Sashe 14
Hamshakiyar Uwa Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Da mata za su san darajar su game da wannan daren da sun kasance suna ririta kansu tamkar dai ƙwai a kan kanfa, baza su yi guje guje ba, bare wani hawa keke ko bishiyoyin kamar yadda likitoci suka faɗa. To har bare su biye wa wani azzalumin namiji ya rusa musu rayuwarsu y a goge sumu wannan tarihin da za su kafa na daren farko kafawa ta har abada.
....
Ta kama hannun ta riƙe shi a cikin na ta tace "Abinda kawai nake so da ke shine ki cire tsoro kina son mijinki na tabbata da haka, sannan ki zama mai juriya a duk yanayin da yazo miki a wannan dare, sannan duk da cewa baƙon al'amari ne zai riske ki, ina son ki bashi haɗin kai da goyon baya hakan zai rage miki shan wahalar da ki ke jin tsoro, sannan kar ki manta da addu'a baki sani ba ko da Allah zai baki rabo a yau. Ina fatan kin gane karatun da ba kowace uwa ke iya zaunar da 'yar ta ta koyar da ita shi ba wannan karatun ina karantar da iya 'ya'yana ne amma yau na karantar da surukan kuma ina fata kin gane." A hankali nace na gane. Tace "Yawwa akwai wani abin kuma ina zuwa" Ta kira Juma ta zo da sauri tace gani. Hajiya ta ce, 'Kije ki dafa min madarar shanun nan da aka kawo ɗazu kofi ɗaya ki zuba zuma ki kawo mata yanzu." Juma ta ce to, ta juya da sauri . Ni kam ina cike da mamakin wannan al'amari bansan yadda zan fassara Hajiya ba, kuma ban iya gane domin ni yi don ta taimake ni ko kuwa domin jin daɗi da nutsuwar ɗanta, koma don me ta yi dai na yaba mata har ga Allah, kuma ta ƙara girma da kima a ido na,ta sanar da ni wani ilmi wanda hankulan mutane ba sa kaiwa gurin. Sannan na lura gidan ba'a magana mai ƙarfi sam sai kuma sai kaga duk suna ji. Shamaki kusan so uku in ya zo zance da nayi magana zai ce in ke yin ƙasa da murya ba a nesa yake ba.
Hajiya ta katse min tunanin da cewa "Kina yin al'ada ne?" Na girgiza kai alamu 'a 'a, ta ce "Yawwa in kin in komai da zai faru tsakanin ɗa mijinki ya faru to kuma kar ki zama raki da ƙazanta, ki tashi ki gyara jikinki kar ki kwana cikin ƙazanta na san dai tunda da karatunki ba sai an koya muku wankan janaba ba, niyya ce kawa ta raba su da wanda ki ke yi a duk wata. Na sunkuyar da kai sannan kaɗa kai alamun haka ne.
Juma ta kawo madarar Hajiya ta amsa ta miƙamin tare da faɗin maza shanye yanzun nan zata riƙe miki ciki kuma zata taimaka miki sosai gurin saukar ni'ima haka zai rage muku raɗaɗi ke da shi."
Na kurɓa na ɓata rai. Tace "Maza shanye, ki ɗauke numfashin in bakya ra'ayinsa kar ta tada miki zuciya." Haka na shanye duka na aje kofin, tace "Yawwa Allah ya bada sa'a. Juma zo ki kai ta Allah yi muku albarka dukan ku.
Hannuna Juma ta kama muka nufi ɗakina tace 'yarnan kin shigo da ƙafar dama, alamu suna nuna cewa Hajiya ta yarda da ke ke kuma sai kiyi ƙoƙarin cin waɗansu jarabawa da zata miki na tsawon shekara ɗaya in kin tsallake kin zama matar gida, in kin kasa sai ki bi sauran matan mijinki ki koma gidanku koda kuwa kin haihu ki dire abinda ki ka haifa. Gabana ya faɗi na maimaita kalmar Jarabawa a zuciyata. Ta dafa i lokacin da muka iso ƙofar ɗaki na, naga har kin tsorata, zan baki satar amsar jarabawa guda ɗaya, ki zama mai gaskiya da faɗin gaskiya duk rintsi ko da kin aikata ba dai-dai ba, ya kasance ya kasance kin faɗi gaskiya. Tace To.
Zantukan Hajiya da na Juma sun yi matuƙar tasiri a zuciyata har ma naji na rage fargaba sannan na samu ƙwarin gwiwar miƙa wuya. Sai dai kuma zancan Juma ya zo min da sabon firgici. Ta sa hannu ta ƙwankwasa tare da sallama. Ya bata izni ta murɗa ta buɗe sannan ta koma baya alamun in shiga. Yana zaune a kan kujera yana kallon TV ya ke yi, ya canza kayan shi zuwa baƙar Jallabiya mai surfani ruwa zaiba, ya yi kyau sosai. Na nufi kusa da shi na zauna, bazan iya fassara yanayinsa ba, amma nafi zaton ya ji haushi ne. Nace Yaya, ya dube ni "Na '"am Baby in zo muje ne in kai ki gidan?" Na sunkuyar da kai ina wasa da gefen lafaya ta, ka yi haƙuri bazan ƙara ba. Ya ɗora ɗan yatsan sa a. kan leɓunana, ki daina bani haƙuri. Ya kama hannuna "Tashi muje ki kici abinci zaki ci ko?" Na ɗaga kai alamun e. Na ɗaukar wa kaina alwashin bazan masa gardama ba. Ya kama hannuwa na biyu ya damƙe cikin nasa. Yace "Baby Wato shiyasa duk Duniya in aka cire Allah da ma'aiki sai Hajiya bana iya kai kuka na ga kowa, ba wani aboki ko wani ɗan uwa, ni ban taɓa zuwa mata da matsalata bata share min hawaye ba duk abinda ya ta so min ya shige min duhu gabanta nike kai shi kuma sai ki ga komai ya zo min cikin sauƙi.
