← Book details Hamshakiyar Uwa Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 34

Sashe 16

Hamshakiyar Uwa Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Amma na damu kasancewar bamu karya tare da ango na ba,
har tara saura bai shigo ba, na ɗan kashin giɗa a gefen gado na kira wayar Umma, kamar in shiga ta wayar in ganta, idanuna suka kawo ruwa lokacin da ta ɗauka, nace Umma ina kwana? Ta amsa muka gaisa, na tambaye ta Abba tace ya fita. Nace zan kira shi,ta ce su Jamila za su zo anjima ko ina son wani abu?".Na ce tazo da su Jafar da Baba Habu. Umma tace "To dama suna ta mitar basu je ba." Nace to. Na kira Abba na gaida shi, yana ta min nasiha, hawaye na bin kumatuna. Muna yin sallama Shamaki ya na shigowa, ya tsaya yana kallo na. "Ke da wa kike waya naga kina kuka?" Na miƙa mishi ya amsa ya ce A"bba ki ka kira." Ya zauna yana share min hawaye, "To menene abin kukan kuma?" Ya sakar min cakulkuli, na saki dariya tare da faɗawa kan gado. Yace da fatan kin karya dai ko?" Cikin zolayar nace najira ka baka dawo ba, sai nace ƙila acan ka ke ƙari. Ga mamaki na sai naji yace kamar kin sani, bana iya karyawa da kowa sai da Hajiya, abinda zai baki mamaki ko ƙasar na bari to na bar karin safe har sai na dawo." Na ɓoye mamakina sannan nace abin birgewa ina son irin soyayyar nan tsakanin ɗa da mahaifi.
Sai naga ya saki baki ya zuba min ido gaba ya faɗi nace na faɗi ba dai-dai ba ko? sai ya sa hannu ya kuma janyo ni zuwa jikinsa yana faɗin Allah na gode Allah yarinyar nan liɗifi kamin da ka bani ita. Nace kamar ya ke nan fa? Yace A kan karin kummalon da nake yi tare da Hajiya a cikin matana akwai wadda tace wai in auri uwar tawa, dukkan su kamar irin wannan ranar ba wadda bata min ƙorafi ba. wannan mummunar kalma tafi komai ɓata min rai har kuka na yi." Nace bata kyauta ba. Yace ke kaɗai ce baki min ƙorafi ba kuma ban gani ko a fuskarki ba, don Allah kar ki canza kinji?" Na kwantar da kai ƙirjinsa kar ka canza min kaima. Yace insha Allahu.
Yace "Bari inje in shirya zan fita kasuwa." Na dube shi ba hutu? Yace matane zasu cika gidan." Nace haka ne, to abinci fa? Ya kama kumatuna, "Za a kai min har kasuwa yau zanci jagwalgwalon Baby Allah ya sa Hajiya ta ci ina roƙon ki ki ƙure basirar ki, abinda baki gane ba ki tambayi Juma." Nace to kuma zan baka mamaki.Ya miƙe zai tafi, nace Yay sai na rufe baki na. Ya saki dariya bari Hajiya ta jiki garama kin yi saurin samo min suna ko kice Shamaki. Na matse kafaɗa bazan iya cewa ba. ."Amma jiya ki ka ce Shamaki Aliyu dan girman Allah! Na nufi gurin shi da gudu na ɓoye fuska ta a cikin shi ina faɗin don Allah ka dai na ɗazu wai har a gaban Hajiya kuma wai zaka faɗa? Muje in taya ka ka shirya ka tafi. Yana dariya yana faɗin "Ok kina korata neko? Muka nufi ɗakinsa, naga an cire zanin gadon an yi shinfiɗa an gyara komai. Nace waya gyara ɗakin nan? Yace "Menene" na yi shiru, yace "Bakya son a gyara ne?" Na ɗaga kai alamun e. Yace"Bazaki iya gyaran ɗakin nan ba." Saboda me? Na tambaye shi tare da zuba mai ido. "Ɓangaren nan yana da girma za a kawo miki mai aikin da zata kula da naki sasan da kuma wasu buƙatunki." Nace kar a kawo min, sannan kuma abar min gyaran nan gefen na ka a hannunna domin Umma da Abba sun faɗa min aikina ne in kula da kai da duk wani abu naka da ka aje a gidanka. Sun ce aljanna ta a nan zan nema amma kai kuma kana son ka hanani samun wannan damar. Na ƙarasa maganar cikin tura baki a yanayin shgwaɓa. Ya aje rigar da ya cire zai shiga banɗaki, ya kama hannuwana guda biyu. "Zanyi ta addu'a ga su Umma ina gode musu da irin ginin da suka min ta tarbiyyar da suka miki, ni suka taimakawa da yarana da zaki haifa min ƙilama har da waɗanda ba ke ki ka haifa ba. Allah ya sa jiyan nan mun samu Zeena." Na rufe fuska ina faɗin shiga wanka kafin ka canza maganar kuma ni ce zan fito maka da kayan da zaka sa. yace "Ni da kayan duk naki ne yadda kika dama haka kowa zai sha, ina nufin duk yadda ki ka shirya ni haka kowa zai lalle ni."

