← Book details Hamshakiyar Uwa Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 34

Sashe 13

Hamshakiyar Uwa Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Takwas da rabi ina gyara fuskata bayan nayi salla, sai kiran wayata ya shigo. Cikin faɗuwa gaba na sa wayar a kunne ban iya ko sallama ba. Yace "Baby" a sanyaye nace na'am. Yace "Gamu nan shigowa yanzu ke da su waye?" Gaban ya sake faduwa naji kamar cikina ya karta. Nace su Jamila ne. Yace "Ok sai ki gyara sosai ki rufe jikinki nake nufi." Nace to. Yana aje waya Maman Iman tana ƙwankwasa ƙofa suka buɗe mata suka gaisheta kai tsaye ta shigo cikin ɗakin ɗayar mai min kwalliya ce. Tace Karamar mu babbar mu ga ango nan zuwa bari a gyara min ke.
Na gaishe su cikin kunya da girmamawa. Sannan nace shima yanzu ya kira wai zasu shigo. Tace Bari in ƙara in dakatar da su. Ta dube ni, ya naga duk jikin ki ya yi sanyi? Na yi ɗan murmushi nace ba komai. Tace "Ni dai sai kinyi kyau." Ta kirashi ta dakatar da su. Nan fa ta kuma gyare min fuska da kwalliya, aka turare min gashi da jiki, ta ɗakko lafaya tana cewa "Cire a layyace min ke cikin wanna lafayar." Mai kwalliya tace ina kika sai wanana lafayar? Tace kayan 'yan gayu ne DEEJANGALA ENTERPRISE kin san kayan su akwai kyau ga sauƙi, kuma abin birgewar kin ga wannan lafayar ta jikin ta, zai wahala ki ganta jikin wata.

Mai kwalliya tace don Allah zaki bani number ta. Maman Iman tace zan baki mana. Ni dai ina jin su na ta labarinsu, na É—au kyau kamar 'yar tsana. Maman Iman tace "Ki rufe min fuskar ki kar abokai su gane Kinji ko? Kya dai gaishe su ta cikin mayafin." Nace to. Sukayi sallama wayar ta tayi ringin, sai ta É—aga tana cewa, "Ku shigo ango mun. kammala"
Su Jamila suka .shigo suna buɗa fuskata suna leƙawa suna faɗin kyau da ƙamshi. Ni dai shiru na yi domin fargaba da wani irin tsoro suke gigita ni.

Cikin haka aka ƙwanƙwasa ƙofa suka amsa sannan Fati ta tafi ta buɗe Sai kurum naji ina faɗin Hasbunallahu wa ni'imal wakil. Suka zauna falo ina jiyo muryar Yaya yace "Jamila kiranta." Ta shigo ta ce Yaya Baby ki fito. Na ce na shiga uku Jamila wallahi tsoro nike ji.
Hannu ta riƙe min ta yi min jagora muka fita domin na ƙi buɗe ido. Tace "Menene abin tsoro, na bita muka fita, sai naji ta zaunar da ni a kujerar kusa da shi, ya kasance har ina jin ƙamshin turare sa. Shi kuma ya kashe ni da ido duk da fuskata a rufe a mayafi amma ina kallonsa.

......
Abokansa sun yi addu'o'insu sannan suka yi nasiha sannan suka haɗa da tsokana aje min kuɗi suka yi, sannan kuma suka ba ƙawaye suma wai na sayen baki, duk da basu ga fuskar amarya ba. Yaya yace "Alhaji Shamsu ku maida yaran nan don Allah." Alhaji Shamsu yace su fito mu kai su. Da sauri na riƙe hannu Jamila jikina yana rawa nace ke k i tsaya sai gobe. Tace "Yaya Baby so ki ke yi Abba ya kusan halaka ni, da duka kenan.' Yaya ce koma ki zauna kinji ai gobe zaku dawo ko Jamila? Na saka kuka yace "Jamila ki tsaya to sai ki kwana." Ya yi maganar cikin lallashi. Tace Wallahi ta sani in har na kwana Abba zai min dukan tsiya, ita tana nan lif a ɗakinta. Yace "To Kiyi haƙuri kibarta ta tafi. Nace to ka kira Abba ɗin ka faɗa masa. Ya ɗakko wayar ya kira amma tana kashe. Na sakar mata hannu jikina a sanyaye, na yi baya na zauna akan kujera. Suka tafi ya raka su bakin ƙofa suna wucewa maida ƙofa ya rufe.

