← Book details Hamshakiyar Uwa Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 34

Sashe 21

Hamshakiyar Uwa Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Zan tashi sai ga su Meema cikin shirin makaranta. Suka durƙusa har 'yar Anisa suka gaida Hajiya. Nace kun gama shirya wa. Suka kalle ni sai suka ce Hajiya ina Dady?.Tace "Yana ciki kuje da sauri ku gaida shi karfa ku jima ku dawo yanzu ku tafi."
Azima ta shigo itama cikin kayan makaranta ta gaida Hajiya sannan ta nufi ciki kenan zata gaida mijina. Na miƙe tare da faɗin to bari inje. Hajiya ta ce Allah ya yi albarka. Ina shiga falonsa na samu yaran suna ta wasa Azima ta ƙwanƙwasa ƙofar ɗakinsa. Na dube ta sai naji wani kishin ta ya kamani, nace Ke ɗan jira mana ta tsaya. Nace zauna bari ya fito. Tace "Za muyi latti." Yadda ta yi maganar ya nuna itama akwai alamun kishin. Nace bari ya fito yanzu.
Ya gama shiri tsaf cikin farar shadda, ya ce "Yau ba a zo an bani kaya ba." Nace naje gaida Hajiya ne. Ya janyo ni jikin sa, "Jiya kinyi bacci kin barni nasan gajiya ce." Nace na gaji sosai, kuma inna yi bacci aka tashe ni dama ciwon kai nake yi ,jiya Allah ya taimake ni kaina baiyi ciwo ba da ka tashe ni, ko da yake na koma baccin da wuri. Yace "To saboda me?" Nace ban sani ba, amma ƙila domin bana yin baccin rana ne. Yace "To kinci bashin na jiya yau za'a maida min. Na zaro ido bashin me? yace "Zan faɗa miki inna dawo," Nace yara fa na jiranka a falo. Da sauri ya fito yana faɗin "Za su lattti." Azima ta gaida shi ya amsa tare da tambayar ya yaga fuskarta haka ba walwala. Tace ba komai. Ya ɗauki yaran duk ya sunbace su ya musu addu'a suka rugo gurina "Momy ina kwana?" Na amsa na yi musu addu'a nima. Azima ta gaishe ni na amsa sannan suka fita. Ya kalle ni "Momy yara." Nace na am Dadyn yara. Muka koma ciki muna dariya. Ya zauna bakin gado yana min wani kallo, "Zan tafi kasuwa ina ƙishirwa." Na yi kamar ban gane ba sai nace, Bari a ɗebo maka ruwa mana. Ya ɗauki jakarshi na amsa. Yana faɗin "Ba wannan ba, nace To wanne? Ya lakuci kumatuna "Zaki sanshi inna dawo." Muka fito har ƙofar falon Hajiya na miƙa masa ya ƙi amsa ya shige falon Hajiya ya rusuna ya cire hula ta dafa kanshi tana yi masa addu'a. Ya miƙe na saci kallon Hajiya cikin ɗari ɗari na ce mishi ga jakar. Ita ma ni take kallo, yace "Kin fasa rakani motar ne?"
Na kalli Hajiya da sauri, ta ɗaga kai alamun inje,sai na bishi. A falon kusa da waje ya tsaya yace "Da bazaki rako ni ba tsoron me ki ke ji?" Nace inajin nauyin Hajiya ne. Yace Hajiya zataji daɗi taga kina kula da ni yana cikin abinda take dubawa a cikin jarabawarta." Na sunkuyar da kai. Dama kaima kasan Hajiya tana jarabawa? Ya sunkuya ya sunbaci leɓunana, yace "Ki koma daga nan bana son masu aiki su lalle ki, ki zama tare da wayarki zan kira ki."
Nace Allah ya tsare ya bada sa'a. Na dawo na durƙusa gaban Hajiya Nace za 'a yi miki wani abu ne? Jin shiru yasa na ɗago na dubeta, ita ma ni take kallo. Na buɗe baki zan yi magana ta ɗora yatsanta akan leɓenta da sauri alamun inyi shiru. Sannan cikin isa ta ce, "Haka ku ke magana kamar kuna yin magana da maƙota? Haka ki ke yi wa ɗana magana? da irin wannan sautin ku ke hira lokacin da ya ke zuwa zance? Na yi shiru ina kallon ta. Ta girgiza kai sannan ta ci gaba da faɗin akwai buƙatar ki sake sabon tsari game da irin wannan hayaniyar da ki ke tsammanin cewa magana ki ke yi." Na kaɗa kai alamun naji, domin ina tsoron kar inyi magana in sake yin sauti mai ƙaran da tace. Tace "Tashi ki je kuma ba ina nufin ki kama baki ki min gum in anyi magana ki kaɗa kai kamar ƙadangaruwa ba." Da leɓuna na amsa ban bari sun fitar da sauti ba. nace To.
Na zauna a bakin gadona na yi shiru ina tunani wajibi ne in koyi yadda suke magana domin in samawa kai na sauƙi, amma ta yaya? Wa zai koya min yadda suke magana? Amma kuwa anya ba nau'in wulaƙanci a lamarin Hajiya, shi so ɗaya ya min magana tun yana zuwa zance,kuma daga lokacin na rage sautin muryata in muna magana da shi. Sannan su Juma da yaran ai duk na yi magana da su amma banji wanda ya ce komai game da sauti na ba. Na tuna yadda Hajiya ta wani toshe kunne kamar na kunna mata lasifiƙa, kuma ita ma munsha yin magana da ita kafin yau. To ko yau ɗin na ɗaga murya ne? Na tambayi kai. Koma menene na sha alwashin yadda na shigo gidannan matsawar ba da mijina na samu matsala ba,zan jure komai da komai in samu zama hamshaƙiya kamar yadda ta faɗa.
Na yi gyaran murya na soma gwada yadda zan yi magana a gidan da kowa a gidan.

