Sashe 25
Hamshakiyar Uwa Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Tace "To tunda kinƙi tambayar shi ni ga tawa gudummawar nan ki bata Allah bata lafiya. Na faɗa miki tun daga ƙarfe biyu sai ki shirya ki jira zuwan direba kar yazo a barshi yana ta jira." Nace sanyi duk yadda ki ka ce Allah ya saka da alkhari.
Na fito tasa Juma ta É—auki ledar ta kai mota sannan na fita,sai da na tabbatar gani zaune a mota sannan na kira Jamila ta wayar Umma nace gani a hanya. Sai naji ta kwashi ihu da murna na kashe wayar na jefa a jaka,,sannan na buÉ—e ledar inga abinda ke ciki. Turmin atamfa guda biyu, sai wata farar Envelope na buÉ—e kuÉ—i ne 'yan É—ari biyu rafa É—aya. Tabbas zargina ya tabbata Hajiya latsa ni ta yi .
Tabbas sai na zama mai kula domin na fuskanci Hajiya ta iya latsin basira.
A bakin lungun gidanmu ya tsaya, ya fito ya bude min ƙofa, sannan na fito ya amshi ledar ya biyo ni.
Kamar na taka da gudu in isa gida haka babu,amma sai na tafi sannu saboda direba da ke biye da ni cikin girmamawa.
Na amshi ledar na yi masa godiya sannan na shiga da sallama, kamar taron suna gida ya cika, ban ko tsaya amsa gaishe gaishe ba na nufi É—akin Umma da gudu tana zaune a kan gado sanye da atamfar ankon bikina. Na zauna bakin gado na kama hannun ta ina sannu Umma. Sai fara'a ta ke yi tana kallo na. Na gaishe ta na tambayi jiki sannan na gaida sauran mutane. Sai faÉ—i ake yi amarya tubarkaalla. Umman Amina tace ya surukar ki kuwa? Ai mun taho muna hirar ta wannan mata tana da kirki kuwa? Na yi murmushi nace tana da kirki sosai kuwa. Na É—akko laidar nace gashi ma tace a kawo wa Umma. Nanfa kuma aka shiga yaba mata.
Jamila ta kama hannu na muka shiga ɗakinmu na da muka zauna,tace "Yaya Baby wai don Allah kina da ciki ne?" Nace ke Jamila yaushe ki ka zama haka? Tace "Ba wai yaushe na zama haka bane, kinsan dai nice abokiyar shawara,nace bani da komai me ki ka gani? Tace "Kinyi kyau." Nace danma baya samun zama Jamila kinsan ko hira bamu taɓa yi ba,amma karki faɗawa Umma. Tace "Kamar yaya ko hira ba ya kwana a gidan kenan?" Na bata labari dai dai da fahimtar ta. Tace "To kinsan me za kiyi?" Nace 'a'a tace da rana kisha bacci da dare ki tashi ki dire ki ce bakya jin bacci shima ki tsare shi da hira."
Nace Gaskiya Jamila kina da kwanya, amma kuma zan tausaya mishi ai in har zaije da rana ya sha wahalar kasuwa dare kuma in hana shi ya huta. Tace Hajiyar ta rage mishi lokacin lissafin da ranar ko da daren mana.
.....
Nace Jamila kenan, zan gwada Allah ya sa dai kada hakan ya zama wata matsalar a gidan kinsan komai a gidan ɗan ƙa'ida ne.
Jamila tace "Ameen insha Allahu ba wata matsala, yanzu dai nasan za'a canza miki waya, ina riƙon taki, ko kiba ni 'yar dubu biyar in sai mai botura." Nace ina naga kuɗin da zan baki, kinsan Allah banda kuɗin nan da Baba ya aiko ki kika ki ka karɓa da sai in ce miki ni ban taɓa ganin takardar kuɗi a gidan nan ba. Shi kanshi ban taɓa ganin kuɗi wai yau gashi a hannun shi ba.
Jamila ta saki baki tana kallo na. "Dama duk kirarin kuɗin basu a zahiri kenan suna ɓoye a banki?" Nace to ƙila hakanne. Tace "Rannan wata 'yar Ajinmu tana labarin Gidan Hajiya Zeena da irin dukiyar da ke danƙare a gidan wai 'yan uwansu ne. Na ce mata ni yayata a gidan ta ke aure. Da farko ta ƙaryata wai Ɗan Alhaji Baita ba zai auri 'yar gidan mu ba. Shiru na yi mata sai da wasu 'yan ajinmu suka tabbatar mata shine ta yarda,tace gaskiya ta dangwalo, ance gidan suna da ɗakin kuɗi ko ƙananan yaran gidan sai dai su shiga su ɗiba, sannan Makka duk wata." Na kwashe da dariya nace kai mutane Allah ya kyauta. Jamila ta ce "Dama ni na musa wannan labarin amma ina kokwanto nace bari dai zan tambaye ki inji tunda na san dai ke yanzu kinsan komai." Na kauda zancan da faɗin, tashi ki rakani gidan su Zuhra mu gaisa da su.
