← Book details Hamshakiyar Uwa Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 33 OF 34

Sashe 33

Hamshakiyar Uwa Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ina fita direba yana isowa na shiga muka wuce.
Hajiya ta tambayi maijego da jariri na ce duk suna lafiya. Tace "Amma lafiya lokacin da kika kira É—azu nake jin 'yan surutai?" Nace hira ce 'yan barka ke yi ni surutun nema ya ishe ni shiyasa nace zan tafi. Ta yi murmushi "Mata ai in sun taru basu da labari sai gulma ko hirar mazajen su, mai tunani kuwa bata da wannan lokacin."
Nace Allah ya kyauta na shige É—akina.

Da dare Shamaki suna cin abinci, ina dama masa wata fura da ya zo da ita, yace "Wai kuwa Hajiya yarinyar nan ta faɗa miki matan nan sunje gidan Shamsu?" Tace waɗanne matan ne? Yace "Su Naman Anisa da Maman Meema ne nasan tabbas su ne domin Maman Mubina na san bata ƙasar nan, ko tana nan ma bazata zo ba."
Hajiya ta Kalle ni, haka ne? Nace e sune, suma sunzo barka ne. Tace sunzo gulma dai,Allah ya sa dai ba su yi miki wata maganar banzar ba." Nace 'a'a hirar su suke yi. Yace "Ba wata hirar su, yarinyar nan bazata faÉ—a bane Allah ka É—ai ya san abinda su ka yi mata." Na kalli Hajiya wadda ta zuba min ido. Nace To yanzu kam koma menene ai ya wuce, ni nayi musu uzri domin babu daÉ—i kana son abu ka rasa shi, sannan ka ganshi a hannu wani kuma wanda ka ke ganin bai kai ya samu ba,kuma ace ya zama nasa,kai kuma shari'a ta shata maka layi da shi. Ni na yafe musu, kuma don Allah ku yafe musu ko domin albarkacin 'yan yaransu.
Suka kalli juna yace "Kinji ko Hajiya, yarinyar nan a kwai ta da ƙume abu a zuciya, to kafin mu yafe sai ki faɗa mana abinda suka ce."
Hajiya ta É—aga masa hannu, sannan ta ce an yafe musu, Allah ya yi miki albarka.

Na soma tunani cewa ƙarya ne baya nema da Naman Anisa, domin na bincike wayar shi babu alamun sunan ta duk da cewa akwai lambobin da ya ajiye su da haruffa.

Kwanaki uku bayan wannan badaƙalar sai Hajiya ta aiko Juma musamman ta kira ni, na zo,tace min "Abinda ya sa ta kirani,tana son ne ta min wani taimako ta min gata, amma tasan cewa bazan faɗawa Shamaki ba." nace To, tace "Nasan kina samun komai a gidan nan tafannin ci da sha haka ne?" Nace haka ne. Tace "Amma baki da kuɗi ko taro mijinki baya baki ko sisi ko yana baki?" Nace baya bani. Tace "To zan saka dire ba zai kai ki gidan wani malami zan biya shi zai miji aiki yadda zaki samu damar karbar wani abu a gurin shi." Na ɗago kai cikin mamaki na kalli Hajiya. Tace kina mamaki ne ko?" Babu abin mamaki ina son ya zama sai yadda ki ka ce masa zai yi, kuma zaki nesan ta shi da waɗan can mata.Ina jin takaici iyayenki ya kasa yi musu wata kyauta a matsayin shi na ɗan Alhaji Baita." Ina son ya sai miki mota ki ke hawa da kanki." Yanzu dai je ki shirya." Na tsurawa yatsun kafa ta ido ina kallo,nazarin maganar Hajiya nake yi, kamar ba ita ba mai mugun son ɗanta da ɓoye laifin shi ita ce zata ce wai in mallake shi kuma ita zata biya.
Bana zaton za a samu wata uwa ko da mahaukaciya ce da za ta aikata hakan. Wata zuciyar ta ce ko kuma duk cikin gwajin ne. Hajiya ta katse ni. Ki tashi ba'a.bori da sanyin jiki.
Na sunkuyar da kai nace Hajiya ki yi haƙuri, ba sai mun yi masa haka ba, bani da bukatar kuɗi a hannu na, domin yana yin komai yadda ya kamata,rannan cewa ki kayi ya bani abin barka na gidan abokinsa kuma ya bani na kai. Iyaye na kuwa aure suka turo ni suka faɗa min cewa ibada ce zan yi har ma suka tabbatar min anan zan samu aljanna baza su yafe min ba in har suka ji layin da na koma.
Kuma Hajiya yana yi miki biyayya ni kuma yana sona, don Allah kar mu yi masa komai ba zan iya cutar da shiba. Harara ta jeho min, sannan tace Kin Fini sanin abinda ya dace ne?" Nace a a,tace to duk ranar da na saka lokaci dole kije ayi masa wannan aikin." Na ɓata rai ban kuma magana ba. Tace ni kike ɓatawa rai dan zan taimake ki da dangin ki." Tashi ki bani guri. Na miƙe na tafi ina mamaki.