Shamaki a kasuwa duk wani kaikawo da wata ganawa da manyan kwastomomin su da ya ke yi sai amaryarsa tana zuciyar sa Allah Allah Allah yake ya ɗan samu dama ya kira ta ya ji muryarta kuma ya tabbatar ta na cikin ƙoshin lafiya.

Ina tsaka da gwaji .kiransa ya shigo, a zuciya ta nace Yawwa bari in gwada da shi, na ɗaga na amsa da muryata can ƙasa. Da sauri naji ya ce, "Baby me ya faru? Ba lafiya ne?" Nace a a mekaji? Yace "Muryar ki wata iri." Nace ina koyon yadda zan ke yin magana da ku ne?
🖊️🖊️🖊
️Ya ce "Kamar yaya kenan? Nace ashe ina ta magana da ƙarfi maimakon ka faɗa min sai ka ci gaba da sauraron a haka sai da Hajiya ta nusar da ni a yau, don Allah ka yi haƙuri, kuma daga yau na saukar da muryata ni ma. Nayi ya yi shiru, can ya ce. "Karki takura kanki zuwa yanzu ni na saba da maganar ki." Ya canza maganar da faɗin "Fatan ki na cikin ƙoshin lafiya."
Nace lafiya lau ya kasuwa? Allah ya taimaka. Yace "Ameen.

