Sashe 31
Hamshakiyar Uwa Part 2 Complete Hausa Novel · about 4 min read
Na gyara zama,ta ce Rabi'atu jiya ya muka yi dake anan gurin? Na ɗago na dubeta ina ƙoƙarin tunawa, nace munyi magana da yawa musamman ta aurensa da Azima. Tace "Yawwa amma ya muka rabu?" Nace kince kar in nuna masa munyi maganar. Tace Yawwa to kuma ya akayi kika yanke masa irin wannan hukuncin na azabtarwa?" Nace Hajiya wallahi yadda muka yi maganar nan a nan gurin wallahi a nan nabarta. Bance banji zafin kishi ba,amma wannan ba laifi bane dan zai ƙara aure zan bashi duk wani goyon baya Hajiya wallahi bazan ɗaga masa hankali ba.
Tace to faÉ—a min menene ya yi miki?"
Na sunkuyar da kai nace Hajiya kiyi hakuri nasan Shamaki ɗanki ne,kuma kina sonshi fiye da kowa, amma ni kuma mijina ne akwai wani sirri tsakaninmu wanda ya kamata in suturta shi daga ni sai shi sai Allah. Ina neman alfarma ki bar wannan maganar ta wuce a gurina ki ƙara yi masa addu'a kawai. Yau ce rana ta farko da naga jikin Hajiya ya yi sanyi harma ta rasa abin faɗi na kusan sakwan talatin. Sannan ta ja wani dogon numfashi tace, "Ki sani riƙe abu a zuciya yana haifar da ciwo,tattauna Matsala da wani yana rage damuwar kuma ni ce mafi dacewa ki tattauna wannan damuwar da ni." Nace Hajiya dole ne mu koyi yadda zamu kashe mu rufe domin samun kwanciyar hankalin ki, duk da ban kasance likita ba, a shekarun ki yanzu bakya buƙatar duk wani abu da zai tada miki hankali. Tace "Babban abinda ya fi komai ɗaga min hankali shine inga Shamaki a damuwa, ina yin kowane irin abu dan in samar masa da kwanciyar hankali aurenki misali ne." Na yi shiru, ina tunani Hajiya tana yi wa ɗanta makauniyar soyayya wadda ta sa sam bata iya hango matsala. Na dube ta, zan yi iya yi na inga bai shiga cikin wata damuwa ba daga yau. Naɗaga yatsa kamar mai ɗaukar alƙawari. Bata ce ƙala ba ta ɗaga waya ta kirashi,ya zo ya zauna yana satar kallo na. Tace "Shamaki matar ka ta dage akan babu komai da ka yi mata, sai dai ina mai baka shawara ka yi ƙoƙari ka gyara abinda ka ɓata a idanunta. Ya kalle ni, na yi ɗan murmushi ka yi hakuri da yanayin da na saka ka a ciki. Shi dai idanu ya zuba min yana kallona. Anisa ta shigo ta nufi gurin Hajiya da littafi a hannu ta gaisheta sannan ta gaida Dadynsu,sai ta dube ni Momy ina kwana, ta zauna kan cinya ta,tace Momy Anty Azima bata yi min Homework ba. Na amshi littafin ina dubawa, nace to zo muje gefe mu yi. Na koya mata Rahin ta zo ta tafi da ita domin yi mata shirin makaranta. Na dubi Hajiya suna magana ƙasa ƙasa da Shamaki nace zan dawo kafin su Juma su haɗa abin karyawa.
Lokacin da ya shigo domin shirin tafiya kasuwa ina gyaran gadon shi, ya tsaya ya harÉ—e hannayen shi yana kallo na, na ce akwai wani abu ne? Ya girgiza kai sannan ya shige banÉ—aki.
Na fito masa da kaya kamar yadda na saba ya shirya tsaf na ɗauki jakarsa na rataya a kafaɗa. Ya janyo ni zuwa jikinsa ya rungume ya sa hannuwan shi guda biyu ya ɗago fuskata ido cikin ido muke kallon juna, yace "Baby yanzu bazaki faɗa min.. Nasa tafin hannu na narufe mishi baki tare da faɗin shissss ya wuce babban baƙo. Muje ka tafi Allah ya tsare gabanka da bayan ka. Yace kimin alƙawarin cewa bazaki yi kuka ba." Nace bazan yi ba. Ya sunbaci goshina sannan muka tafi tare.
Cikin satin na zama cikin taka tsantsan kuma na duba wayar shi naga 'yan mata sun masa magana amma duk bai bada amsa ba. Babu daÉ—in ganin haka tabbas an É—an samu ci gaba domin hakan da ma ya taimaka inda na tada bala'i da sai ya tada borin kunya ya yi bala'i kuma ya murje harma ya ke min gadara a gabana sai ya yi wayar shi tunda ya lura bazan iya komai ba.
Matar Abokin shi Alhaji Shamsu ta haihu , yace in shirya da dare zamuje barka. A gaban Hajiya ya yi maganar na ji daɗi domin ina son muna ɗan fita da shi. Hajiya tace ka je kai kaɗai ita kuma anjima ta shirya direba ya kaita ka bata abin barka. In kuma taron suna zata je shikenan sai ta bari sai ranar. Ya kalle ni kamar yana son yaga yadda zanyi tunda yasan ina son mu fita da shi na sha faɗa masa cewa ina son mu ɗan fita ko a ƙafa ne, sai ya ce inyi hakuri in ya samu lokaci ƙasar waje ma zamu fita.