawar murya nace wallahi ban sani ba Jamila, amma na samu kaina a matsananci son Yaya Aliyu iya tunanin sa in na zurfafa sai na yi wannan kukan. Kuma na kasa gane dalili. Kimin fatan Allah ya sa shima yana sona. Jamila ta shiga lallashina tana share min hawaye tana faɗa min cewa tabbas ya na sona, kuma aure babu fashi kuma za a yi komai cikin rufin asiri. Muka kwanta cikin saƙe saƙen zukata. Sai Muryar Abba muka ji yace "Ke Baby zo nan.'.. Muka tashi da sauri zaune nace Jamila me yafaru? Ta yarfa hannuwa alamun bata sani ba. Jikina ya soma ɓari, na ce kodai ya ji zantukamu ko kuma wasu sun shigo shi akan maganar binciken Aliyu ya fasa aura min shi. "Ina ki ke?" Muryar shi ta ƙara ratsowa. Jamila cikin sauri tace kije mana amma komai zai ce ki yi shiru. Na miƙe na fita yana zaune kan tabarma inda sukan zauna da Umma.