← Book details Hamshakiyar Uwa Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 34

Sashe 18

Hamshakiyar Uwa Part 2 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Masu hotuna da bidiyo ana ta ɗauka gaskiya ni tsarin ya yi min, wata zuciyar tace tunda kin tsallake Hajiya ta ci kyace abin ya birge ki mana. Haka dai aka ci aka sha sannan aka gama. Aka kai wa Hajiya abin magana zata yi jawabin godiya amma kafin haka sai ƙawarta Hajiya Zulaiha ta amsa ta isar da saƙon Hajiya game da abincin da amarya ta ciyar da su, tace "Zan yi ɗan bayani kaɗan kafin Hajiya ta yi godiya, gaskiya amarya girki ba laifi amma a ƙara gyara hannu sosai, ta ɗan taɓa baki, ya yi daɗi sai dai ɗan gyara guda biyu dazan miki, na farko ɗanwake mai da yaji ne sai kika bamu da miya. Na biyu kin mana ɗan zubi a dambu sai ki ƙara sakin hannu kaɗan saboda rowa bata da wani amfani kuma bata cikin sunnar gidan nan. Na sunkuyar da kai, ina mamaki amma duk da haka ni ce da godiya tunda ƙorafin ya tsaya a haka,,Hajiya ta ci abinci Allah ya soni ni.
Hajiya ta amshi abin magana tayi godiya ga kowa tare da fatan duk za su koma gidajen su lafiya.Sannan ta sa albarka tare min fatan zama jarumtar mace musamman gurin yi wa miji biyayya. Aka abin maganar wai ince wani abu bani wai nima in yi godiya. Gabana yana faɗuwa na amsa. Nace Mun gode Allah ya maida kowa gida lafiya, kuma insha Allahu zan yi amfani duk shawarwarin da aka bani zan kiyaye. Haka taro ya tashi kowa na san Barka. Ana tashi aka kira la'asar. Hajiya ta kirani inyi sallama da baƙinta. A lokaci ne wannan mai cewa ina da rowar same ta tana cewa "Hajiya Zeena duk matan da ke Kano amma Shamaki ya rasa wadda zai ɗauka sai wannan cokokuwar ko cikin 'ya 'yanmu ya kasa zuwa ya duba. Na kalli Hajiya lokacin da takecewa
"Bar ɗan yau da abinda ya ke so Hajiya Zaliha. Wani mugun so ya ke yiwa yarinyar nan ba domin na samu tabbacin ba asiri suka yi masa ba da a haka zan kalli abin. Gaggawa fa ya yi aka je aka nemo masa auren ta. Ni kuma kinsan matsala ta, ina son ɗana da yawa kuma ya rayu akan samun duk abinda ya ke so, in ba ɗana abinda ya ke so matsawar yin hakan ba saɓon Allah bane." Nace su sauka gida lafiya na juya raina ba daɗi, na soma jin takaicin kushe min halitta da ake yi. Gefena tanƙam da 'yan uwa da 'yan unguwa sai kallo na suke suna min murna. Na zauna bakin gado Jamila ta zo ta ce "Abinci ya yi daɗi Yaya Baby kuma ke ki ka dafa?" Na ce e mana. Wayata ta soma ringin ta miƙo min. Na amsa Mijina ne Hajiya ta hana ni faɗa masa Yaya To bansan wane suna zan saka masa ba. Na ɗaga, yace " Yaya Baby gaske ne ke kika dafa abincin nan?" Cikin shagwaɓa na ce wai don Allah nice Yaya? Yace "Ina son yadda su Jamila suke faɗa ne." Abicin bai yi daɗi bane ko? Na tambaye shi. Yace "Inji wa, ai in faɗa miki abincin Hajiya ne kaɗai ya fi naki daɗi." Na yi murmushi a zuciya ta nace ai ita Hajiya komai nata ya fi na kowa. "Sannu soyayyata ,kin yi ƙoƙari sosai.
.....
Da na dawo zan shige zan shige gurina sai naji kukan yara, sai na samu kaina da nufar gurin su. Rahin ta yi musu wanka tana ta fama da su zata sa musu kaya amma Mubina bata son kayan da aka ciro musu, ita leshi za a sa mata, Anisa kuma ba wannan takalmin take wa kuka ba, sai an canza. Meema tana kicin kicin saka nata kayan. na shiga nace me ya same su? Cikin girmamawa Rahin ta ce Rigima suke jin yi Anty kinga ga kaya wai kowccen su bata so." Na ce to ki barsu kowa ta ɗauki wanda ta ke so mana ina ganin ai kamar ba matsala ko? Rahin ta ja baya tace "To ku zaɓa amma don Allah kar ku zubo kayan domin shirya su ba ƙaramin aiki bane durowa uku, aiki ne." Nace kije kusa sai su nuna miki sai ki ciro wa kowaccen su yadda ba zai ɓaci ba ko? Ta ce "To " Yara suka bini da kallo sannan suka kasa nuna wanda suke so. Nace In zaɓo muku? A tare suka ɗaga kai.
Na dubi Rahin anko ake yi musu kullum?. Tace "Wani lokacin suna sa daban daban." Nace Hajiya tafi son su sa kaya iri ɗaya? Tace "Ban taɓa jin Hajiya ta yi magana akan haka ba ."
Na kama hannun su suka nuna min duk abinda suke so, nace to muje É—akina sai in shirya ku a can. Da sauri suka yarda suka bini Rahin ta bini da kallo. nace ki gyara musu kayan kawai.

