← Book details Hamshakiyar Uwa Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 34

Sashe 17

Hamshakiyar Uwa Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Goma saura na saka hijabi na fita, na nufi gurin Hajiya na tsugunna na yi mata sannu da hutawa ta amsa, nace nazo gurin yin aiki. Ta nuna min ƙofa da hannu bi nan zaki samu su Juma a kicin.
Hajiya ta bi Baby da kallo cikin wani kallo na nazari, kamar kowace amarya dai haka take zuwa a nuna mata kuxin ƙarshe dai abinci ya ƙi ciyuwa, ta taɓa baki bari dai mugani, domin ta lura yadda abubuwa ke faruwa a safiyar yau ana samun ɗan banbanci da wanda suka faru a matan da Shamaki ya aura, a safiyar farko misali in ya bar gurinta ya nufi ɗakinsa don ya shirya ya tafi kasuwa ya kan ɗauki lokaci bai fito ba, haka ma dai a wannan karon, ya ɓata fiye da awa ɗaya sai dai banbancin da ta lura da shi shine fitowar wannan karon akwai banbanci da na sauran, a yanayin sa a fili yana cike da nishaɗi da kamanin angwaye, sannan kayan da ya saka ta tabbatar ba zaɓin shi bane domin tasan a guri ɗaya yake saka babbar riga shine in zashi wani taro. Tace Allah ya sa dai a dace. Ta miƙe domin yin sallar walha.

Ƙaton kicin na riska kuma na zamani ta window kuma na hango wani kicin ɗin na gargajiya inda wasu mata su uku suke ta aiki. Juma kuma tana ɓarar magi, na yi mata sannu ta ce "Amarya kin fito?" Nace e, tace "Muje in nuna miki an gama suyar kaji, wannan ma magin fefe ɗin da za'a yi ne na ke barewa." Nace Sannun da aiki, Mukaje na gani na yi musu sannu. Suka ce Me za a dafa?" Naja Juma gefe nace me ki ke ganin Hajiya tafi so a taro? Tace "E to tunda kin tambaye ni zan faɗa miki, muna yi shinkafa jalaf, tuwo, da alala, waina sinasir funkasau da sauran su, amma yanzu kin ga babu maganar waina ko sinasir, tuna da ba a tashi yin su ba yanzu ko ba gaskiya ba, sai dai a ƙara da wani abin." Nace in akwai kayan ɗanwake za mu iya yinsa, da kuma dambu da funkason ko kina ganin mutane ba za su so su ci waɗannan ba?
Tace "Yannan ki ke maganar ba za su so shi ba,ai yanzu babu abinda ke kwantai in dai abinci ne. Muna da ɓarjajiyar shi kafar dambu sai dai bata da yawa sosai, in kuma na kuskus za ayi to." Cikin sauri nace A'a za a yi shi haka ai ko ɗanwake ba mai yawa sosai za ayi ba, na tare maganar kuskus ne domin ban taɓa yin na kuskus ba.
Tace 'To ki faɗi gaba ɗaya abinda muke buƙata wanda babu sai a kaiwa Hajiya list za ta aike ni in siya." Na ɗan yi shiru, sai dabara ta faɗo min nace tuwo da kayan shinkafar ki lissafa ki fidda wanda babu, ni kuma sai in lissafa miki na dambu da ɗanwake. Nayi haka ne dan su nafi iyawa. Haka dai muka tada lissafin tuwo za ayi miyar ganye da agushi shinkafa soyayya sai alala da funkaso dambu da ɗanwake. Haka dai aiki ya rincaɓe mana danma suna da hanzarin kuma komai an ɗora wasu akan gas ga kuma murahu. Ina yi ina addu'a Allah ya fidda ni kunya ƙarfe ɗaya da rabi komai ya kammala sai tuwo da suke ɗauewa a leda Gida ko ina ya ɗauki kamshi. Gaskiya su Juma sun iya girki kuma sun taimaka min sosai. Suka ce inje tunda kwashe tuwo ne ya rage in sun gama sai su kai inda aka jere komai.