Na buɗe durowarsa na tsaya kallon kaya, kaya iya kaya, na yi ta buɗe ƙofofin ina kallon ko wane ɓangare, ɓarin agoguna ne da gilasai na ido, abin dai ya cika ni da mamaki. Na fidda masa wata shadda mai kalar sararin samaniya da malun-malun na je duniya hulunansa na fidda wadda zata dace, har agogo da gilas na cire komai.
Yana shafa mai ina kallo yadda suma ta kwanta a sassan ƙirji sa, zuwa ƙwaurin sa, abin ya matuƙar birgeni ni. Ya kalle ni ta cikan madubi, "Zaki taimaka min a bayana?" Na miƙe tare da faɗin sani kawai zaka yi Ni nawa aikatawa ne, na lakuci mai ina shafa masa a baya, ya lumshe ido Baby tsigar jikina tana ta shi, nace in bari ne? Ya ce "A 'a kimin sosai." Ya juyo ya rungume ni, "Baby komai na ki ya yi min." Na yi murmushi. Mu
Haka ya saka kayan na wanke shi da turare, na ɗaukar masa jakarsa mai ɗauke da laptop. Na kai shi har bakin ƙofar da zai shiga falon Hajiya. Yace "Yaya Baby a iya nan?" Nace Nice Yaya kuma? Hajiya zata ga cewa daga zuwana har na rako ka zai zama kamar na zaƙe ne. Ya lakuci hancina tare da faɗin soyayyata mai wayo.
....
Da na dawo zan shige zan shige gurina sai naji kukan yara, sai na samu kaina da nufar gurin su. Rahin ta yi musu wanka tana ta fama da su zata sa musu kaya amma Mubina bata son kayan da aka ciro musu, ita leshi za a sa mata, Anisa kuma ba wannan takalmin take wa kuka ba, sai an canza. Meema tana kicin kicin saka nata kayan. na shiga nace me ya same su? Cikin girmamawa Rahin ta ce Rigima suke jin yi Anty kinga ga kaya wai kowccen su bata so." Na ce to ki barsu kowa ta ɗauki wanda ta ke so mana ina ganin ai kamar ba matsala ko? Rahin ta ja baya tace "To ku zaɓa amma don Allah kar ku zubo kayan domin shirya su ba ƙaramin aiki bane durowa uku, aiki ne." Nace kije kusa sai su nuna miki sai ki ciro wa kowaccen su yadda ba zai ɓaci ba ko? Ta ce "To " Yara suka bini da kallo sannan suka kasa nuna wanda suke so. Nace In zaɓo muku? A tare suka ɗaga kai.
Na dubi Rahin anko ake yi musu kullum?. Tace "Wani lokacin suna sa daban daban." Nace Hajiya tafi son su sa kaya iri ɗaya? Tace "Ban taɓa jin Hajiya ta yi magana akan haka ba ."
Na kama hannun su suka nuna min duk abinda suke so, nace to muje É—akina sai in shirya ku a can. Da sauri suka yarda suka bini Rahin ta bini da kallo. nace ki gyara musu kayan kawai.

A Kan gadona nace su hau Meema tace "Hajiya ta hanamu tace gadonmu kawai zamu hau amma banda na manya." A raina nace tofa! Sai nace ai Hajiya bata nan kuma ni bazan faɗa mata ba. Sai suka kalli juna, Mubina ta zau a kan kafe ɗin gaban gado, Meema ta ce "Hajiya ta faɗa mana in bata nan Allahnta yana nan, kuma zai ganar da ita inhar muka yi ba daidai ba. Na sauka kan Kafet ɗin batare da na sake magana ba, nace bari a fara shirya Anisa ita ce 'yar ƙarama ko? Meema ta ɗaga kai, sannan tace "Anty ke ɗin wacce ke ma nan gidan ki ke?" Nace ni Mominku ce, ba sunana Anty ba. Mubina da Anisa duk suka kalle ni , Mubina tace "Kema a nan gidan ki ke?" Nace e mana ga ɗakina ma. "Kece Momin da Dady yace zaki zo in anyi biki?" Inji Meema. Nace la! ashe ya faɗa muku, to ni ce. Anisa tace "To Momy anyi bikine?" Nace anyi jiya yau ma za ayi. Suka fara murna." Na gama shirya su muna ta 'yar hira suna min tambayoyi na shirme ita biye musu domin ni ina son hira da yara don haka naji sun shiga raina domin na lura suna da wayo. Na gama musu fesa musu turare, Meema ta kalli wayata "Momi in ɗauki wayar ki?" Nace me zaki yi da ita? Mubina ta amshe da cewa "Akwai game a ciki?" Nace babu amma ku zo in ɗauke ku hoto mukayi hotuna ni da su. Nace to sai ina? Suka ce za suje gaida Hajiya ne. Nace to ai ni baku gaishe ni ba, suka ce Hajiya ake fara gaishewa sai Dadi shikenan sai mu gaisheki. Nace to haka ya yi daga nan su gaishe min da Hajiya. Suka tafi ina bin su da kallo.
Chapter 16 · 0% Book details