To yauma rana ta uku haka na fuska sai ƙarfe shabiyu ya shigo, ni kuma na yi kwanciya ta na kulle ɗaki, banji bugun sa ba sam. Ban farka ba sai kiran sallar asuba, da na farka na ganni a ɗakina take naji fargaba, ko yaya wannan bawan Allahn zai ɗauki bin oho. Cikin sauri na ɗakko wayata na duba bai kira ni ba, na shiga banɗaki na yi alwala na fito naji ana ƙwanƙwasa min ƙofa. Da sauri naje na buɗe, shine a tsaye zashi massalaci yace " Ashe kin tashi ma toshi kenan na tafi masallaci." Babu wata alama ta damuwa data nuna a fuskar sa. Nace to, dama ka yi ta kirana ne baccin ne mai nauyi banji ba. Ya yi murmushi "Kada ki damu, ban kira wayarki ba ma,saboda zata tashe ki bacci kuma kinga kanki zai yi ciwo yanzu kije ki yi salla nima kada in makara.
Na idar da salla na zauna kan sallaya ina tunanin ta ina zan ɓullowa wannan al'amari. Yanzu ma nasan sai zai tafi kasuwa zai shigo ya shirya.
Na ɗakko ƙur'ani na zauna ina ta karatu har ƙarfe bakwai, na tashi da sake wani salon dabarar na shiga na fesa wanka na gyara fuska ta na zuba kwalliya na saka Atamfa doguwar riga na ɗaura ɗankwani bayan na saki gashina a kafaɗa. Na fesa turaruka mayafi na yafa kamar mai zuwa unguwa na nufi gaida Hajiya. Suna zaune kamar kullum suna zantuka ƙasa-ƙasa.
Nayi sallama can ƙasan maƙogwaro suka amsa na durƙusa na gaida Hajiya ta amsa fuska a sake, sannan na juya na gaida shi ya amsa yana ta kallona, na ɗan zauna jim,sai na dubi Hajiya zan iya zuwa in taya su Juma aiki? Duk suka Kalle ni, ya kalli Hajiya da sauri. Tace "Menene dalilin ki na so shiga kuxin?" Na ƙasa ƙasa da murya, dama dai ina son in koyi wasu abubuwanne waɗanda ban taɓa ya ba. Tace "To sai ki rubuto min abinda baki iya ɗinba kinga sai in sa a koya miki."
Na koma gefe na zauna ina kallon su,sai satar kallona ya ke yi da mun haÉ—a ido sai ya faki idon Hajiya ja É—aga min gira. Can Hajiya tace. "Kinga tashi jeki iciki kin raba mana hankali muna magana. Na yi mata sallama cikin ladabi sannan na tafi.
Ina ta kai kawo a cikin ɗaki ina neman shawarar da zan yanke. Hajiya bazata yarda in zauna kusa da su ba kuma bazata bari in raɓi su Juma ba,ga mijina munyi nesa dole dai in samawa kaina farin ciki na nufi gefen sa ma jiya Rahin da yara ana shirin makaranta,na zarce gurinsu. Ta taga na ke kallon yadda suke shirin, sai na shiga na ƙara gyara musu. Mubina tace "Momy saboda ke momy ce shine ki ke saka mana kayanmu?" Nace e mana ai ita Momy ta son taga yaranta sunyi kyau sosai sun fi kowane yara. Meema tace Zainab ƙawata tace su Momynsu ta ke yi musu Homework mu kuma sai dai Anty lesson take mana. Nace wacece kuma Anty Lesson Rahin ta ce wadda ke zuwa gida tana ƙara musu karatu. Nace au, to ina kuma Azima ta ke? Rahin ta nuna min ɗayan dakin da hannu ta ce ita ga ɗakinta can.
Na tashi na nufi ɗakin tana zaune bakin gadon ta tana saka safa, ɗakine sosai irin na mace da komai a ciki. Ta bini da kallo nima dai ita nike kallo zancan gaskiya kuma yarinyar tana da kyau sosai. Nace Azima baki zo ɗakina ba Ni gashi na zo naki, ko bakya son mu saba ne? Taɗan taɓa baki. "Ni bana da ra'ayin sabawa da kowa sai Hajiya kawai." Nace haka ne. Ni kuma nafi sabawa da Shamaki. Ta kalleni da sauri sai kuma ta sunkuyar da kai ta ci gaba da abinda take yi. Nace bari in tafi,in kin dawo zaki zo ɗakina? Tagirgiza kai tare da furta 'a'a.
Chapter 21 · 0% Book details