Sashe 12
Hamshakiyar Uwa Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Ya murza hula saƙar Gabas wadda ta tafi da kayan. Yadda kowa ke kallon sa haka nima nake ƙare masa kallo, fara'a fuskarsa ita ta bayyana tsantsan farin cikin da yake ciki.Haƙorin Makkansa yana haskawa, ina son haƙorin sosai ya ƙara masa kyau.
Suka tsugunna suka gaida su Umma abokan wasanmu sai tsokanar sa suke yi. Jamila ta kamo hannuna tana faɗin "Kifito kin laɓe kuma kina leƙensa." Na fito ya bini da kallo. Abokan suka ce mai hoto ya matso. Haka dai aka yi ta ɗaukar hotuna Ango fara'a ta kasa yankewa. Murya ƙasa ƙasa yace "Baby ina son mu yi magana ga shi ko ina mutane." Nace to ya za ayi? Ko zamuje gidan Usman Amina tunda duk suna nan? Yace " Ina ne?" Nace inda ka same mu jiya. Ya ce "To." Har abokan muka taka da Jamila soron gidan muka shiga muka bar abokan da Jamila a waje tana yi musu tayin abinci suka ce walima zasu tafi yanzu. Muna shiga Yaya caraf ya kama hannuwana cikin ɗoki, duka biyun yana musu wani irrin kallo, tsigar jikina ta tashi yarr, zan kwace sai yace "Kiyi haƙuri Baby an ɗaura mana aure, tun a ,jiya ina son in shafa wannan fulawar amma bani da damar aikata haka, saboda nasan shara'a bata bani dama ba." Na jure yana shafawa da lallausan hannunsa sai kurum naji ya sunbaci bayan hannuna, ya kafe ni da ido, duk tsoro ya bayyana a fuskata cikin rawar murya nace, Yaya kar fa wani ya ganmu. Ya girgiza kai, muryar shi a sarƙe ya ce in ɗan rungume ki Babu?" Na kwace hannuwana da sauri, sannan nace suna jiran ka a waje fa. Ya matso naja baya da sauri nace Jamila. Ta shigo tana faɗin "Menene?" Ta kalleshi har lokacin ni yake kallo, batare da ya lalle ta ba ya yi mata alama da hannu wai taje. Ta yi yar dariya ta fita. Ya matso ina ja baya har naje bango daf dani ya tsaya ya saki ɗan murmushi. "In Jamila ta iya cetonki yanzu anjima ko gobe wa zaki kira?" Gabana ya yi mummunar faɗuwa, na ganni wata 'yar tsuntsuwa a gabanshi. Muryata na rawa nace ina son inje in sha ruwa ne Ya yi murmushi. Yasa yatsa ya lakuci janbakin leɓena, ya lasa akan harshen sa. Sannan ya kauce gefe tare da faɗin "To soyayyata, kunga ga hanya nan nasan dai yanzu sai. in an rako ni, ko da yake zamu yi waya aiko?" Da sauri na nufi ƙofa ina cewa e zamuyi waya. Sai na ji ya saki dariya tare da faɗin "Matsoraciya." Mukayi sallama da su suka tafi ina ta bin Yaya da kallo, ashe dai shima ɗin ba kyalle bane. Sannan ya ƙara jefa ni cikin tunani.
🖊ï¸ðŸ–Šï¸ðŸ–Š
ï¸Maganganun shi sun jefa ni a fargaba, na shiga É—imuwa sosai, harma na kasa cin komai, kuka na yini yi, mutane suna zaton kukan barin gida ne, duk da cewa akwai hakan amma dai fargaban karon battar da zamu yi da Yaya ya fi komai É—aga min hankali.
Da taimakon su Jamila na yi ta canjin kayana. 'Yan kafin kayan ɗaki sun dawo duk sun ruɗe suna bada labarin gidana Gidan Hajiya Zeena ne. Sun gigice da ciye ciye da aka basu, wasu kuma suna murna sunga Hajiya Zeena. Nace to kenan dai Yaya ƙara rufe ni ya yi.
Jamila ta ce na faÉ—a miki, to ke menene na ki na É—aga hankali mai maimakon murana Allah ya baki sai ki yi masa godiya. Shiru na yi domin bazata fahimce ni ba.
Da yamma motocin ɗaukar amarya suka iso motoci na gani a faɗa. Na ƙanƙame Umma ina kuka sai lokacin naji duk auren ya fita kaina. Tace "Meye hakan kuma, ki tafi Allah ya bada sa'a ya albarkaci zaman ku ina fata zaki ɗauki dukan shawarwarin da muka baki. Haka Umman su Zuhra ta ɓanɓare ni ina kallon Umma tana hawaye muka Fita gidan su Abban su Zuhra shida Annan mu suka min nasiha suna ta maimaita min in yi haƙuri, in zama mai yawan haƙuri har sai da na fara tunanin kalmar nan da ake ta nanata min akwai dalili. Muka fita nabi layinmu da kallo ta zuciyata ta sake karyewa sai naji tamkar na tafi kenan.
