← Book details Hamshakiyar Uwa Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 34

Sashe 4

Hamshakiyar Uwa Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

A dai dai wannan lokacin Hajiya ta kalli Shamaki sosai zarginta game da takardar ya bayyana kuma in har haka ne yarinyar sun zo, neman taimako ne haƙiƙa sun fadi babbar jarabawar ta. Wanda hakan zai sa ko da an yi wannan auren to sun zaɓtarewa yar su wani babban maki. "Ka bani in duba" ta furta cikin isa irin yadda take yi in ƙasaitarta ta motsa. Bashi da wani zaɓin da ya wuce ya bata waɗannan takardun na gaskiya ya saurari Allah wanda yake ta kira sunayen shi ɗari ba ɗaya a ƙasan zuciyarsa. Sanin kanshi ne in ya bata waɗanda ba su bane zata gano na gaskiya ta hanyar yin magana da Maman Afra. Wanda hakan zai iya haifar da ƙatuwar matsalar da zata iya soke auren Baby wanda yake ayyana hakan da mutuwar tsaye a wurinsa. "In har ka bari na tafi daga falon nan karka sake ka tambayi dalilin da ya sa na janye batun auren ka."
Kalaman Hajiya suka ratsa kunnuwansa. Cikin sauri ya miƙa mata tare da faɗin afwan afwan ina duba shi ne. Ta amsa tare da faɗin "Ai guda ɗari ne a gurin dole ka kasa tantancewa. Ta ɗauki gilashinta ta saka ta soma bin shafi shafi tana dubawa, bata ga wani abu da zai sashi yin irin wannan rashin natsuwar da har ta jefa shi a zarginta ba, amma dai ta yi imani dole akwai wani abu. Don haka ta maida hankali ga Number daya ɗauka, yana kallon ta har ya soma murna, sai kuma ya zaro idanu ganin tana ɗaukar lamba. Ta danna kira ya tafi, har ya katse ba a ɗaga ba.Ya haɗiye yawun bakin sa da ya ɗauke, sai kuma ya ga ta ƙara dannawa. Sai aka ɗauka, ta danna handsfree ta yi sallama, cikin yanayin damuwa aka amsa. Tace "Daga Zeena Foundation ne inda kuka zo neman taimako, ance ku kawo mahaifin yarinyar amma ba ku zo ba?" Cikin girmamawa aka bata amsa, "Kiyi Haƙuri Hajiya Mahaifinta ya ce shi ba zai zo ba." Kafin ta ƙara magana sai taji muryar namiji ya amshi wayar. yana magana cikin fushi, Hajiya yarinyar nan tawa ce dan ina talaka bani da rashin godiyar Allahn da har sai naje maular kayan ɗaki. Batare da izinina taje ba. Kuma ban aike ta ba, bana buƙata kiyi haƙuri. Hajiya zan mata iya yi na, ku ba waɗanda suka fini buƙata." Ya kashe wayar ba tare da jiran amsar ta ba. Falon ya yi tsit in bada ƙaran AC da kuma TV da ke yi can ƙasa. Kusan daƙuƙa tamanin, sannan Hajiya numfasa ta ce, "To kaji sirikin ka irin amsar da ya bayar." Shamaki yace Sirikina kuma Hajiya? Tace "Ka dai na yi kamar wani baka gane komai ba, tun daga sunan yarinyar na fuskanci surukan ka ne, kana son ka ɓoye min domin kar in gani, dama baka ɓoye kana nuna rashin nutsuwa ba, babu lallai in gane abinda ka ke ciki. Ta gyara zama ta ɗanyi ƙasa da murya, tace, In tambaye ka mana Shamaki." Ya sunkuyar da kai tare da faɗin ina jinku Hajiya. Tace "Wai inada wani mugun hali ne? Da sauri yace Subhanallah! Mai ya kawo wannan furucin! Baki da mugun hali Hajiya, baki kusanci, mugunta ba. Tace "To me yasa ka ɓoye min cewa surukan ka sun zo neman taimako?" Ya numfasa Wallahi Hajiya zaman da nayi a nan gurin shine ya kawo har na na kula. Sannan na ɗauki lambar ne na bincika na gano. "To daka gano da wane irin hukunci zaka ɗauka?" Dama dai zan maida ne su bi ƙa'ida da ake bi, domin abu bai min daɗi ba, yadda nasan mahaifin yarinyar nan da haƙuri wadatar zuci da ƙoƙarin nema kuma ace sun zo neman taimako. Wallahi da kika kira shi naji daɗi sosai da naji cewa babu sa hannunsa, ita ma Umman ta su ƙila wasu ne suka zugata. Hajiya ta sauke ajiya zuciya tace "Ni kaina da ace Uban ya zo haƙiƙa sun kayar da 'yar su babbar jarabawa. Amma me zaka ce game da ita uwar da take aikata abu ba tare da sanin mijinta ba, wane tunani zaka yi game da 'yarta mai kwaikwayo daga gareta? Kasan dai uwa ce makarantar farko a gurin kowane yaro." A ƙasan zuciyarsa yace ta ƙirƙiro wata damuwar Allah ka fidda ni. Ya ɗanyi gyaran murya yace Hajiya ba wannan ne abin dubawa ba, abin dubawa shine, da Abba ya ji abinda Umma ta yi kuma ya daka tsawa, ya hana kuma akaji ba a bijire ba. Shine abinda za ku duba Hajiya saboda wancan kuskuren ne da kowa zai iya aikatawa. Ko Allah da ya halicce mu muna yi masa kuskure amma da mun amshi kuskurenmu mun tuba shike nan. Hajiya ta saki maganar da faɗin "To ko ba komai sai ka godewa sirikin ka domin yadda ya yi jarumtar ƙin amsar kayan nan, ya kwace ka daga ƙaryar da kamin ta farko, sai dai kuma bayan tiya akwai wata caca." Shamaki ya zaro ido. Wacce fa? Hajiya tace "Wannan zan jira sai lokacin da ka ke jin cewa ni mahaifiyar ka ce, kuma wadda ta ke yi maka so da ƙauna zalla babu sirki, wadda ko mutum ka kashe zata iya rufa maka asirin da har duniya ta tashi ba wanda zai ji. Kai wadda zata iya bada ranta domin fansar naka. Lokacin da duk ka fahimci hakan sai mu yi ɗaya magana."