A Kan gadona nace su hau Meema tace "Hajiya ta hanamu tace gadonmu kawai zamu hau amma banda na manya." A raina nace tofa! Sai nace ai Hajiya bata nan kuma ni bazan faɗa mata ba. Sai suka kalli juna, Mubina ta zau a kan kafe ɗin gaban gado, Meema ta ce "Hajiya ta faɗa mana in bata nan Allahnta yana nan, kuma zai ganar da ita inhar muka yi ba daidai ba. Na sauka kan Kafet ɗin batare da na sake magana ba, nace bari a fara shirya Anisa ita ce 'yar ƙarama ko? Meema ta ɗaga kai, sannan tace "Anty ke ɗin wacce ke ma nan gidan ki ke?" Nace ni Mominku ce, ba sunana Anty ba. Mubina da Anisa duk suka kalle ni , Mubina tace "Kema a nan gidan ki ke?" Nace e mana ga ɗakina ma. "Kece Momin da Dady yace zaki zo in anyi biki?" Inji Meema. Nace la! ashe ya faɗa muku, to ni ce. Anisa tace "To Momy anyi bikine?" Nace anyi jiya yau ma za ayi. Suka fara murna." Na gama shirya su muna ta 'yar hira suna min tambayoyi na shirme ita biye musu domin ni ina son hira da yara don haka naji sun shiga raina domin na lura suna da wayo. Na gama musu fesa musu turare, Meema ta kalli wayata "Momi in ɗauki wayar ki?" Nace me zaki yi da ita? Mubina ta amshe da cewa "Akwai game a ciki?" Nace babu amma ku zo in ɗauke ku hoto mukayi hotuna ni da su. Nace to sai ina? Suka ce za suje gaida Hajiya ne. Nace to ai ni baku gaishe ni ba, suka ce Hajiya ake fara gaishewa sai Dadi shikenan sai mu gaisheki. Nace to haka ya yi daga nan su gaishe min da Hajiya. Suka tafi ina bin su da kallo.

Goma saura na saka hijabi na fita, na nufi gurin Hajiya na tsugunna na yi mata sannu da hutawa ta amsa, nace nazo gurin yin aiki. Ta nuna min ƙofa da hannu bi nan zaki samu su Juma a kicin.
Hajiya ta bi Baby da kallo cikin wani kallo na nazari, kamar kowace amarya dai haka take zuwa a nuna mata kuxin ƙarshe dai abinci ya ƙi ciyuwa, ta taɓa baki bari dai mugani, domin ta lura yadda abubuwa ke faruwa a safiyar yau ana samun ɗan banbanci da wanda suka faru a matan da Shamaki ya aura, a safiyar farko misali in ya bar gurinta ya nufi ɗakinsa don ya shirya ya tafi kasuwa ya kan ɗauki lokaci bai fito ba, haka ma dai a wannan karon, ya ɓata fiye da awa ɗaya sai dai banbancin da ta lura da shi shine fitowar wannan karon akwai banbanci da na sauran, a yanayin sa a fili yana cike da nishaɗi da kamanin angwaye, sannan kayan da ya saka ta tabbatar ba zaɓin shi bane domin tasan a guri ɗaya yake saka babbar riga shine in zashi wani taro. Tace Allah ya sa dai a dace. Ta miƙe domin yin sallar walha.
Chapter 18 · 0% Book details