Sashe 7
Hamshakiyar Uwa Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Na tashi da zazzaɓi amma haka na ci gaba da aikin gida domin nasan ciwon na rashi ji daga masoyina ne. Dayake anyl hutun boko hakan islamiyya an bada hutu tunda aka yi saukarmu, dan haka Jamila ma suna gida. Ta same ni kwance ga dumamen tuwao na da kunu na kari a gabana. Tace "Wai don Allah ke haka kike son a kai ki gidan mijin?" Nace Jamila ina ganin Yaya ba wani sona da yake yi, hawaye suka soma zubo min. Ki duba fa Jamila ba zuwa ba kira ko saƙo na kira ya ƙi ɗagawa. Jamila cikin sanyin jiki tace "Nima dai inata yin waswasi amma kawo wayar ki mu gwada wata dabara." Umma ta leƙo tace wai jikin ne kin kuwa sha maganin? Nace Nasha tace harda gajiya ,bari inje gurin Umman Amina inji batun zannuwan gado da labulaye da muka yi magana. Muka ce to. Jamila ta rubuta saƙo kamar haka.. Yaya Aliyu barka da War haka, nice Jamila ƙanwar Baby, bada sanin ta na ɗauki wayar ,na turo saƙon nan ba. Baby bata da lafiya tun cikin dare, ta suma ta farfaɗo amma jikin da sauƙi yanzu, nace ta sanar da kà i tace abarka ka faɗa mata. Kana cikin uzrori, amma ta bar saƙon cewa in ajalinta ne ya zo dan Allah ka jagoranci gawarta zuwa kabarinta ,kuma ka yi mata addu'a. Na saki baki lokacin da Jamila ta ke karanta saƙon. Nace ke ina kika samo wannan iya tsara zancen? Tace "Haba Yaya Baby kina mace baki san yadda za ki dagula lissafin namiji ba, in ya dagula miki naki,? Ni nan da kike gani na in har na fara soyayya za a sha fama." Nace duk yadda kike kallon abin ba haka bane. Amma mu jira lokacin sai mugani yanzu dai tura masa wannan saƙon muga ya abin zai zama. Minti kamar biyu da tura saƙo har na soma fargabar ko ya gani ya share, sai ga kira, zan ɗaga Jamila ta amshe wayar tare da faɗin dakata tukunna handsfree. Ta yi sallama,, yace "Baby" Tace Jamila ce Yaya Baby ta samu bacci. Yace "wai me ya faru ne Jamila?" Tace To ni dai tun juya bangane mata ba, ta damu wai baka zo gurin sauka ba, kuma baka ɗaga mata waya, wannan dai shine mafarin ciwo har tana suma, mukam har mun sare amma yanzu da sauƙi, sai dai fa ba cin abinci ga dumamen safe ya nan har kokon bata ci ba. "Innalillahi wa'inna ilaihira'un! To an kaita Asibiti ne?" 'A 'a ko magani taƙi sha sai wasiyya take bari. Yace ina zuwa ya kashe. Muka sa dariya, Jamila ta ce "Yanzu zai zo. Nace in su Umma sukaji fa? Ta ce ke zaki aɗa musu? Barshi ya zo." Umma tana ɗaki ta kwanta. Muka ci gaba da tattaunawa kamar minti ashirin da gama yawa sai ga kira ya kuma shigowa. "Waye? Na tambayi Jamila da sauri ta nuni min fukar wayar kafin ta ɗaga. Tace Yaya. Yace "Kizo gani a waje tace to. Ta kashe wayar. Na miƙe zaraf tace ina zakije? Kwanta kawai ki jira ni. Ta fita wai sai naji kishi Jamila zata gurin masoyina, amma nasani ba wani abu bane. Sai dai duk da haka na ji tsoro na laɓe ina jiyo muryata tana maimaita masa. Yace ya zo ne muje asibiti, tace ai da sauƙi kuma Umma na bacci Abba baya nan kaga ai badama aje amma ka shigo kaga jikin nata. Da gudu na juya na kwanta kan 'yar tsummar katifar mu na rufa.