Ina son ki riƙe ta a matsayi mahaifiya kuma kar ki ɓoye mata damuwar ki ko a kai na ne, sannan duk rintsi .kar ki koyi ƙarya komai nauyi gaskiya to ki faɗa mata koda laifi ki ka yi Ina son ki Baby
ina son mu zauna na har abada." Na ce Insha Allahu zan yi duk yadda ka ke so. Yace "Amma yanzu dai kina sona ko?" Na ɗaga kai, ya miƙe tare da faɗin Muje muci abincin.
Anjere komai kan wata shimfiɗa ta fata ga abubuwan tada kafaɗa a gefe, tsakiya an rubuta Amira sai aka yi hoton zuciya sai aka rubuta Shamaki. Ya buɗe flas ɗin kaji tare da faɗin "Al 'adar gidanmu tana shan banban da ta wasu ina fatan zaki jure, maimakon ki ga abokaina sun kawo kazar amarci da gasashiyar kaza sai ki ga Hajiya ta ta aiko ko?" Nace Ni bansan ma yaya ake yi ba. Ya yanko tsoka da wuƙa ya ce "Buɗe baki." Na sunkuyar da kai sannan na ɗago na karɓa. Haka dai mukaci kaɗan muka tashi, ya kama hannu na zuwa cikin ɗakin baccina ya soma warware min lafayar da ke naɗe a jikina tare da faɗin "Ki cire ta ki sha iska ko?"
Ya jefata kan gado na hankalin sa ya ɗauku zuwa gashin kaina, ya nutsa yatsun sa a ciki, ya ja zuwa ƙarshe gashi, na lumshe idanu ina jin wani yanayi mai cike da biyu, shuƙi da fargaba. Yace "Wai dama gashin nan da na gani jiya a gurin party na mu ne ba ciko aka yi ba?" Kai na iya ɗagawa domin bana iya fassara yanayin yadda ya kamata. Ya ce "Alhamdulillah kin boye shi a hijabi naji daɗin haka sosai yau na ganshi abin ya birge ni Baby ina son gashi da yawa.
Banyi magana ba. Ya sake ni "Ki cire wannan rigar ki yi shirin bacci sai ki same ni a É—akina." Bansan É—akin ba. Na faÉ—a cikin yanayin tausayi. Ya shafi kumatuna ki nemo É—akin mijinki." Na bishi da kallo ya fice.
Naje gaban madubi na tsaya bayan na cire rigar jikina na maida doguwa ta bacci. A madubina ina iya kallon jikina domin rigar babu abinda ta ɓoye. Gaskiya bani da wani shef na irin na mata, ɗan ƙuguna dai gashi nan haɗe da baya, haka ma ƙirjin kamar mai ƙirgan dangi, cikina kuwa sun haɗe da baya, sai naji ina fargaba r karma ya kalli surata ya yi daya sanin aurena.
A haka na zura hijabi na É—auki wayata na kulle É—akina na fita neman É—akin mijina kamar yadda ya ce.
Na gane ɗaya. ƙofar zata maida ka falon Hajiya, ɗaya kuma ta fita zuwa barandar gefena kai tsaye, sai kuma ga wasu biyu. Na tura ɗayar sai naga ta buɗe, na leƙa wani ƙaton falone na alfarma shigen na Hajiya.
Na shiga sai naga ƙofa biyu .na buɗe ɗayar sai naga wani dogon corridor ne, na bishi sai na hangi ƙofofi gudan biyu. Kafin ƙofar sai naga Window na tsaya jikin window na buɗe labulayen a hankali ɗaki ne ƙato mai ɗauke da gadajen yara guda biyar. Kowanne da fitowar sa ta saka kaya babba. A kwance yaran Shamaki ne suna bacci cikin kwanciyar hankali can gefe ga mai kula da su a nata gadon. Na yi musu addu'a kamar yadda Abbanmu ke mana in ya zo duba mu mun kwanta bacci, na tofa musu daga inda nike sai na juya. Tsaye ƙyam yana kallo na. Na ɗan daburce kamar mara gaskiya, nace ban iya gano ɗakin ba, Allah ya sa hakan ba wata al 'adar na saɓa ba. Ya kama hannu na, "Amma kin gano na yaranki ko?" Ya ƙara so ya ɗaga labulen ya kallesu, tun da ki ka zo kin haɗu da su?" Nace 'a'a. Yace "Na faɗa musu cewa Momyn su tana zuwa, san nan wancan gadajen guda biyu na ƙannen su ne, zaki haifa musu ko?" Na rufe fuska. Ya kama hannuna, "Muje ko za'dace tun a daren yau.
Ɗakin sa ba tarkace gadone gashi nan kamar suffar ƙwai kalar ruwan zaiba madubi manne a bango sai kuma tafkekiyar durowa ta shafe bango, can ga durowar takalma gata huluna kamar kasuwa, sai gefen gadon sa ga fitilar karatu da Alkur'ani a gefe, sai wani littafi Nobel.
Na ɗago na lalle shi. "Ɗakin ya yi miki ko kina son a canza wani abu?" Cikin jin kunya na sunkuyar da kai ashe yana kallona ina ƙarewa ɗakin kallo. "Kiyo alwala mu yi godiya da addu'ar samu zuri'a ta gari."