Ta ciki mayafi ina ganin harabar gidan na gane, kai tsaye suka shiga da ni falon Hajiya cike da mutane tana hakimce a kujerarta kamar yadda na zata, tana ta yi mana sannu da zuwa.
Aka kaini gabanta aka zaunar, aka ce ga 'yar ki Hajiya mun kawo miki. Tace "To Allah ya yi musu albarka ya sa mun ƙulla alkwairi ina fatan kun faɗa mata yadda zata zauna da mijinta lafiya. Yanzu ku kaita ɗakinta, nawa shi'anin sai gobe inda ita amarya zata girka mana abinci tare da taimakon masu aiki ta bamu ni da mutane na, ina fatan zaku zo domin ku ci girkin 'yar tawa. Sai kallon kallo ake yi. Umman Amina tace insha Allahu. Ta ce Maman Umar ta jagorance mu zuwa ɗakina.
Aljannar duniya, haka kowa ke faɗi, ni dai ina lulluɓe a zaune bakin gado ina jin yadda suke labarin kayan kyale kyale da na kallo kyan ɗakin ɗaki sun tafi da mutanen don haka sai waɗan da suka yi kafin abin ya zame masu sabo. Haka dai ina zaune bakin gado kai na a rufe kowa sai bani shawara yake yi ki kwantar da hankalin ki ki yi biyayya ki ci arziƙi iyayenki su ci. Da haka duk aka watse, nace don Allah a barnin su Jamila sa dawo zuwa dare. Aka bar su bayan kowa ya watse sai na cire mayafi daga fuskata na fito falo ina ƙarewa ɗakin kallo. Na ruɗe wai ni Rabi 'yar magini ni ce da wannan dakin. Kenan zanyi murna da ƙaryar yar da Aliyu ya min? Na tambayi kai na. Abinda ya ƙara ɗaukar hankalina shin me ya kawo hoton babban baƙonmu na gurin sauka inda yake bani allona? Naje na zurawa hoton ido, a take na gane komai, wannan babban baƙon wato dai Yaya ne, duk cikin raina min hankalin da ya yi ne.
Jamila ta zo gurin ta
tsaya a gaban hoton ta sa hannu ta dafa ni, tace "Wannan shigar tamkar babban baƙon gurin saukar ku." Nace shine, tace "Ashe babban baƙon ɗan uwan su ne?" Nace shi kanshi ne a hoton nan kenan kinga shine babban baƙon. Jamila ta yi dariyar mamaki ta lakuci kumatuna tare da faɗin "Lalle shi wannan ɗan wasan kwaikwayo ne, to bin ya birge sosai." Ta zaro ido, kamar ta tuna wani abu. "Kenan shine ya sai kayan ɗakin nan?" Na sa mata hannu a baki na toshe domin bana son su Zuhra su ji. A hankali nace tabbas shine. Muka zubawa juna ido nace ina tunanin yadda zan yi masa zancan.
Jamila tace. "Kawai ki shere azuwan baki gane ba." Nace barshi yadda ya yi wasa da hankalina haka zan yi da nashi, sai ya faÉ—a min da kansa cewa shine. Jamila tace "Duk ba wannan ba, ya zakiyi da girkin gobe?"
....
Nace ko a jikina ban wani damu sosai ba, nafi damuwa da yaudarar da Yaya yamin, ni gaskiya a tsarina bana son in auri mai kuɗi saboda gudun wulaƙanci, na yi ƙasa da murya me mata uku suka yi masa duk ya raba su da 'yayansu ya kore su? Bakya tunanin yadda zan zama bazawara? Bakya tuna yadda masu min dariyar nuna min farin cikin na dace zasu koma yi min dariya tare da Allah ya ƙara?Dan haka wannan yafi zancan yin girki a gobe. Abinna na iya shi zanyi, kuma sun san daga ina aka ɗakko ni.
Jamila tace "Allah ya dafa miki, kuma zan zo goben in taya ki." Nace kefa nan zaki kwana kuma ba zaki shiga kicin ba. Ta zaro ido. "Rabani da faÉ—an su Umma, na dai dawo goben kamar yadda suka ce za a iya zuwa amma gaskiya bazan kwana ba. Na yi alamun kuka, tace "Garama kar ki sa a ranki.
Haka dai Su Fati da sauran 'yan layinmu suka buÉ—e kofar suka shigo da sallama duk zatona sun tafi. Jamila tace "Na zata kun wuce?" Sai sukace sai an rako ango tukunna.
Bayan sallar Isha aka kawo abinci tuwon shinkafa da miyar alayyaho ta É—au kifi da nama, sai jalaf É—in shinkafa ta ji naman kaji ga lemuka masu sanyi. Nan suka hau ci. Ni kam duk da ina jin yunwa amma zan iya cin komai ba, saboda far gaba sai dai ruwa na É—auka na sha.
Bayan sun gama Jamila ta ce su Amina su kai kayan ita kuma za ta gyara gurin, sai tsiya suke min wai ba su ga laifina ba in banci ba anjima da kazata ta amarci anjima kar in cika ciki yanzu. Ni dai ban kula su ba, sai fargaba da suka daÉ—a jefani ciki.