Umman su Zuhra tace "A 'a ,ga fa amare muka gaisa ta tambayi Hajiya nace tana lafiya duk tace a gaida ku. Tace ai wannan mata daga gani zaki sha ɗani a gurin ta, sam mace ba rahma magana ma da kyar a ke yinta ita dole ga mai kuɗi." Nace la kuma Umma sauƙin kai ne da ita dan baki zauna da ita bane. Hajiya ba ruwanta wallahi. Ta taɓa baki, "To kenan mu ta wulaƙanta? Nace ta yi muku wani abu ba daidai ba ne? Tace "Koda yake ke kina rufe radda muka kai ki. Kallo ma bamu ishe ta ba, bare washe gari da muka koma." Nace ikon Allah ƙila dai ko mutane ne suka mata yawa kin san shi'anin taro. Haka dai na yi ta kare Hajiya domin ko iyayena bazan bari su ji sirrin zama na da Hajiya ba, kar in ɗaga musu hankali,ko kuma su zo suna jin haushin ta. Jamila ma sai da nayi mata kashedi domin kar ta faɗa.Na san kuma bazata faɗa ba.
Muka dawo ana ta raha duk wata budurwa ta lungun mu da taji labarin na zo sai ki ganta wai tazo mu gaisa. Kamar yadda Hajiya tace daga ƙarfe biyu in shirya haka na yi, ina yin azahar na shirya ina jira direba. Jamila tana ta mita wai maimakon in kai dare. Nace ana wanke tukunya dan tuwon gobe ne, bazai yiwu in wuce lokacin da aka bani ba. Da naga uku ta kusa na kira Hajiya na gaisheta cikin girmamawa na haɗa ta da Umma ta yi godiyar saƙo, sannan na tambaya ko direban ya iso. Tace "Aka ta aike shi ne in ya dawo zai zo.
Sai biyar da wani abu ya iso,muka kama hanya zuwa gida.
Umma dai citta da daddawa ta bani wai in kaiwa Hajiya. Na kai mata nace inji Ummanmu tace "To an gode jeki kaiwa Juma.
Na kai mata kicin ta ce amarsu ansha gida kin dawo da wuri ko Hajiyarmu ce ta baki lokaci? Na yi ɗan murmushi nace sai anjima. Tace kinga a nan babu wannan na'urar hakan yana ɗaya daga cikin abinda zai sa Hajiya ƙi ta barki ki zo nan ɗin. Nace kalle ta ban yi magana ba. Taci gaba da faɗin "Ko da yake jimawarki a nan shima abin tuhuma ne a gurin Hajiya. Na yi 'yar dariya nace Baba Juma kina da abin dariya wallahi. Tace 'yar nan da baƙin wayo ki ke, kin ƙi ki ɓara dan kar ince kin yi munafircin Hajiya ko? To sha mutumin ki, Hajiya bata amsar magana sai da hujja ba bugar cikin ki zanyi ba. Nace ni Bab Juma bana gane irin waɗannan zantukan. Tace "Ba wani bakya gane wa, daga ganin waɗannan wayayun idanuwan naki kar ki ke kallon kowa.
Ni dai na fice, zan nufi gefena. Hajiya tace "Basa cikine naga kin jima? Nace suna ciki munyi magana ne. Tace to madallah.
Ƙarfe sha biyun dare ina kwance a tafkeken gadon Shamaki ina ta ninƙaya, ina son in gwada hikimar Jamila ne in tsare shi da hira. Na ɗauki wayata ina shirin tura masa saƙo cewa yau dai ina jiransa hira na ke son mu yi.Sai kawai naga saƙonsa kamar haka.
"Baby ban samu dawowa ba ƙila ma ba gobe ba, amma zan sanar da ke in zan dawo. In kin kira ni baza ki same ni ba,amma ni zan kira ki a duk lokacin da na samu dama."
Na karanta na sake karantawa. A fili nace tofa! Ni wai dama wannan ne auren da mata ke cewa Allah ya kai su gidan hutu su yi aure su huta? Hummm gaskiya kam ina hutawa in dai bacci da cin abinci da nama shine hutu.
Na sauka a gadon na nufi É—aki na na kwanta.
Ban sake ji daga mijina ba sai bayan kwana biyu ina zaune shiru zama ya ishe ni, na tashi na nufi sasan su Mubina, sai ina jiyo hayaniyar su a wani guri. Nabi hanyar sai na riski wani É—an gurin shan iska da 'yar rumfar gargajiya, ga lilon yara sannan gurin akwai ni'imar bishiyu. Suna ta wasa can kan wata kujera Azima ce tana karanta wani littafi na Hausa. Nace Azima kuna nan kuna shan iska kenan? Ta É—ago ta lalle ni haka sama-sama tace "Umm." Ta maida kanta ga karatun. Na isa gurin su Meema nace ku daina wasa kuzo in koya muku karatu kuna s? Duk duka ce e, suka biyo ni nace muje É—akin karatun ku inda Antynku ta lesson ta ke koya muku, ni na islamiyya zan muku.