← Book details Hamshakiyar Uwa Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 34

Sashe 24

Hamshakiyar Uwa Part 2 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Naji daɗin ganin Umma ta sami sauƙi kuma ko da Hajiya ta hanani zuwa ashe tana aika musu da abinci, sannan bata hana mijina zuwa ba ya duba Umma ba.

Kwanan Umma uku a asibiti aka sallameta amma Hajiya bata barni na je ba, koda yake ban tambaya bane ina jin tsoro, da nace zanje sai ya ce in tambayi Hajiya. Ni kuma sai in yi shiru bana sake maganar , kuma ko a fuska bana nuna wata damuwa. Amma kira inna kira su sai munyi waya da kowa a gidan har su Jafar. Na dangana na zubawa sarautar Allah ido. Ranar da zata cika sati ɗaya da 'yar tana raye sai a ce ranar suna, 'yan Kurna za su zo da ƙawayen ta za'ayi ɗan taro. Jamila ce ta tsegunta min gaskiya ina son zuwa dan haka tun yau na rubuta mashi saƙo cewa ina son gobe zanje gida in duba Umma saboda za 'a yi ɗan taro.
Shina amsa ya aiko min da ita kamar kaka..." Ki je ki sanar da Hajiya." Na yi shiru cikin tagumi Hajiya ke aure na da komai zai ce in tambayi Hajiya. To shi mai zai hana ya tambayar min. Na danna kiranshi. Ya yanke ya kira ni. Na É—aga. Nace ya kasuwa? Yace "Alhamdulillah" Nace dama zance ne ko zaka tambaya min Hajiya É—in wallahi ni sai inke jin tsoro kar ta ga kamar na matsa mata.

Yace "Baby haka dokar gidan ta ke, ke zaki tambaya da kanki in taga ya dace shikenan zata barki, har yau baki fahimci Hajiya bane shiyasa ki ke jin tsoronta. Ki tashi yanzu kije ki same ta ki faÉ—a mata uzrin ki, in ta yarda shike nan." Nace To bari in gwada, mu kayi sallama.
Lokacin ƙarfe uku zata yi domin an yi azahar. Na sameta tana karatun wani ƙaramin littafin. Na durƙusa na gaisheta sannan na ce Hajiya dama ina son in tambaya ne ina son inje gida in duna Umma da jikin ta, goben ta ke kwana bakwai.
Ta ɗago kai ta ce za tayi taro kenan? Nace 'yan uwanta ne zasu taru. Ta yi shiru na ɗan lokaci sannan tace "Mijin ki zaki tambaya Ni menene nawa?" Nace ai na tambaye shi yace min duk abinda ki ka ce shi za'ayi. Ta sauke ajiyar zuciya "Kira min Juma." Da sauri na miƙe domin kiran Juma. Tare muka shigo, tace "Juma dubi yarinyar nan sosai ki gani ta canza daga yadda ta zo gidan nan Ni kullum juya iyau na ke ganinta?" Juma tace ta canza gaskiya ta murje ta yi haske Hajiya ai dole a canza kinsan hutu daban ya ke. Hajiya ta dube ni. "Jeki Allah ya kaimu goben zan duba in gani inzaki samu zuwa.
Na ce to, ko fuska ban canza ba har naje ɗaki. To ranar ma dai Shamaki bai dawo ba, daga can wai ya tafi Lagos sai text ɗinsa na gani, wai tafiyar gaggawa ce .Lamarin ya fara sani tunanin ko dai ba wani so da mutumin nan yake yi min. Bana samu wata kulawa da na ke buƙata in nayi la'akari da yadda na ke karantawa a littafai, ko 'yan unguwar mu da na kan ga sun fita da mazajen su irin da da dare haka suna ɗan zaga gari suna shan iska. Ni gani a kulle ba aikin fari ko na baƙi, bani da ko sisi sai dai inyi kallo in ci insha, ko hira mu yi da mijina ta gagara har yau bansan abinda ya fi so ba, shima bai san abin da na fi so ba ko wanda bana so ba .