Yasa hannu ya buɗe fuska. Tabarakallah Masha Allah. Ya furta cikin jin daɗi, ya saka yatsa ya ɗauke siraran hawayen fuskata ya tsugunna a gabana. "Haba Baby ai kin gama hawaye insha Allahu menene zai saki tashin hankali haka? Faɗa min damuwar ki yanzu?" Cikin rawar murya nace gida zan koma. Ya zauna "Me zaki yi acan?" Ya tambaye ni a gigice. Nace ba komai ni dai ina jin tsoro ne. Cikin mamaki yace "Tsoro kuma? To tsoron wa?" Na yi shiru. Ya ce "Ko dai kin ɓoye min ne dama baki so na?" Nan ma naƙi magana. Ya miƙe cikin damuwa. Ni kuma na ci gaba da ɗan kukana. Yace "Kinga bana son wannan kukan tashi in kai ki gida." Nace Abba zai dake ni ne. Sai naga ya yi 'yar dariya, yace "In har bazaki je ba to gaskiya ki yi shiru ki faɗa min abinda ki ke tsoro kuma ki faɗa min gaskiya in dama ba so na ki ke yi ba." Na rasa abin cewa sai dabara ta faɗo min, ai dama ya yaudara ni, nace Ka ɓoye min gaskiyar ka, kuma ni bani da ra'ayin auren mai kuɗi ina tsoron wulaƙanci bana son in zama bazawara ne. Sai naga ya yi dariya, sannan ya miƙe. "Zo muje. Ya kawo hannu zai kama nawa, cikin firgici naɗan ja baya, ya kalle ni har sai da naji wani iri. Yace "Muje" nabi bayan shi dai dai lokacin da Juma ta nufo sashen mu tace masa "Ga kaji amarcin inji Hajiya tace a kawo Uban ɗakina." Yace Je ki kai tana nan ko ta shiga ciki? Tace "Tana nan Azima tana mata tausar ƙafa Yace "Ta ƙafa.
Haka kuwa mun samu Azima ta na yi mata tausar. Ya rusuna cikin girmamawa, nima na yi kamar yadda ya yi. Yace Hajiya an samu wata ' yar damuwa ne. Ta kalli Azima "Je ki kwanta." Azima ta kllemu sannan ta fice. Hajiya ta zuba mana ido "Damuwa kamar ta me?" Ya ce game da yarinyar nan ne wai sai na kaita gida yanzu, tun da ta gane cewa ni É—an Ali Baita ne ban faÉ—a mata ko ni wanene ba, ya kwashe duk yadda mukayi tun kafin a É—aura aure da nace talaka nan nake so ya faÉ—a mata.