Yau ne karo na farko da Yaya ya shigo cikin gidanmu, duk da gidan talakawa ne ko ina siminti ya ɓurje amma fes a share ko tsinke ba zaka gani ba. Ta je ɗakin Umma ta ɗakko sallaya tazo ta shinfiɗa masa a gefen katifar inda muke salla. Ƙamshin turare sa ya cika ɗakin kamar na tashi zaune, amma ba dama dole umarnin Jamila zan jira a wannan lokacin. Ya ce haka jikin ya yi shine bata sanar da ni ba. Jamila ta ce Wallahi ta hana, yanzu dai bari in tashe ta. Yace "A'a barta kawai Jamila ta taɓa ƙafa ta tare da faɗin Yaya Baby! Na yi miƙa kaɗan dama fuskata na kallon bango na juyo a hankali, sai na sauke idanuna kan angona, na tashi zaune da sauri na zuba mishi ido. Jamila ta sulale ta fita ƙofar ɗaki. Yace Baby ya jiki? Nace na samu sauƙi ya akayi ka sani? "Jamila ta sanar da ni, ki daina damuwa saura kwana nawa mu zama a tare na har abada Baby, kwana biyar kacal." Na lumshe ido na ware su a kan fuskarsa, me yasa baka zo min sauka ba? "Nazo Baby, kun yi karatu ku duka, kin yi ke ɗaya kina kuka suratul Muhammad wanda nima sai da na zubda hawaye, ashema kece shugabar ɗaliba, kin amshi kyautuka harda na ladabi babban baƙon ku wani Basarake ya baƙi kyautar kayan ɗaki yadda ya yi ta jawabi akan ki shine duk kishi ya kama ni, na tafi domin sai naga kamar yana sonki gashi mai hali kar ki juya min baya." Na sauke ajiyar zuciya tare da haɗiye wani ƙududu da ya tokare a zuciya ta. Nace Alhamdulillah ashe ka zo, Yayana warke ciwon da ke damuna a zuciya na matsin na ƙara yin ƙasa da murya, nifa. lokacin bana cikin hayyacina ni dai kunnena ya ji lokacin da yake sanarwar zai min kayan ɗaki, kuma in zaka harbe ni bazan iya faɗa maka kayan da ke jikinsa ba, na san dai akwai baƙin glashi a idonsa. Kuma ko shine ƙaruna a kuɗi ya yi kaɗan bai isa ya raba zuciya ta da sonka ba. Shine ka ƙi ɗaga kirana tun kafin ranar sauka, shin ko me na yi maka? Yace "Abubuwa ne Baby baza ki gane ba, amma ba da wannan wayar na fita ba ranar sai da na dawo na ga kiran amma kiyi haƙuri. Ya kalli robar gefe na, ki tashi ki karya. Ban musa ba na matsa kusa da robar na buɗe, nace Jamila bani cokali. Ya kalli tuwon shinkafa da miyar kuɓewa ɗanya. Ta miƙo ya amsa, nace to kaima kac,i ko baka cin tuwo? Yace "Ni na karya, ke dai ki ci." Na ci kaɗan nace nasan baza ka iya cin abincin gidanmu bane. "Saboda me?" Ya jeho min tambaya. Nace to ka ci, in gani. Ya amshi cokalin sannan yace waya girka?" Nace ni mana. Ya sa cokali ya ci dan ƙarami sannan ya ƙara. Naji daɗi ya ce me kike son cin in aiko maki anjima? Nace babu, yace to zan miki aike zan koma tunda kin samu sauƙi. Ya kira Jamila ya bata dubu ɗaya yace ta siyo min Maltina. Na rakoshi har soro yace in koma kar in fito zai zo ya kawo min kuɗin Party. Jamila ta dawo siyan Maltina tace ƙwaya biyu na siyo kisha ɗaya ni kuma in iragewa su Jafar canjin a baiwa Umma inta tashi. Nace zan rage mata itama ta ɗansha saboda Ummar. Jamila tace ba gashi ya zo ba, amma ke kuka da ƙunci kawai ki ka iya sai kiransa ya na ja miki aji. Nace Jamila ai na daina raina wayonki wannan shiri haka, kinga yadda jikinsa ke rawa har tuwon nan ya ci. To haka dai muka ci gaba da tattaunawa har Umma ta farka. Saura kwana biyar biki mutane sai tsegumi ake yi ba aga ina yin wani gyaran jiki ba. Harda muka yi maganar da Jamila tace ko mu yi wa Umma magana. Nace a a mu barta. Umman Amina dai ta kawomin wasu jiƙe jiƙe ina sha,da wani tsimi. Sai kuma wata kaza nan mara daɗi akace in cinye. Saura kwana huɗu biki kuwa aka kira Abba daga Gandu wai yaje zai ɗauki kayan da akayi masa alƙawari. Da ya kawo kayan sai maƙocin mu aka roƙa gidansa ya tashi ya yi sabo zai gyara ya zuba haya, aka zuba. Banje kallo ba, amma an ce harda dinning table kaya irin na masu kuɗi abin ba a magana. Ranar ya aiko min ta katin ɗaurin aure dana Dinner. Muna ta juya katin Dinner wai a ZEENA Event gurin da gwamnoni da manyan masu kuɗin Kano suke shagali. Jamila tace "Ni fa na soma zargin Yaya nan kamar yana basaja." Nace ke ba wani basaja kinsan yana musu yaron shago, kuma suna mutunci tsaf zasu iya bashi. Jamila ta ce haka ne kuma. Muka samu Zuhra da Amina muka soma rabon kati. Labari ya zaga lungu da saƙo za a fita perty a bikin Baby kuma ZEENA Event center. Nan fa sai surutun wasu suce ɗan karya ne, wasu suce ƙila gadin gurin ya ke har gida waɗanda ba su samu kati ba suke zuwa wai a basu saboda son ƙwaƙƙwafi. Ango bai zo ba sai ranar Alhamis. Ya zo bayan magariba wai yana sauri, yace gobe Juma'a in shirya ni da Jamila Yayarshi zata zo ta kai ni gurin wadda take musu lalle. Yace itace zata miki duk wani gyara, kuma sune suka shirya Party. Nace to yace in faɗi me nake buƙata, nace ba komai dama ai kuɗin perty ɗin zai bada. Ya fito dubu goma yace duk da haka ga wannan kiyi haƙuri ni baza mu haɗu ba sai a gurin Dinner ranar asabar. Nace to za a zo a ɗauke mu ne? Yace e za a kawo motoci ya yi wa abokansa magana insha Allahu. Na ce to na gode. Yace in shiga gida. Na shiga soro na tsaya ya wuce, na dawo na leƙashi ya tafi da sauri, farin ciki ya mamaye zuciya ta. Sai naga su maman Fati suna leƙensa suma dama Fatin ta wuce muna tsaye. Nace kai mutane akwai su da son saka kai cikin damuwar wani.