🖊️🖊️🖊️
*HAMSHAƘIYAR UWA🧕🏻*

*NA*

*HALIMA ABDULLAHI K/ MASHI*

_PAID BOOK_
_Kuɗin karatu ₦600_
_Account number 0700549935 Halima Abdullahi Access Bank a turo shaidar biya ta wannan number 08140004302 ko katin Mtn_
_Phone 08140004302_

*DOKA*
_Ban amince wani ya É—ora littafin nan a wani Social media ba,ko a maida mini shi Audio ba tare da iznina ba yin haka daidai yake da fuskantar fushin hukuma. A kiyaye_

*Masu son a Tallata masu hajarsu suyi magana ta wannan number 09068032427*

*Page 13*

Cikin sanyin jiki Shamaki ya sunkuyar da kai, tabbas ya sani Hajiya tana yi masa so tsantsan na tsakanin É—a da mahaifiya. Kuma tabbas 'yan uwansa suna son sa sai dai fa ba kamar Hajiya ba.
Kuma su suna iya tattauna damuwar shi da mazajensu saboda so da kuma yarda da juna. Amma Hajiya bazata iya tauna kowace matsala tasa ko ƙarama ko babba da su 'yan uwansa ba. Hajiya ce keda maganin damuwar sa kuma ita yafi dacewa ya kai ma wa kuka, kamar haka ta ke nufi.
Ya ɗago ya kalleta ta zubawa TV ido, kamar tana kallo, amma ko shi ya san tunani kawai take yi. Ya ɗan ƙara matsawa kusa. A hankali ya furta "Hajiya" ta yi kamar bata ji ba. Ya sake matsawa kusa da ƙafarta, yace Hajiya. "Faɗi ina ji." Ta furta ba tare da ta waiwayo ba. Yace tun tuni nasan kina min so fiye da irin wanda ki ka furta. Ba zan iya kawo bayanin irin soyayyar da kike min ba, ni da 'yan uwana. Haƙiƙa na samu 'yan uwana mu yi magana, amma ba kamar yadda ku ke zato bane Hajiya. Nauyi nike ji in sameki da irin wannan zancan. Hajiya ta maido kallon ta gare shi, ta soma faɗin "Ni fa na ɗauki cikin ka, na haifeka, na shayar da kai da wannan maman nawa, ni ce wadda na riƙe ka aka yi maka kaciya. Aliyu ka tuna ban daina yi maka wanka ba sai da na ga alamun balaga sun fara bayyana atare da kai. Lokacin ka shiga ajin farko na ƙaramar Sakandire. Anyi haka? Shamaki ya kaɗa kai alamun ya tuna. Tace "To a kanme har zaka ce kana jin nauyi na?" Shamaki cikin tsananin kaunar mahaifiyar sa ya ce, Hajiya na yi kuskure mai girma, kece ya kamata in tunkara amma ki yafe min tare da sauran 'yan uwana a ƙoƙarin su na nuna ƙaunarsu a gare ni, amma ko da na faɗa musu duk sunce gurinki za a dawo sai dai su za su zo a madadi na. Hajiya tace a a bana bukatar su a gidana game da wata matsala taka. Ni da kai muna kwana a gida daya su da ke kwana a gidan mazajen su shine har sai sun wanko ƙafa domin yin gyara a matsalar gidana?" Ayi mana afwa Hajiya, zan sanar da su ba sai sun zo ba. Kuma insha Allahu zan sanar da ku damuwar a yanzun nan in har kun yi min izni.
Chapter 4 · 0% Book details