Hajiya tana gama ji tsaf, sannan tace "Ke yaya sunan naki ma?" Yace Rabi'a. Tace ɗago kanki ki dube ni. Na kuma sunkuyar da kai, ta ci gaba da faɗin "Ni ce mahaifiyar sa Aliyu Ali Baita. Ni ce Hajiya Zeena wadda dai ki ke ji, shine autana a cikin 'yay'anmu biyar da muka haifa da Ubansu Alhaji Ali Baita, ya gaji mahaifinsa a suna, ya gaji mahaifinsa a kuɗi ina nufin dukiya, ya gaji mahaifinsa a biyayya, ya gaji mahaifinsa a soyayya. shima bai taɓa neman wani abu na rasa ba, abu ɗaya ya kasa samu shine mace ta gari ko ince miki soyayyar gaskiya shine dalilin ɓoye miki asalinsa da ya yi kuma da ran yin hakan kwalliya ta biya masa kuɗin sabulu." Ta numfasa sannan ta ci gaba. "Kar kiyi alaye kice wai ke bakya son mai kuɗi, wannan labari ne domin mai kuɗi shine abin so, dalilin haka ne ya ɓoye miki cewa shi mai kuɗi ne domin ya samu soyayya ta gaskiya wanda muke sa ran cewa ya samu, bai kamata ki shigo da wata damuwa kuma a irin wannan daren na f arko mai albarka da tarihi a gurin duk wata ɗiya mace, ba." ta nuna ni da yarda ke bari in faɗa miki wani abu wanda ban taɓa faɗawa surukai na ba face 'ya'yan da na haifa. Ta ƙara rage sautin muryarta sannan ta nuna . Shatima tashi ka tafi, zan sa Juma ta r ako ta. Ya miƙe tare da faɗin sai da safe Hajiya , tace "Kana jina, karka damu kuma kabi komai a hankali kar ka manta da addu'a acikin ko a wane irin yanayi ka ksance." Ya ɗan shafa kai tare da faɗin i nsha Allahu Hajiya.

Yana bada baya tace, "Ban yarda cewa bakya son É—ana ba, domin ya cika ta ko ina É—a namiji. Zanfi yarda in kince kina jin tsoron daren farko, tabbas 'yarnan daren nan na fargaba ne ga duk wata mace wadda ta alkinta mutuncita ko akasin haka, wadda bata san namiji ba, tana tsorata ya zata kasance, a farkon al"amarin, haka kuma wadda ta san namiji a waje tana tsoron kar fa angon ya gane." "Rabi'atu" Na É—ago na dube ta. Sannan na sake sunkuyar da kai. Taci gaba da tambaya ta. "Kin kasa cin binci yini yau? " Cikin raunanniyar murya nace Wallahi ni ko yunwar ma bana ji. Tace da zaku fito gida me kikaji a zuciyar ki ? Na sunkuyar da kai.Tace "kar ki damu faÉ—a min ni mace ce, 'uwa kuma kaka. sannan ina son in tantance in har da gaske baki son É—ana bazan bari ya É—ora miki idda ba zan sa ya sahale miki yanzu kuma ya kai ki gidan iyayen ki. Sannan ki sani ba a min karya a gidan nan ki amsa min tambayoyi na gaskiya." Nace Ni ada ina son sa sosai amma yau gaba É—aya ji nayi aure ya fita a raina, ko da muka zo gidan nan zuwa yanzu sai naji na daina son shi,Ni tsoron sa ma nake ji gaba É—aya. don Allah Hajiya ki ce ya maida ni gida.

Ta saki murmushin mai sauti, ki nutsu kar ki ruÉ—a kanki, kin zo wani mataki mai mahimmanci a rayuwa wato daren farko. Ta matso ta kama hannu na tace,
"Yata bana manta irin wannan daren saboda kima da martabarsa, na ina faɗawa 'yayana martabar wannan daren domin na taɓa kasancewa a cikinsa, da a ce ni marubuciya ce zan rubuta in wallafa babban kundi mai shafi sama da dubu ina mai bayyana kima da darajar wannan daren. Don haka ina mai baki shawara kar ki bari vwannan daren ya tafi a haka batare da kin zama Hamshaƙiya a gurin mijinki ba, zama Hamshaƙiya a gurin miji shine ya ke sa ki zama Hamshaƙiya a idon duniya har zuwa kan ahalinki. Ƙila yanzu duk bazaki fahimci abinda nake son sanar da ke ba, sai nan gaba.
Chapter 13 · 0% Book details