Wai Hajiyar da na sani ce kuwa,kai abinnan fa da ban tsoro. Sam ban faɗawa shamaki ba,sai dai Hajiya na ɗan ja jiki da zuwa gurinta isai in yana gurin, duk da cewa bata sake yi min maganar ba. Umman mu ta sanar da ni tana son ta zo ranar lahadi domin ta ga ɗakina tunda bata taɓa zuwa ba, nace Allah ya kai mu. Da dare ina yi wa Hajiya tausa suna hira da Shamaki nace Yawwa Hajiya Ummana tace zata zo ranar lahadi ta ziyar ce mu. Ta ɗago ta dube ni "Wace ce Ummarki?" Yau ne naji na fara jin haushin Hajiya domin zan jure ni amin komai amma bazan jure a ci zarafin iyayena ba. Shamaki yace mahaifiyar su mana. Ta kalle shi "Ta sanar da kai kenan?" Yace nasan dai ita ce Umman su.. Na kasa ɗago kai dan haushi. Yace Allah ya kaimu amma dai harda su Jamila zata zo ko?" Ya tambaye ni,kamar yana son ya gane ko raina ya ɓaci ne ko kuma ya san cewa ba ayi min adalci ba. Hajiya tace "Yaushe ki ka ce ma?" Na dube ta cikin murmushi takaici nace Hajiya ka wai zance ta barshi ba sai ta zo ba in zuwan nata akwai wata damuwa ne, ni sai in saka lokaci inje ta ganni. Hajiya tace "Tace yi 'yar dariya tare da faɗin yau dai na ga hassala a fuskar ki Rabi'atu ba yadda za a yi mahaifiyar ki baza ta zo gidan ki ba, domin gidanki ai nata ne. Sai ki faɗi abinda ya kamata a bata in zata tafi." Nace ba sai an bata komai ba Hajiya, ita kawai zata ziyarce mu ne.
A É—aki Shamaki yace ki yi hakuri banji daÉ—in yadda Hajiya ta yi ba." Nace haba ya wuce ka wai. "Yace ki tuna min ana gobe zata zo,nace nan da kwana uku ne zan tuna maka.
Yace "Ina ta son mu yi wata magana kuma ina ta tunanin ta ina zan ɓullo wa lamarin ne.." Nace ka faɗa min mana. Yace kin san maganar Azima?" Nace wace maganar a ciki ta auren ku, ko ta ɓarin da ta yi? Ya zaro idanun cikin rawar baki ya ke tambayar "Waya faɗa miki?" Na kama tafin hannun shi na sarƙafe cikin nawa nace nifa 'yar gidan nan ce karka manta, dole zan sani, amma ka sani wajibi ne in rufe duk wani sirri na gidan aurena, wannan amana ce. Yace "Amma me kika sani game da ɓarin da ta yi?" Nace bansan komai ba banda ɓarin. Yace "An saka auren mu wata huɗu ina fatan baza ki shiga damuwa ba." Yawun baki na ya tsaya cak. Gaban sai wani irin duka ya ke yi. Na saɓule hannu na daga na shi, nace a haba ba wata damuwa Allah ya baku zama lafiya, amma dai ita ma a gidan nan zata zauna? Yace "To shine dai har yanzu ba mu gama tattaunawa da Hajiya ba." Hawayen da nake ta riƙewa ya kwaranyo min kafin in goge har ya gansu, ya tashi ya je ya kulle ƙofar ɗakin shi ya zare makulin ya saka a aljihu. Ya zo ya zauna kusa da ni ya saka hannu ya ɗago fuskata ya saka yatsa yana share min hawayen yace "Nasan zaki fice ki tafi dakin ki ne kije kiyi ta kuka, bayan kin yi min alƙawarin baza ki ɗaga hankali ba." Na kirƙiri murmushin yaƙe, hawayen suna sake kwaranya,nace kayi hakuri ina ta ƙoƙarin inga cewa na tsaida hawayena amma na kasa. Yace, "Karki damu fa, ko mata nawa zan kawo Baby kinsha gaban kowace a zuciyata, kuma Baby ke ce mace ta farko da nake shakkar in ganta a damuwa bayan Hajiya. Ki tattala hakan Baby ina da tabbacin za muyi rayuwa mai tsawo da tsawon rai." Ya ɗago fuska ta muka haɗa ido "Kinsan me yafi damuna?" Na girgiza kai, ya kai hannu ya ja doguwar rigata ya zura hannu ya shinfiɗa shi a tafin cikina, na ƙosa inga kin samu ciki,na fara tsoron ko akwai wata matsala." Nace duka wata uku da kwanaki ai ba 'a jima ba." Yace "An jima mana, mace bata wata a gidan nan sai ta ɗauki ciki fa." Nace to muyi addu'a jinkirin ya zama alkhairi kuma duk ga yara a gidan. Yace "Wallahi ban taɓa samun kai na da son ganin mace da ciki kamar ke ba." Nace Allah ya bamu masu albarka.
Koda ya ci gaba da sarrafa ni domin biyan buƙatar sa yanayin kishi bai barni na taimaka masa ba kamar yadda muka saba, hasali ma hawaye na na ci gaba da zubdawa har ya samu kansa. Ya dube ni yace "Yau dai ni nayi kiɗa na da rawata ko Baby?" Nace kamin afwa da uzri. Yace shike nan muje muyi wanka.

Gaskiya ina da kishi mai yawa ƙiriƙiri na kasa bacci kuma duk da na tashi na yi sallar dare na faɗawa Allah damuwa ta hakan bai hana zuciyata saƙamin cewa in nemi saki daga gare shi ba. To amma ya zanyi da wutar sonshi da ke ruruwa a zuciyata.

Ranar Lahadi tamkar ranar salla ce a gurina tun safe kowa na gidan ya fahimci hakan Shamaki ya ce to in har Umma zata zo da wuri zata iya samu na, nace bari in kira inji. Jamila na kira na tambaya ta ko da wuri Umma zata zo, sai tace sha biyu zata zo ta dawo ƙarfe biyu.

Ɗaya saura wayar ɗakina ta yi ƙara,na ɗaga Hajiya tace "Ki zo ga Ummanki da murna nace To.
Chapter 33 · 0% Book details