Hajiya tana salla a. Falon ya soma cika da Jama'a yaranta duk sun iso da 'yayansu, na rusuna na gaida kowa sannan na nufi gefe na. Maman Nana tana cewa yanzu Maman Iman ke cigiyar ki. Nace ina kicin ina take? Tace tana salla, na ce nima bari inyi sallar
Na shiga É—aki zan shiga wanka sai naga wayarta a kan gado, sai lokacin na tuna da wata waya, na É—auka dan in duba ko an kira ni.
Kiran Shamaki yafi goma ga saƙo na fara duba saƙunan, magiya ya ke in naga kiran shi don Allah in kira.
Cikin rawar hannu na danna kiran shi tana shiga ya ɗaga. Baby lafiya? Nace lafiya Lau, ina kicin muna aiki ne,ban tafi da wayar ba. Yace "Ko ina ki ke Baby ki zama da wayarki a hannu, na manta zaki yi mana girki, kinji yadda hankali na ya tashi ne kaɗan ya rage in taho gidan." Nace da ka kira Hajiya zata faɗa maka cewa ina kicin. Yace "Taɓ to ya za'ayi in iya kiran Hajiya in tambaye ta ke, akwai buƙatar ki lura da abubuwan da basu kamata ba. Ya ki ka san zata kalli abin?" Na yi shiru domin banga wata matsala game da hakan ba to kullum sai Hajiya ta yi abinda na sha mamaki. Yace "Tunda kina lafiya shike nan, dama dai inji muryar ki ne, yau na zama cikin yawan tuno ki da miki addu'a. Kin dasa wani abu a zuciyata iya jiya zuwa yau, dan Allah Baby kar ki canza ta min yaya. Kowa ya ganni a kasuwa sai ya yaba da kayan da ki ka zaɓa min kuma kin san abin mamaki na taɓa saka kayan amma banji wanda ya ce na yi kyau ba sai yau, har waɗanda ba su san na yi aure ba da sun ganni sai suce kamar ango." Cikin mamakin irin zuba zance da Yaya ke yi nace naji daɗi sosai da na saka a farin ciki, insha Allahu bazan taɓa canzawa ba, yin hakan fa dai-dai ya ke da juyawa aljanna baya. Yace me ki ke yi yanzu? Nace wanka zanyi inyi salla sai na shirya fita filin taron. Sai kawai naji subba ta ratsa kunne na ta cikin waya,ta bi sassan jikina wanda haka ya tilasta min sulalewa na zauna a kan gadon tare da kumshe ido. Na ɗago waya na kalla baya sautin ya katse layin .
Cikin sanyin jiki na shiga wanka. Bayan nayi salla yau ma dai kwalliya ce aka caɗa min na ci leshi ina ta ƙamshi su Jamila sunzo da su Umman Amina har da maƙotanmu da yawa abu mamaki,dangin Abba ma sunzo. Wani ƙaton fili ne a gidan an shirya shi kamar tantin larabawa. An zuba kujeru a gaban kujerun na alfarma Hajiya tare da wasu manyan Hajiyoyi ƙawayenta suna zaune a kai kusan su goma dukkan su kowa tana ji da kanta.
Sai layi na biyu 'yayansu ne. Sannan sauran mutane da abokan arziƙi a sauran kujerun wanda teburi ke tsakiya. Kamar yadda Maman Umar ta shigo ɗakina muna zaune, tace matar waliyina Umma su Zuhra ita ce ta riƙo ni har gaban su Hajiya. Haka aka yi, ina durƙusa na gaishe su, suka amsa cinkin isa da ƙasaita. Sannan Na duƙusa na gaida yayun mijina, aka kaini wata kujera da aka tanadar min. Wata malam ta tashi ta fara gabatar da nasiha game da zaman aure, biyayya ga miji, bin uwar miji, bin dangin miji tsafta iya girki da sauran su. Sai dai banji inda ta faɗi yadda ya kamata uwar miji ta mutunta matar ɗanta ba,dangin miji su girmama matar ɗan uwansu ba,haka banji ta yi magana game da hakkin mace akan miji ba,amma tayi magana sosai akan haƙƙin miji akan matarsa. A zuciya ta nace ko ina dai yanzu mutane suna kare abincin su ne suna yin abinda suka san shine fitar su.
Bayan an gama MC ta sanar cewa yanzu lokacin cin abinci ne wanda amarya ta dafa kuma zata fara gabatarwa a gaban Hajiya, amma kafin haka sai ta É—an É—ana dukkan abincin da ta dafa, sannan za a kai ga Hajiya da Aminanta. Yin hakan ba wai ana zargi ba ne al'adace.
Gabana ya faÉ—i na tashi na nufi gurin da aka jere kayan abincin kowa ya kallona, na zaci su Juma zasu zo su taimaka min amma sai na ga kawai kowa kallona yake yi. Na É—auki tire na jera plate huÉ—u suka cika shi na zuba shinkafa nasa tuwo a É—aya na saka dambu a É—aya sai kuma na sa Alala a É—aya, na kuma jera huÉ—u É—aya mai zurfi sa matsami na tsamo É—anwake na zuba a mai zurfin. Sai na zuba kaji da kifi da naman rago. Colsow kuwa shima madubi daban sai na zuma a karamin plate na sa cokali na É—iba na sa a baki ina ci, sai naji an kwashi tafi. Duk a ruÉ—e nake, na É—auki tiren na soma kaiwa ina jerewa a teburin gaban su Hajiya. Sai da na cika teburin komai na zuba musu, lemuka dai dama na ga anjere su da ruwa a kan kowane tebur.
Na koma na ci gaba da zubawa, anan ne Juma suka zo suna miƙawa teburin su Maman Umar zuwa na sauran jama'a. 'Yan unguwarmu da yake a ko ina sai an nuna halin, nan suka fara zuwa suna cewa Baby a bamu. Juma ce ta kore su, ta ce kowa ya koma mazaunin shi zai samu. Bayan an gama da manya sai Mc Ta sanar cewa Amarya ta koma nata mazaunin yanzu masu rabon za su zo su raba. Wata mata tare da 'yan mata suka shigo suka soma rabon abincin ni kam Idanuna da hankalina suna kan teburin su Hajiya har zuwa lokacin da mutane suka fara cin abinci ta irin su ba'a fara ba, sannan yanayin kallon da wasu aminan ta suke min ya sa jikina yin sanyi, a zuciya ta kuwa addu'a nake Allah ya fiddani.
Kusan kusan mutum uku suka fara cin abincin sannan lura d Hajiya i ta fara ci, sai dai wani abin ban iya gane ko ya ta ji abincin yadda take komai cikin ƙasaita.
Chapter 17 · 0% Book details