Sashe 15
Hamshakiyar Uwa Part 2 Complete Hausa Novel · about 5 min read
Banɗakin ya birge ni, na zuba wa fuskata ido a ƙasan zuciya ta kuwa farga ne."
Bayan mun idar yace "To Bismillah ki zo ki kwanta dan nasan kin gaji zan ɗan matsa miki jikinki sai ki samu bacci ko? Gana ya faɗi. Amma sai kalaman Hajiya suka dawo kunne na, ki zama mai juriya kuma ki bashi haɗin kai hakan zai sa komai ya zo miki da sauƙi." Na miƙe na je gabansa ya kama ni ya zaunar a cinyar sa.
Da ace zan iya bada labarin abinda ya faru a lokacin da duk wata mace budurwa zata so ƙwarai ta kame mutuncin ta da kimarta har sai ta riski irin wannan ranar.
Cikin bacci naji ana shafa gashin kaina, na buÉ—e ido a hankali muna haÉ—a ido, na maida su da sauri na lumshe, komai ke zuwa min tar abinda ya faru, gaskiya namiji mace ce raunisa, domin na tuna yadda mutumin nan ya yi a jiya. Sai Muryar sa a cikin kunne na, ki tashi ni na tafi masallaci. A hankali nace to sai ka dawo. Sai da naji fitarsa sannan na tashi a gajiye na shiga banÉ—aki. Har na idar da salla abubuwan da suka wakana tsakaninmu kawai nake gani.
Na ɗaga bargo zan kwanta sai naga wasu guraren da suka ɗan ɓaci sai dai a canza. Na yi ɗan murmushi, sannan na sauke ajiyar zuciya, tun jiya nake cike da alfahari.
Naji shi shiru sai na fita zuwa ɗakina, na watsa wanka na saka doguwar riga baƙa na yafa mayafinta, sannan na nufi gaida Hajiya. Ban ganta a kan kujerar ta ba,sai naji magana ƙasa ƙasa a gefe, ina kallon gurin sai naga ashe sune tana kan sallaya yana gefe ya sunkuyar da kai, kamar mai ɗaukar darasu. Nima naje nayi irin sunkuyon sa a gefenta na fara gaida ita ta amsa tare da faɗin "Ya baƙunta?" Nace Alhamdulillahi. Na ɗan shafi kallon inda ya ke, shima ni yake kallo. Nace Yaya ina kwana.Ya amsa tare da tambayar baƙunta. Hajiya tace tun a waccan ranar na faɗa miki cewa ki daina kiran sa da Yaya, kin san dalili? Na girgiza kai. Tace "Ba ku da wata alaƙa mai kama da hakan ta jini ko ta danga rere, don haka ki ce masa Aliyu, ko ki faɗa masa Shamaki, ko kuma ki faɗa masa suna irin naku na 'yan zamani, amma bana son inji Yaya ɗinnan." Nace to insha Allahu na dai na, dama sunan nasa ne bazan iya faɗa ba. "Jiya kin faɗa duka biyu." Na dube shi da sauri, muka haɗa ido na sunkuyar da kai, sannan na miƙe Hajiya zanje ciki. Tace "To Allah ya shi albarka, kamar ƙarfe goma sai ki fito ku yi mana abincin jama 'a ta." Nace To.
....
Na koma na rusuna kusa da Hajiya nace a ƙalla kamar abincin mutum nawa za ayi? Ta zuba min ido. "Me yasa ki ka tambaya?" Gabana ya faɗin Allah dai ya sa yin hakan ba laifi bane. Nace dama dai na tambaya ne domin kar a yi shi ya yi kaɗan ko kuma ya yi yawan da zai zama kamar almunbazaranci, ta kaɗa kai alamun ta gamsu, "Kamar na mutum hamsin za a yi zuwa Saba'in. " Nace To. Ɗaki na koma dan in jira shi ya zo mu karya.
Juma ta shigo da babban tire, jere da flas na shayi da na abinci, ga samiru. Na yi mata sannu ta amsa, tace "Ki karya kummalon ki amarya ki maida hankali ga naman da ke ciki waccan Samirar kece mace ta farko da Hajiya ta sa ayi wa irin wannan dahuwar a cikin wancan takardar mai kyalli ga gashasshen nama nan, duk matan da Alhaji Shamaki ya aura ke ce kaɗai bata buƙaci in je in ciro mata zanin gadon da ku ka kwana a kai ba. Saboda haka ina baki shawara ki yi ƙoƙarin cinye jarabawa." Nace Na gode, amma don Allah zan iya tambaya? Kai ta ɗaga. Nace wace irin jarabawace ki ke ta min magana tun jiya? Juma ta yi ƙasa da murya tace "Jarabawar zaman gidan nan ce kuma shekara ɗaya ce, zan sake tambaya ta ɗaga min hannu tare da faɗin ki bi a sannu." Nace To me rashin aiko ki cire zanin gado ya ke nufi? Tace "Kenan ta gane ke kin kawo budurcin bata buƙatar ta ga shaida." A zuciya ta nace Hajiya dai ta matsa wa kanta a wannan fannin duk da na gamsu da bayanin ta.
Na sauke ajiyar zuciya, nace, Da ku zamu yi aiki anjima? Ta ce "E dama zan tambaye ki ko mu rage aikin tun yanzu?" Nace Hajiya baza ta yi faɗa ba? Tace "A'a ai ita ba ruwan ta kece zaki kula da komai." Nace to kamar me zaku rage. Tace tafashen kaji in za a soya ne sai ki bamu umarni, da naman rago kuma akwai kifi ma. Nace to ku soya ɗin. Tace "Za ayi pepe ne ko kuwa?" Duk da ban iya ba sai na ce e har pepe ɗin ma kuyi, shima kifin ku yi zan shigo kamar goma. Tace "To aike 'yarnan baki da girman kai amma sauran ko kallo bamu ishe su ba, sai dai ace wanke min wannan yanka min waccan sai sun gama Hajiya ta kasa ci. In kuma har Hajiya bata ci ba to kin faɗi jarabawar farko, daga ranar kun ƙulla. Basa tuna mune gidan mu muka san kanshi. Na yi ɗan murmushi na gode Baba Juma. Da sauri tace "Allah ya yi miki albarka 'yarnan kin san darajar tsofaffi."
Tana fita nace Yawwa kai Allah na gode maka da ka bani mafita, sannan wannan kam akwai ta da magana, zanji abubuwa da dama a gurin ta cikin hikima. Naci nama gasashe da yaji na sha shayi da wainar ƙwai, ƙosai
da kunun gyaɗa kuwa ko kallon su ban yi ba domin ba baƙi na bane.