← Book details Hamshakiyar Uwa Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 34

Sashe 3

Hamshakiyar Uwa Part 2 Complete Hausa Novel · about 4 min read

Shamaki ya buÉ—e flas É—in abinci ya soma zuba farar shinkafa, idanun Hajiya suna kansa har ya gama sannan ya zauna ya fara ci yana son tuno wane labari ne Hajiyar ta fi maida hankali sosai. Kodai labarin mahaifin su,ko kuma dai labarin kasuwancin su daidai lokacin wayar shi ta soma ruri, ya kalla Soyayyata . Ya É—ago ido ya kalli Hajiya ta tsare shi da kallon tuhuma dole ya yi wayar a gabanta domin fidda kansa. Ya yi É—an murmushi bayan ya gama wayar ya tauna abincin da ya zuba a bakinsa zai yi magana,sai ta É—aga masa hannu, gama cin abinci, ka fi kowa sanin cewa bana son ana magana lokacin cin abinci, ka gama sai kamin bayani kamar haka..
Duk saboda son yarinyar ne ka soma munafurta ta har ka shirya zama da 'yan uwanka saboda ni? Sannan ka ciro min fayal ɗin da kake ɓoyewa da hannunka har kana zubar da su dan kawai in rasa gane wanene ka aje gefe. Sannan ka min bayanin dalilin yin duk wannan alamun na rashin gaskiya da kake yi tun da ka shigo gida, kuma ka faɗa min da wa ka yi waya da ka shiga ɗaki! Cokalin da ke hannun Shamaki ya faɗi abincin ya zube masa a riga. Yawun bakinsa ya ƙafe sannan ya tsaida idanun sa akan Hajiya cikin tsananin firgici.

🖊️🖊️🖊

️*HAMSHAƘIYAR UWA🧕🏻*

*NA*

*HALIMA ABDULLAHI K/ MASHI*

_PAID BOOK_
_Kuɗin karatu ₦600_
_Account number 0700549935 Halima Abdullahi Access Bank a turo shaidar biya ta wannan number 08140004302 ko katin Mtn_
_Phone 08140004302_

*DOKA*
_Ban amince wani ya É—ora littafin nan a wani Social media ba,ko a maida mini shi Audio ba tare da iznina ba yin haka daidai yake da fuskantar fushin hukuma. A kiyaye_

*Masu son a Tallata masu hajarsu suyi magana ta wannan number 09068032427*

*Page 12*

Na isa gaban Abba cikin tsoro na zauna, duk jikina babu inda baya rawa, ina da tabbacin da "Abba zai ce an fasa ba Yaya Aliyu ni, bana ko shakka zan iya faɗuwa a gurin sumammiya. Sai naji ya tausasa murya ya ce "Baby" Cikin rawar murya na ce na'amm Abba. Yace "Kina ganin baki da wata damuwa in har aka ɗaura auren nan aka kai ki gidan yaron nan a haka babu kaya ko kuwa kina ga akwai wata damuwa in roƙe shi ya ɗan ƙara mana lokaci muga abinda Allah zai yi?" Na sauke wata wawiyar ajiyar zuciya. Sannan nace Abba ba ni da wata damuwa akan haka, ai munyi maganar da shi ya ce ai duk al'ada ce, kuma ya ce min zai siya in ya samu kuɗi. Abba ya daka min tsawa "Ke! ni ban tambaye ki dogon labari ba, abin da na tambaye ki kawai shine, zaki zauna da mijinki lafiya ko da ba mu samu munyi miki kayan ɗaki ba?" Zan zauna. Na bashi amsa da sauri kamar ina jiran tambayar. Umma ta fito daga ɗaki tace Sannu Baban Babu nifa gaskiya bazan iya kai yarinyar nan gidan miji babu kayan ɗaki ba, kodai ka je ka ciyo ko bashi, ko kuma ka yarda muje ka saka hannu a wancan na tallafin a karɓo, baka da shi, to menene naka na yin girman kai? Abba ya miƙe "Salamatu" ya nuna Umma da yatsa cikin tsananin fushi wanda ban taɓa gani ba, yace ki shiga hankalin ki da ni, in ba haka ba kuma zan yi matuƙar baki mamaki domin zaki tafi gidanku ki haihu a can , ni kuma in aurar da 'yata cikin kwanciyar hankali. Jamila ta fito da sauri ta nufi gurin Umma ta riƙe mata hannu ta na cewa "Umma kiyi shiru: don Allah. Ni kuma kuka ne ya suɓuce min na kasa furta komai, saboda ni iyayena suna sa in sa abinda ban taɓa gani ba tunda na ta so. Kamata ya yi ince su yi haƙuri na fasa auren ma gaba daya, amma yadda nake ji koda tafiya Umman zata yi ba zan iya furta hakan ba, shin dama haka son yake ? Da numfashi yake kamar wani bala'i ko kuwa nawa son ne ya zo a haka? Muryar Umma ta katseni. Lallai Abubakar Allah ya kawo mu lokacin zaka faɗi haka tsakanin ni da kai, to ni kuma da inga aure nan a haka gara ayin bana gidan nan, na yarda da haka. Amma in ka tashi ka bani saki uku ras yadda ba sai na dawo ba.. Da sauri nace Umma kuyi haƙuri saboda ni ba zaku rabu ba. Ni gaba ɗaya ma na fasa au! au!! Sai na samu kaina da kokowa da numfashi na matsawar na furta kalmar zan iya mutuwa. Jina nayi na kai ƙasa ina wani irin numfashi, ina ta kuma ƙoƙarain furta na fasa auren kuma ina jin salatin iyayena kamar daga can nesa, sannan ga muryar Jamila tana kiran yaya Baby! Zuwa can kuma sai na daina jin komai.
Chapter 3 · 0% Book details