Da safe bayan na gama komai naje na sake rusunawa gaban Hajiya nace dama na zo ne inji ko in shirya? Ta dube ni, "Kin faɗawa mijinki? ". Nace tun jiya yace in kin amince sai inje. Ta ce to yau kun gaisa da shi?" Nace 'A 'a, da sauri tace "To saboda me mijinki baya gari amma baki kira shi ba?" Na daburce nace na kira bai ɗaga bane shine na aika mishi saƙo. Tace "Karantamin saƙon inji." A zuciya ta nace iko sai Allah. Na ɗauki wayar na fara karantawa.
Fatan ka tashi lafiya,na kira ka baka É—aga ba,nasan kana cikin uzri dama dai zan gaishe ka ne, fatan zaka dawo lafiya Allah ya bada abinda aka je nema.

Ta dube ni tace "Ameen" Kin kyauta sosai ki yi ta yi wa mijinki addu'a, sai dai ba irin ɗan sunan nan na ku na zamani yadda zai ɗanji sanyi da irin "yan kalamai haka masu daɗi? Na sunkuyar da kai. Hajiya dai son kanta ya kai inda ya kai.Na faɗa a zuciya, a fili kuma nace, zan gyara insha Allahu. Tace "Yawwa ai gara a gyara ɗin. Kije ki shirya sai direba ya kai ki, ƙarfe nawa zaki dawo?" Cike da murna nace duk lokacin da kika ce . Tace ki zama cikin shiri daga ƙarfe biyu zai koma ya ɗakko ki.

Ina fita falon na sheƙa da gudu ɗakina harda rawa ina ɗiban shoki tsabar murna. Na shirya tsaf cikin shigar Atamfa. Gaskiya na ɗan ciko komai nawa ya ɗan ƙaru.
Na fito falon Hajiya na zauna a gefe. Ta dube ni. "Antyn zumuɗi har a shirya kenan, to inga jakar me zaki kaiwa Ummar ta ƙi?" Nace miƙa mata tare da faɗin ba komai zandai je in ganta. Ga mamakina sai naga ta caje kakar sai 'yar hoda ta ce sai tissue. Ta miƙo min jakata. Sannan ta ce Haka" zaki gidan hannu rabbana?" Nace to ai Hajiya Ni bani da abinda zan ba su. Tace Ai abin kunya ne kina auren mai kuɗi kamar Shamaki amma kije gida hannu na dukan cinya haka, ba daɗi ai kyanshi ace kinje jakar nan cike da kuɗi duk wanda ya halarci taron sai ki bashi wani abu."
Take zuciyata ta faÉ—a min cewa Hajiya tana da wata manufa a maganar ta. Nace to ni kuwa Hajiya ina zan samu kuÉ—i har in yi hakan? Tace "Ga Mijin ki da kin kira shi sai ya tura miki ta account ku biya da direba ki cire."
Na sunkuyar da kai ina ta nazarin maganar Hajiya duk da cewa sak ta yi maganar kamar daga ranta, amma sai najii a jikina cewa Hajiya tana sane ba domin Allah ta yi wannan maganar ba.

Ta katse min tunani da cewa "Ki kira shi mana." Nace Hajiya ni ko account ɗin ma bani da shi,,kuma banda haka ma yaya za 'ayi yana irin wannan wahalar ko isasshen lokacin kansa baya da shi amma sai inkirashi ya bani kuɗi ba tausayi kenan, inda ace haka ake yi Hajiya da ba'a kawo haka ba. Mu gode da irin ɗawainiya ta kai abinci Allah ya saka a mizani, suma suna ta godiya su Umma da Abban. Ta zura min ido,can tace shike nan ki shiga ɗaki na zakiga wata leda a saman gado na ki ɗakko min." Nace to, na miƙe ita kuma ta ɗauki waya tana kiran layin direba.

Yau ne ranar farko da na fara shiga ɗakin baccin Hajiya, wani mugun ƙamshi ya bugi hancina. Sai dai ban tsaya kallo komai ba, domin ina tsoron ko akwai kyamara.. Amma fa ɗaki ne na alfarma. Na durƙusa na miƙa mata nace gashi.
Chapter 24 · 0% Book details